Saturday, December 13
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Bidiyon Haduwar G-Fresh da Sheikh Ibrahim Maqari inda yace ya ji wa’azin da malam ya masa kuma yanzu zai rika fadakarwa ko da ta hanyar wasa ne

Kalli Bidiyon Haduwar G-Fresh da Sheikh Ibrahim Maqari inda yace ya ji wa’azin da malam ya masa kuma yanzu zai rika fadakarwa ko da ta hanyar wasa ne

Duk Labarai
A karshe dai Tauraron Tiktok, GFRESH Al-amin ya hadu da Sheikh Ibrahim Maqari inda yace ya ji nasihar da malam ya masa. Gfresh yace zai rika fadakarwa yanzu ko da ta hanyar wasa ne. https://www.tiktok.com/@gfreshfanpage/video/7536960885865073926?_t=ZS-8yoDr9ou5Wz&_r=1 A jiya ne dai aka ga Gfresh a gaban malam yana tambayar shin ko ya halatta mutum ya rika Bidiyo da iyalinsa yana watsawa Duniya. Malam dai ya bashi Amsar cewa, idan abinda ake yi bai sabawa addini ba, babu matsala.
Gwamnatin tarayya na barzanar korar ma’aikata, 3,598 daga aiki

Gwamnatin tarayya na barzanar korar ma’aikata, 3,598 daga aiki

Duk Labarai
Gwamnatin Tarayya na barazanar korar ma'aikata, 3,598 da suka ki yin tantancewa daga aiki. Gwamnatin tace idan aka sake yin tantancewar, duk wanda bai yadda an tantanceshi ba, za'a dauka kawai takardat daukar aiki ta boge gareshi. Za'a yi tantancewarce daga ranar 18 ga watan Augusta zuwa ranar 28 ga watan a ma'aikatu daban-daban na tarayya. An bukaci ma'aikatan dasu gabatar da takardun daukarsu aiki dana karin girma da sauransu.
Kamun da akawa Tsohon Gwamnan Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal siyasa ce kawai>>Inji PDP

Kamun da akawa Tsohon Gwamnan Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal siyasa ce kawai>>Inji PDP

Duk Labarai
Jam'iyyar PDP, Reshen jihar Sokoto ta bayyana cewa, kamun da akawa tsohin Gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal siyasa ce. Me magana da yawun jam'iyyar, Hassan Sanyinnawal ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai da safiyar ranar Talata. Yace EFCC ta bar asalin masu rashawa da cin hanci inda take kama irin su Tambuwal. Yace hakan kokari ne na dakile 'yan Adawa da kuma hana yiwa shugaba Tinubu suka da gaya mai gaskiya. Ya yi kira ga masoyan Tambuwal su kwantar da hankali amma su tsaya kai da kafa wajan goyon bayansa.
Gwamnatin Nijeriya Ta Yi Maraba Da Naɗin Maryam Bukar Hassan A Matsayin Jakadiyar Zaman Lafiya Ta Duniya

Gwamnatin Nijeriya Ta Yi Maraba Da Naɗin Maryam Bukar Hassan A Matsayin Jakadiyar Zaman Lafiya Ta Duniya

Duk Labarai
Gwamnatin Nijeriya Ta Yi Maraba Da Naɗin Maryam Bukar Hassan A Matsayin Jakadiyar Zaman Lafiya Ta Duniya. A yau Litinin ne gwamnatin shugaba Tinubu ta karɓi baƙuncin fitacciyar mai waƙar baka Maryam Hasan wadda ta yi nasarar zama jakadiyar zaman lafiya ta majalisar dinkin duniya. Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ne ya karbi bakuncin jakadiyar da tawagarta a fadar shugaban ƙasa inda ya bayyana farincikin gwamnati da shirinta na yin aiki da jakadiyar yar asalin Najeriya don ƙarfafa zaman lafiya a Najeriya da ma duniya baki ɗaya. Da yake jawabi ga tawagar ta Global Advocate for Peace ta Majalisar Dinkin Duniya, Shettima ya bayyana Maryam a matsayin mace mai tsayuwar daka wajen sadaukar da basirarta ga wanzar da zaman lafiya musamman a wata ƙasidarta mai taken 'Rikici bai...
Masallata a masallacin kasar Turkiyya da aka sakawa sunan dan Kwallon Najeriya, Victor Osimhen sun ce basu yadda a sakawa masallacinsu sunan Kirista ba, dole a canja

Masallata a masallacin kasar Turkiyya da aka sakawa sunan dan Kwallon Najeriya, Victor Osimhen sun ce basu yadda a sakawa masallacinsu sunan Kirista ba, dole a canja

Duk Labarai
Masallata a masallacin Bulut Mosque dake kasar Turkiyya sun ce basu yadda da canjawa masallacinsu suna zuwa Victor Osimhen ba. Masallacin dai an ginashine a shekarr 2008 inda aka saka masa sunan Bulut. Abinda ya faru shine a Google, idan ka duba masalacin zaka ga sunansa Victor Osimhen Mosque. Saidai masallatan dake Sallah a masallacin sun ce Dan kwallon bai taba amfanar masallacin da komai ba sannan bai taba amfanar garinsu da komai ba dan haka basu yadda da wannan ba, bugu da kari gashi kirista ne. Wasu dai na ganin cewa, kuskurene aka samu wajan rubutu da ya kawo hakan.
Kalli Bidiyo: Mutane na ta Mun sharrin wai Qaruwanci na yi aka bani motar GLK, ni kuma wallahi ban ma taba haduwa da wanda ya bani ba>>Inji Rahama Sa’idu

Kalli Bidiyo: Mutane na ta Mun sharrin wai Qaruwanci na yi aka bani motar GLK, ni kuma wallahi ban ma taba haduwa da wanda ya bani ba>>Inji Rahama Sa’idu

Duk Labarai
Tauraruwar Tiktok, Rahama Sa'idu ta bayyana cewa abinda mutane ke fadi akanta wanda ba daidai ba shine wai ita karuwace. Tace musamman sanda aka bata kyautar Motar GLK, tace da yawa na cewa wai ta bayar da kantane. Tace amma abinda mutane basu sani ba shine wanda ya bata motar bata taba ganinshi ba. Tace suna dai waya, yana ce mata zai je sayen takalma dan ita abinda take sayarwa kenan. Kalli Bidiyon anan
Maimakon Miliyan 10 da yayi Alkawarin baiwa tauraron Kannywood, Jamilu Kochila a matsayin gudummawar Aurensa, Dan kasuwa, Baballe Na’abba yace a yanzu zai basu kujerar makka da Madina

Maimakon Miliyan 10 da yayi Alkawarin baiwa tauraron Kannywood, Jamilu Kochila a matsayin gudummawar Aurensa, Dan kasuwa, Baballe Na’abba yace a yanzu zai basu kujerar makka da Madina

Duk Labarai
A lokacin bikin Tauraron Kannywood, Jamilu Kochila, da yawa sun yi alkawarin bashi gudummawa amma basu cika Alkawari ba. Daga cikin cikin wadanda suka yi wannan alkawarin, akwai dan Kasuwa, Baballe Na'abba wanda yayi Alkawarin bayar da gudummawar Naira Miliyan 10. Saidai daga baya a yanzu yace zai baiwa Amarya da Ango kujerun zuwa Makkah da Madina. Mansurah Isah ce ta bayyana hakan.
Da duminsa: Hukumar EFCC na tsare da tsohon gwamnan Sokoto, Tambuwal kan badakalar Naira Bilyan 189.

Da duminsa: Hukumar EFCC na tsare da tsohon gwamnan Sokoto, Tambuwal kan badakalar Naira Bilyan 189.

Duk Labarai
Da duminsa: Hukumar EFCC na tsare da tsohon gwamnan Sokoto, Tambuwal kan badakalar Naira Bilyan 189. EFCC TA Garƙame Tambuwal A Abuja Wakiliyarmu Khubrah Mustapha Dabai A halin yanzu dai tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal yana hannun hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC a hedikwatarta da ke Abuja. Ana yi wa Tambuwal tambayoyi ne kan zarge-zargen fitar da makudan kudade da suka kai Naira biliyan 189, wanda aka bayyana a fili cewa yin hakan ya saɓawa dokar halatta kudaden haram, ta shekarar 2022. Majiyarmu ta talabijin ta tattaro cewa tsohon gwamnan ya isa ofishin EFCC ne da misalin karfe 11:30 na safe, inda aka kai shi gaban kwamitin bincike kan badakalar kuɗaɗen. Duk ƙoƙarin da Dimokuradiyya Tv ta yi har zuwa lokacin hada wannan rah...
Makusancin Kwankwaso, Abulmumin Kofa, ya gana da Tinubu karo na biyu cikin makonni biyu

Makusancin Kwankwaso, Abulmumin Kofa, ya gana da Tinubu karo na biyu cikin makonni biyu

Duk Labarai
Makusancin Kwankwaso, Abulmumin Kofa, ya gana da Tinubu karo na biyu cikin makonni biyu. Abdulmumin Jibrin Kofa, makusanci ga Rabiu Musa Kwankwaso na NNPP, ya sake ganawa da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a fadar Aso Villa, Abuja, a ranar Lahadi — karo na biyu cikin makonni biyu. Rahotanni sun nuna cewa ganawar ta dauki tsawon sa’o’i biyu, inda ake kyautata zaton ta shafi dangantakar Tinubu da Kwankwaso da kuma karuwar adawa ga jam’iyyar APC a wasu yankunan arewacin Najeriya. Jibrin, wanda ya ki bayyana dalilin tattaunawar, ya yi ganawa ta farko da Tinubu a ranar 30 ga Yuli, inda ya ce sun tattauna kan dunkulewar kasa da ci gaban ta. Ganawar ta na zuwa ne kwanaki bayan zargin Kwankwaso cewa gwamnatin tarayya na fifita kudu a ayyukan ci gaba. Wasu majiyoyi daga fadar shu...