Maza ku kiyayi kanku ku daina shan maganin karfin maza, a yau mutane 3 nasan sun sheka lahira saboda shan maganin karfin maza>>Inji Murja Kunya
Tauraruwar Tiktok, Murja Kunya ta jawo hankalin maza akan su daina shan maganin karfin maza inda tace yana kisa.
Murja tace ko a yau mutane 3 tasan sun mutu dalilin shan maganin karfin maza.
Murja tace mutum sai ya je ya asha maganin bashi da tabbas watakila matarsa sun yi fada ba zata bashi ba, a zo a samu matsala.
https://www.tiktok.com/@murjess1/video/7520912629175438599?_t=ZM-8xaTYhDUijY&_r=1
Ikirarin Murja na maganin maza na kisa zai iya zama gaskiya dan kuwa akwai rahotanni da yawa akan hakan.








