Saturday, December 13
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Da Duminsa: ‘Yan kasuwar Man fetur sun rage farashi suna sayar da man kasa da farashin Dangote

Da Duminsa: ‘Yan kasuwar Man fetur sun rage farashi suna sayar da man kasa da farashin Dangote

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, 'yan kasuwar Man fetur sun rage farashin man fetur dinsu inda suke sayar dashi a farashi kasa da yanda matatar man Dangote ke sayarwa. Hakan na zuwane kwanaki kadan bayan da Dangoten yayi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya hana shigo da man fetur daga kasashen waje. Jaridar Punchng ta ruwaito cewa, 'yan kasuwar na sayar da man a farashin 860 akan kowace lita yayin da Dangote kuma ke sayarwa akan 865 zuwa 875 akan kowace lita. Shugaban kungiyar 'yan kasuwar man fetur ta IPMAN, Chinedu Ukadike ya tabbatar da rage farashin inda yace hakan na nuna kyawun kasuwa. Yace yana kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da kada ya saurari kiran da Dangote ke yi na cewa ya hada shigo da man fetur din daga kasashen waje.
Shugaba Tinubu ya nada lumode Samuel Adeyemi a matsayin sabon shugaban Hukumar kwana-kwana

Shugaba Tinubu ya nada lumode Samuel Adeyemi a matsayin sabon shugaban Hukumar kwana-kwana

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya nada lumode Samuel Adeyemi a matsayin sabon shugaban hukumar kwana-kwana masu kashe Gobara ta kasa. Lumode zai fara aiki ne ranar August 14, 2025 a matsayin sabon shugaban hukumar. Hakan na zuwane yayin da shugaban hukumar na yanzu, Engr. Abdulganiyu Jaji ke shirin zauka ya ajiye aiki bayan kaiwa shekarun ritaya watau shekaru 60.
Shugaba Tinubu na nuna tausai sosai a mulkinsa>>Inji Kashim Shettima

Shugaba Tinubu na nuna tausai sosai a mulkinsa>>Inji Kashim Shettima

Duk Labarai
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na nuna tausai sosai a mulkinsa. Ya bayyana hakane a wajan taron da aka gudanar a Arewa House dake Jihar Kaduna. Kashim Shettima wanda me baiwa shugaban kasa shawara kan ayyuka na musamman, Dr Aliyu Modibbo Umar, ya wakilta a wajan taron da aka yi na kwanki biyu, ya bayyana cewa shugaban kasar ya kawo ayyukan ci gaba sosai. Ya bayar da misali a bangaren Ilimi inda yace shugaba Tinubu ya samarwa 'ya'yan talakawa damar karatu inda aka rika bayar sa bashin karatu. Yace daga baya da aka ga cewa, Guarantor da kuma kayyade yawan samun mutum kamin a bashi bashin zai zo da matsala sai aka dakatar da hakan aka rika baiwa daliban bashin kai tsaye.
Kalli Sabon Bidiyo: A karshe dai Ummi Nuhu ta fito da kanta ta fadi kuskuren da ta yi da ya jefata a wahalar rayuwa

Kalli Sabon Bidiyo: A karshe dai Ummi Nuhu ta fito da kanta ta fadi kuskuren da ta yi da ya jefata a wahalar rayuwa

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{"transform":1,"square_fit":1},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":true,"containsFTESticker":false} Tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Nuhu ta fito ta bayyana dalilin da yasa ta fada wahalar rayuwar da aka ganta a ciki ake ta cece-kuce bayan hirar da Hadiza Gabon ta yi da ita. Ummi Nuhu a sabuwar hirar ta da Hadiza Gaon ta bayyana cewa, Babban Kuskuren da ta aikata shine a lokacin data samu dama, bata yiwa kanta tanadin komai ba, jin dadin rayuwa akai ta yi. Tace amma tana fatan jarumai mata musamman masu tasowa a yanzu zasu dauki darasi daga Ra...
Labarin cewa mun dakatar da El-Rufai tsayon shekaru 30 karyane, Munafurcin jam’iyyar APC ne>>Inji Jam’iyyar SDP

Labarin cewa mun dakatar da El-Rufai tsayon shekaru 30 karyane, Munafurcin jam’iyyar APC ne>>Inji Jam’iyyar SDP

Duk Labarai
Jam'iyyar SDP me doki inda tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya koma ta karyata labarin da yayi yawo sosai cewa, ta dakatar da El-Rufai tsawon shekaru 30. Kakakin jam'iyyar a jihar Kaduna, Hon. Darius Kurah ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai inda ya bukaci mutane su yi watsi da wanan magana. Yace wanda aka ce ya fitar da labarin me suna, Araba Rufus Aiyenigba wanda aka ce kakakin jam'iyyar SDP ne karyane bashine kakakin jam'iyyar SDP na kasa ba. Yace kuma abinda ake yadawa cewa, wai El-Rufai na munafurtar jam'iyyar SDP shima ba gaskiya bane.
Kalli Bidiyo: Wallahi ko kadan Ummi Nuhu bata ban Tausai ba, Mace ta wuce shekara 40 amma bata taba aure ba ai ba abin tausai bace>>Inji M Beauty

Kalli Bidiyo: Wallahi ko kadan Ummi Nuhu bata ban Tausai ba, Mace ta wuce shekara 40 amma bata taba aure ba ai ba abin tausai bace>>Inji M Beauty

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Me Tiktok, M. Beauty ta bayyana cewa, ko kadan bata Tausayawa Ummi Nuhu ba. Tace Ummi bata yi amfani da damar da ta samu ba a rayuwa. Tace Ummi ta haura shekaru 40 amma ba ta taba aure ba kuma bata taba haihuwa ba. Ta kara da cewa kai ko da Hadiza Gabon ta kama hanyar tsufa. Kalli Bidiyon anan https://www.tiktok.com/@mgombe55/video/7532783849781218616?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=753278384...
Bamu tare da masu sukar Tinubu suna cewa baiwa arewa komai ba, Tinubu yawa Arewa kokari>>Inji Gwamnoni 18 na Arewacin Najeriya

Bamu tare da masu sukar Tinubu suna cewa baiwa arewa komai ba, Tinubu yawa Arewa kokari>>Inji Gwamnoni 18 na Arewacin Najeriya

Duk Labarai
Gwamnoni 18 na Arewacin Najeriya sun hada kai inda suka ce basa tare da masu sukar Tinubu suna cewa ya ware yankin Arewa baya ma yankin aiki Gwamnonin sun bayyana hakane ta bakin shugaban kungiyarsu, Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahya. Gwamna Yahya ya fada a yayi jawabi wajan taro a Arewa House dake Kaduna wajan taro tsakanin shuwagabanni da Talakawa na kwanaki biyu Gwamnan yace lallai akwai matsin rayuwa wanda suka samo Asali daga cire tallafin man fetur da na dala. Yace amma fa ci gaban ma akwaishi. Ya kawo misalai na Gyaran Titin Abuja zuwa kaduna, da Kano. Da hakar man fetur a Kolmani da dai sauransu.
Tunda kamawa ake, Nima Nace Tinubu bashi da lafiya>>Matashi yace yana son a kamashi

Tunda kamawa ake, Nima Nace Tinubu bashi da lafiya>>Matashi yace yana son a kamashi

Duk Labarai
Wani matashi me suna Ahmad Muhmmad dake yin Tiktok ya fito yayi ikirarin cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu bashi da lafiya Hakan na zuwane bayan da aka kama shahararren dan Tiktok, Sultan kan zargin irin wannan ikirari. Matashin yace tunda kamawa ake shima azo a kamashi. https://www.tiktok.com/@ahmadbalokaci/video/7532568722804886802?_t=ZS-8ySGQiIzSYi&_r=1