Thursday, December 18
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Babu Inda Na Ce Sai Mun Bada Cin Hancin Milyan Uku Kafin A Ba Mu Damar Gabatar Da Kudiri A Majalisar Tarayya, Cewar Hon Usman Ibrahim Auyo

Babu Inda Na Ce Sai Mun Bada Cin Hancin Milyan Uku Kafin A Ba Mu Damar Gabatar Da Kudiri A Majalisar Tarayya, Cewar Hon Usman Ibrahim Auyo

Duk Labarai
Babu Inda Na Ce Sai Mun Bada Cin Hancin Milyan Uku Kafin A Ba Mu Damar Gabatar Da Kudiri A Majalisar Tarayya, Cewar Hon Usman Ibrahim Auyo Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Hadejia, Auyo da Kafin Hausa dake jihar Jigawa, Honarabul Usman Ibrahim Auyo, wanda ake yi wa lakabi da Kamfani ya nesanta kansa da labarin karya da aka yada akansa, wanda aka ce ya ce ba a ba su damar gabatar da kudiri a majalisa har sai sun bada cin hancin naira milyan uku ko fiye da haka. Sannan kuma sai sun yi ta kamun kafa ga sauran 'yan majalisun. A cewarsa ba ya na nufin majalisa ake baiwa wannan kudin ba, a duk sanda mutum zai gabatar da kudiri, akwai wadanda daga waje aikin su shine ka ba su kwangilar rubuta maka kudiri ka biya su, kafin daga bisani ka nemi shawarwari daga wajen takwaro...
YANZU-YANZU: Jami’an DSS Sun Kama Wani Ejan Din PDP Da Kusan Naira Milyan 30 Domin Siyan Kuri’u A Yayin Zaben Cike Gurbi A Kaduna

YANZU-YANZU: Jami’an DSS Sun Kama Wani Ejan Din PDP Da Kusan Naira Milyan 30 Domin Siyan Kuri’u A Yayin Zaben Cike Gurbi A Kaduna

Duk Labarai
Mutumin mai suna Shehu Fantage, an kama shine a jiya Juma'a a wani otal dake cikin garin Kaduna, a yayin da yake kokarin kasafta kudin domin yin amfani da su wajen siyen kuri'u a zaben cike gurbi na dan majalisar tarayya mai wakiltar Chikun/Kajuru. Ita na hukumar 'yan sandan jihar Kaduna ta bakin kakakinta, DSP Mansir Hassan ta tabbatar da kama mutumin da DSS suka yi, inda yake komar su kuma ana kan bincikensa.
Barr. Abba Hikima Fagge: “Shugabannin siyasa ne ke hura wutar faɗan daba a Kano”

Barr. Abba Hikima Fagge: “Shugabannin siyasa ne ke hura wutar faɗan daba a Kano”

Duk Labarai
Barr. Abba Hikima Fagge: "Shugabannin siyasa ne ke hura wutar faɗan daba a Kano" Fitaccen lauya kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum a Kano, Barrister Abba Hikima Fagge, ya yi tsokaci kan matsalar fadan yan daba da ke ta ƙara ƙaruwa a cikin birnin Kano. A cewarsa, ba matasa da kansu ne tushen wannan matsala ba, sai dai shugabannin siyasa da ke amfani da su wajen cimma muradunsu. Barr. Abba ya bayyana cewa, a lokutan siyasa musamman, ana yawan ganin yadda ake rarraba kuɗi da miyagun ƙwayoyi ga matasa domin a tura su wajen tada tarzoma, abin da daga ƙarshe yake jefa al’umma cikin tsoro da rashin kwanciyar hankali. Ya ƙara da cewa, “Matsalar daba ba sabon abu ba ne a Kano, amma abin takaici shi ne yadda shugabannin da ake ɗora ran samun mafita a kansu suke ƙara ƙara wa mat...
Kalli Bidiyo: Ya halatta idan kuna tafiya abinci ya kare muku, babu yanda za’a yi, ku kama daya daga cikinku ku Yqnkq ku ci, amma malamai sun ce wanda baya ajiye gemu ake Yqnkqwq>>Inji Sheikh Shehu Abdullahi Biu

Kalli Bidiyo: Ya halatta idan kuna tafiya abinci ya kare muku, babu yanda za’a yi, ku kama daya daga cikinku ku Yqnkq ku ci, amma malamai sun ce wanda baya ajiye gemu ake Yqnkqwq>>Inji Sheikh Shehu Abdullahi Biu

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama, Sheikh Shehu Abdullahi Biu ya bayyana cewa, ya halatta idan kuna tafiya abinci ya kare babi yanda za'a yi a kama daya daga cikin matafiyan a ci. Malam yace kuma wanda ake yankawa shine wanda baya ajiye gemu. https://www.tiktok.com/@usainihassanmaigaskiya/video/7538368762324487441?_t=ZS-8yvFuG2UH8j&_r=1 Da yawa dai sun yi mamaki da wannan karatun.
Ba zaka bata mana suna ba, Ka kawo shaidar cewa, Sai an biya Naira Miliyan 3 ake gabatar da kudirin doka a majalisa ko mu hukunta ka>>Majalisar Wakilai ga dan majalisa, Ibrahim Usman Auyo

Ba zaka bata mana suna ba, Ka kawo shaidar cewa, Sai an biya Naira Miliyan 3 ake gabatar da kudirin doka a majalisa ko mu hukunta ka>>Majalisar Wakilai ga dan majalisa, Ibrahim Usman Auyo

Duk Labarai
Majalisar wakilai ta bukaci dan majalisar daga jihar Jigawa me wakilar Hadejia, Auyo, da Kafin Hausa, Ibrahim Usman Auyo ya fito ya kawo shaidar cewa sai an biya kudi ake gabatar da kudirin doka a majalisar. Dan majalisar dai yayi wannan ikirarin ne a yayin ganawa da mutanen mazabarsa. Inda yace Ana biyan daga Naira Miliyan daya zuwa 3 kamin gabatar da kudirin doka a majalisar. Saidai a martanin majalisar ta bakin me magana da yawunta, Akin Rotimi tace ba zata bari a bata mata suna ba, wannan ikirari na dan majalisa, Ibrahim Usman na da girma kuma zata bincikeshi ya bata hujjarsa. Tace amma idan bai bayar da wata hujja ba, zata gabatar dashi a gaban kwamitin da'a na majalisar.
Gwamnatin Tarayya zata bayar da bashin Naira Dubu Biyar ga ‘yan Kasuwa da Manoma, Ji yanda zaku samu

Gwamnatin Tarayya zata bayar da bashin Naira Dubu Biyar ga ‘yan Kasuwa da Manoma, Ji yanda zaku samu

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya zata fara bayar da bashin GEEP ga manoma da kananan 'yan kasuwa. Shugaban tsarin Hamza Ibrahim Baba ne ya bayyana haka a Kaduna yayin ganawa da wakilan 'yan kasuwar da manoma a ranar Juma'a. Ya bayyana cewa, za'a bayar da bashine ba tare da ruwa ko jingina ba. Yace kuma bashin daga Naira dubu biyar ne har zuwa Naira dubu dari. Yace kuma za'a bada tazarar watanni 6 kamin a faa biyan bashin. Yace za'a fara bayar da bashin kamin karshen shekarar 2025 da muke ciki a dukkan fadin Najeriya. Yace bashin zai taimakawa manoman da 'yan kasuwar sayen kayan amfaninsu.
ADC ta zargi APC da shirin tafka maguɗi a zaɓen cike gurbi na Kaduna

ADC ta zargi APC da shirin tafka maguɗi a zaɓen cike gurbi na Kaduna

Duk Labarai
Kafin zaɓen cike gurbi da za a gudanar a gobe, rnanar Asabar a majalisun tarayya da na jiha a Jihar Kaduna, jam’iyyar adawa ta African ADC ta zargi jam’iyyar mai mulki ta APC da daukar ’yan daba da kuma karɓar biliyoyin naira daga cikin jihar da wajen ta domin yin magudi. Zaɓen cike gurbin zai gudana ne a mazaɓar tarayya ta Chikun/Kajuru da mazaɓar tarayya ta Zaria/Kewaye, da kuma mazaɓar majalisar jiha ta Basawa. Waɗannan zarge-zargen na ADC sun haifar da musayar maganganu tsakaninta da gwamnatin jihar da kuma jam’iyyar APC. Kwamishinan ƴaɗa Labarai na jihar, Ahmed Maiyaki da ya mayar da martani yana cewa zarge-zargen na ADC “ba su da tushe kuma abin dariya ne.”
Tinubu ya naɗa sabon shugaban gidan talabijin na ƙasa, NTA

Tinubu ya naɗa sabon shugaban gidan talabijin na ƙasa, NTA

Duk Labarai
Tinubu ya naɗa sabon shugaban gidan talabijin na ƙasa, NTA Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi babban sauy-sauye na shugabanci a gidan talabijin na ƙasa, NTA, inda ya naɗa Rotimi Richard Pedro, a matsayin sabon Darakta-Janar na gidan talabijin din na gwamnati. “Sauran manyan nade-naden sun haɗa da Karimah Bello daga Jihar Katsina a matsayin Daraktar Tallace-Tallace, Stella Din daga Jihar Filato a matsayin Daraktar Labarai, da kuma Sophia Issa Mohammed daga Jihar Adamawa a matsayin Babbar Darakta ta Kamfanin NTA Enterprises Limited. “Pedro, ɗan asalin Legas, fitaccen mai kasuwanci a fannin kafafen watsa labarai da kuma mai ba da shawara, wanda ke da kusan shekaru talatin na kwarewar jagoranci a harkar watsa shirye-shirye, wasanni, da kuma tallace-tallace a faɗin Afirka, Birta...