Tuesday, December 16
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli: Zanen Tattoo da Rahama Saidu ta yi akan kirjinta ya jawo cece-kuce

Kalli: Zanen Tattoo da Rahama Saidu ta yi akan kirjinta ya jawo cece-kuce

Duk Labarai
Zanen Tattoo da Tauraruwar Tiktok, Rahama Saidu ta yi akan Kirjinta ya jawo cece-kuce sosai. Tun a kwanakin baya aka ga Rahama Kwance ana mata zanen a kirjinta wanda ya jawo cece-kuce sosau. Saidai a yanzu bayan data saki wasu sabbin hotuna, an kuma ganin Tattoo din ya fito sosai fiye da da. Hakan yasa da yawa suka rika tambayar shin me zanen yake nufi dan kuwa da Yarbanci ta rubutashi. Wasu masu fassara dai sun bayyana cewa, zanen na kirjinta na nufin Allah Dukiya.
Kalli Bidiyon yanda aka kai Adam A. Zango dakin Amaryarsa

Kalli Bidiyon yanda aka kai Adam A. Zango dakin Amaryarsa

Duk Labarai
A jiyane aka daura auren Tauraron fina-finan Hausa, Adam A. Zango da Amaryarsa, Maimuna Musa. Bidiyo ya bayyana inda aka ga yanda aka kaishi dakin amaryarsa. Tuni 'yan Uwa da abokan Arziki suka rika taya Adam A. Zango murnar aurensa. Amarya Maimuna dai ta yi fatan Allah yasa mutuwa ce zata rabata da gidan mijinta. https://www.tiktok.com/@sagir_producer/video/7531874147463482630?_t=ZS-8yyOLukQRHs&_r=1
Da Duminsa: Tauraron fina-finan Hausa, Adam A. Zango ya kara aure, ‘Yar Kannywood ce ya aura, Ji bayani game da fina-finan da ta yi da sanda aka daura auren

Da Duminsa: Tauraron fina-finan Hausa, Adam A. Zango ya kara aure, ‘Yar Kannywood ce ya aura, Ji bayani game da fina-finan da ta yi da sanda aka daura auren

Duk Labarai
Rahotanni da Hutudole ke samu na cewa, Tauraron fina-finan Hausa, Adam A. Zango ya kara aure. Rahotannin sun ce Adam A. Zango ya auri Salamatu wadda aka fi sani da Maimuna Musa ta Garwashi. Sannan kuma itace ta fito Zaituna a Labarina. Hutudole ya samu labari cewa an daura aurenne a ranar Lahadi, 17 ga watan Augusta. Tuni dai 'yan Uwa da abokan arziki suka fara taya su Murna.
Kalli Bidiyo Da Duminsa: A karshe dai an bayyana ainahin Mijin Rahama Sadau, bama dan Najeriya bane

Kalli Bidiyo Da Duminsa: A karshe dai an bayyana ainahin Mijin Rahama Sadau, bama dan Najeriya bane

Duk Labarai
Daya daga cikin wadanda ake bayyana cewa sune suka auri Rahama Sadau me suna Abdullahi Aliyu ya fito ya bayyana cewa bashine mijin Rahama ba. Yace tabbas suna da alaka me kyau tsakaninsa da Rahama Sadau. Saidai yace bashine ya aureta ba dan hotunansu da ake yadawa sun kai kusan shekaru 6 da dauka ba sabbin hotuna bane. Ya kara da cewa, Mijin Rahama Sadau ba dan Najeriya bane, dan kasar Chinane. Kuma nan gaba kadan za'a ganshi. Kalli Bidiyon anan
Da Duminsa: Jam’iyyar NNPP ta Lashe zaben cike gurbi na Bagwai da Shanono

Da Duminsa: Jam’iyyar NNPP ta Lashe zaben cike gurbi na Bagwai da Shanono

Duk Labarai
Jam'iyyar NNPP ta Lashe zaben cike gurbi na Bagwai da Shanono da aka gudanar jiya, Asabar a Kano. Da yake bayyana sakamakon zaben da misalin karfe  12:36am na safe, Professor Hassan Shitu ya bayyana dan takarar NNPP, Dr Ali Kiyawa a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri'u 16,198 inda ya kayar da dan takarar APC, Ahmad Kadamu, da ya samu kuri'u 5,347. 'Yan Jam'iyyar NNPP sun gudanar da zaman dirshan a ofishin INEC inda suka zargi cewa, ana shirin yin murdiyar zabe a sakamakon mazabar Ghari/Tsanyawa. Kakakin Gwamnatin jihar Kano, Sanusi Tofa yace ba zasu bar kofar INEC din ba sai an fadi sakamakon Ghari/Tsanyawa
EFCC ta kwato Naira Biliyan 5 da dala Miliyan $10 daga hannun barayin tsaffin ma’aikatan NNPCL

EFCC ta kwato Naira Biliyan 5 da dala Miliyan $10 daga hannun barayin tsaffin ma’aikatan NNPCL

Duk Labarai
Hukumar hana rashawa da cin hanci, EFCC ta kwato Naira Biliyan 5 da Dala Miliyan $10 daga hannun tsaffin ma'aikatan NNPCL da 'yan Kwangila. Wadannan kudade na da alaka da gyaran matatun man Kaduna, Fatakwal, da Warri. Hakanan kuma Punchng tace ta samu karin bayanin cewa, EFCC din na kokarin kara kwato wasu Naira Biliyan 10 da wasu dala Miliyan $13 da suma aka karkatar dasu. Rahoton yace shugaban EFCC, Ola Olukoyede da kansa ne ke jagorantar wannan bincike musamman ganin yanda aka kashe makudan kudade wajan gyaran matatun man Najeriya amma har yanzu basa aiki. Gwamnatoci da suka shude sun yi kokarin gyaran matatun man fetur din amma basu yi nasara ba.
Kalli Bidiyo: An Kama Akwatin Zaɓe Da Na’urar BVAS A Motar Jigon APC, Mustapha Salihu, A Zaben Ganye

Kalli Bidiyo: An Kama Akwatin Zaɓe Da Na’urar BVAS A Motar Jigon APC, Mustapha Salihu, A Zaben Ganye

Duk Labarai
An Kama Akwatin Zaɓe Da Na’urar BVAS A Motar Jigon APC, Mustapha Salihu, A Zaben Ganye. Wasu jami’an tsaro a jihar Adamawa sun gano akwatin zaɓe da na’urar tantance masu kada kuri’a (BVAS) a cikin motar Mustapha Salihu, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa (Arewa maso Gabas), yayin gudanar da zaben cike gurbi a mazabar Ganye. Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin ‘yan siyasa da jama’a, inda ake zargin yunkuri ne na murde sakamakon zaɓe. An ce an kama kayan zaɓen ne yayin da ake gudanar da aikin tantance kuri’u a wasu rumfunan zaɓe, kuma hakan ya janyo tarin mutane da bacin rai. Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da hukumomin tsaro har yanzu ba su fitar da cikakken bayani kan lamarin ba, amma al’ummar yankin da dama na bukatar a gudanar da bincike tare da daukar ...
Har Gida Shugaban Kasar Libiya Ya Ziyarci Daliba ‘Yar Asalin Kasarsa, Bayan Ta Zo Na Daya A Gasar Adabin Larabci Na Duniya Domin Karrama Ta

Har Gida Shugaban Kasar Libiya Ya Ziyarci Daliba ‘Yar Asalin Kasarsa, Bayan Ta Zo Na Daya A Gasar Adabin Larabci Na Duniya Domin Karrama Ta

Duk Labarai
ALLAH DAYA GARI BANBAM: Har Gida Shugaban Kasar Libiya Ya Ziyarci Daliba 'Yar Asalin Kasarsa, Bayan Ta Zo Na Daya A Gasar Adabin Larabci Na Duniya Domin Karrama Ta Da yake kasar tana da kishin dalibanta, shugaban kasa Abdul Hanid da kansa ya kaiwa dalibar mai suna Nadia ziyara har gida don karrama ta. Wannan labari na dauke da darasi mai yawa game sa shugabanninmu na Nijeriya.