Yanzu-Yanzu:Gwamna Abba ya gana da Tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau
Rahotanni daga jihar Kano na cewa, Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya gana da tsohon gwamnan jihar, Malam Ibrahim Shekarau.
Ganawar tasu ta kasance a sirri.
Saidai rahotonni sun ce bata rasa nasaba da maganar komawar Malam Ibrahim Shekarau jam'iyyar APC.
Ko da a baya an ga yanda Malam Ibrahim Shekarau ya gana da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.








