Wednesday, November 19
Shadow

Masallata a masallacin kasar Turkiyya da aka sakawa sunan dan Kwallon Najeriya, Victor Osimhen sun ce basu yadda a sakawa masallacinsu sunan Kirista ba, dole a canja

Masallata a masallacin Bulut Mosque dake kasar Turkiyya sun ce basu yadda da canjawa masallacinsu suna zuwa Victor Osimhen ba.

Masallacin dai an ginashine a shekarr 2008 inda aka saka masa sunan Bulut.

Abinda ya faru shine a Google, idan ka duba masalacin zaka ga sunansa Victor Osimhen Mosque.

Saidai masallatan dake Sallah a masallacin sun ce Dan kwallon bai taba amfanar masallacin da komai ba sannan bai taba amfanar garinsu da komai ba dan haka basu yadda da wannan ba, bugu da kari gashi kirista ne.

Wasu dai na ganin cewa, kuskurene aka samu wajan rubutu da ya kawo hakan.

Karanta Wannan  Jama'a Ina Neman Taimakon Kudì Domin Duk Mako Uku Sai An Yi Min Allurar Naira Dubu 250, Kuma Sai An Yi Tsawon Watanni Shida Ana Yi Min Allurar, Cewar Malam Nata'ala Na Shìirin Dadin Kowa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *