Thursday, December 25
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Garin Neman Gira… Wannan Matar kiris ya hana ta makance a yayin da taje yin gyaran gira

Garin Neman Gira… Wannan Matar kiris ya hana ta makance a yayin da taje yin gyaran gira

Duk Labarai
Wata mata me suna Refilwe Motiang 'yar kasar Afrika ta Kudu ta sha da kyar bayan da ta je gyaran gira. Refilwe data fito daga yankin Midrand na birnin Johannesburg, tace zata yi tafiyane shine ta je a mata gyaran gira dan ta kara kyau. Matar tace ta je ta zauna an fara mata gyara sai ta ji tana jin zafi. Tace anan ta gayawa me mata gyaran girar amma sai tace mata hakan ba matsala bace gam din ne me karfi ne. Saidai tace can taji zafin yayi yawa ba zata iya jurewa ba. Tace haka ta tashi tsaye ta fita. Tace anan ta ji da kyar take bude idonta, da gudu aka garzaya da ita zuwa Asibiti. An dan kwantar da ita aka bata magani amma daga baya aka sallameta, yanzu tana jin sauki. Matar tace ta yi nadamar yunkurin yin gyaran girar inda tace tana tunanin kar me shagin gyaran ka...
Idan Kun saci kudin Talakawa ku daina kaiwa kasashen Turawa>>Dangote ya baiwa barayin Gwamnati a Najeriya shawara

Idan Kun saci kudin Talakawa ku daina kaiwa kasashen Turawa>>Dangote ya baiwa barayin Gwamnati a Najeriya shawara

Duk Labarai
Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya bayyana cewa bai kamata ace masu satar kudin talakawa suna kai kudaden kasashen turawa ba. Dangote yace babu kasar da ba'a sata, amma banbancin misalin kasashen Asia dana Afrika shine, idan sun saci kudin suna zuba jari dasu ne a kasashen su maimakon kaiwa kasashen Turawa. Dangote yace ba wai yana karfafawa jami'an gwamnati satar kudin talakawa bane amma yana da kyau su san cewa kamata yayi su rika amfani da kudin a cikin gida maimakon kaiwa kasar waje dan ci gaban kasar.
Duk sojan da aka kama ya na shan Wiwi ko ƙwaya zai ɗanɗana kuɗar da>>Kwamanda

Duk sojan da aka kama ya na shan Wiwi ko ƙwaya zai ɗanɗana kuɗar da>>Kwamanda

Duk Labarai
Kwamandan Runduna ta 17 na Sojojin Najeriya da ke Katsina, Birgediya Janar Babatunde Omopariola, ya umarci dakarunsa da su kama kuma su kai rahoto kan duk wani soja da aka kama yana shan wiwi ko amfani da miyagun kwayoyi. Janar Omopariola ya bayar da wannan umarni ne a ranar Asabar a garin Katsina, yayin bikin ranar Sojojin Najeriya ta shekarar 2025 (NADCEL), wanda aka gudanar a ofishin rundunar. A cewarsa, shan miyagun kwayoyi na rage karfin ma’aikata a Najeriya kuma yana barazana ga makomar kasa. Ya gargadi jami’ai da dakarun rundunar da su guji amfani da kwayoyi haramtattu, musamman a cikin bariki. Kwamandan ya bayyana amfani da miyagun kwayoyi a matsayin wani babban abin da ke lalata ginshikin zamantakewa da lafiyar al’umma a Najeriya.
Hotuna: Wani Matashi Ya Dane Saman Karfen Sabis A Jihar Bauchi, Ya Ce Ba Zai Sauko Ba Har Sai Kwamishinan Kudi Na Jihar Bauchi Ya Amince Ya Fito Takarar Gwaman Bauchi A Zaben 2027

Hotuna: Wani Matashi Ya Dane Saman Karfen Sabis A Jihar Bauchi, Ya Ce Ba Zai Sauko Ba Har Sai Kwamishinan Kudi Na Jihar Bauchi Ya Amince Ya Fito Takarar Gwaman Bauchi A Zaben 2027

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wani Matashi Ya Dane Saman Karfen Sabis A Jihar Bauchi, Ya Ce Ba Zai Sauko Ba Har Sai Kwamishinan Kudi Na Jihar Bauchi Ya Amince Ya Fito Takarar Gwaman Bauchi A Zaben 2027 Me za ku ce?
Hukumar ‘yansandan Najeriya ta saka tarar Naira Dubu Hamsin ga matasa masu shigar banza

Hukumar ‘yansandan Najeriya ta saka tarar Naira Dubu Hamsin ga matasa masu shigar banza

Duk Labarai
Newly deployed Nigerian Formed Police Unit (FPU) personnel under the African Union Mission in Somalia (AMISOM) arrive at Aden Abdulleh International Airport, Mogadishu, Somalia on January 6, 2016. AMISOM Photo / Ilyas Ahmed Hukumar 'yansandan Najeriya reshen jihar Delta sun gargadi matasa da cewa, akwai tarar Naira Dubu 50 ga duk wanda aka kama da shigar banza. Hukumar 'yansandan jihar ta wallafa sakonne a shafinta na X ranar Asabar inda tace hakan kokari ne na wayar da kan mutane game da dokokin jihar. Hukumar 'yansandan jihar tace ta yi hakanne dan wasu zasu ce basu dan da wannan doka ba to dan a kiyaye tace zata rika wallafa irin wadannan dokoki akai-akai.
Da Duminsa: A karshe dai Hukumomin Saudiyya sun amince a binne gawar marigayi, Aminu Dantata a Madina

Da Duminsa: A karshe dai Hukumomin Saudiyya sun amince a binne gawar marigayi, Aminu Dantata a Madina

Duk Labarai
Babban sakataren marigayi Alhaji Aminu Dantata, Mustapha Abdullahi Junaid ya ce shirye-shirye sun kammala domin gudanar da jana'iza tare da binne gawar marigayin a garin Madina. Mustapha ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook, inda ya rubuta cewa, "Alhamdulillah an samu amincewar (hukumomi), za a ɗauki Aminu Alhassan Ɗantata daga Abu Dhabi zuwa Madina. Za a yi jana'iza gobe da safe in sha Allah." A safiyar jiya Asabar ne da attajirin ɗankasuwar ya rasu a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, amma iyalansa suka jinkirta binne shi domin a cewarsu, suna su ne su cika masa burinsa na kasancewar a binne a garin na Madina. An dai gudanar masa da sallar da gawa ba ta kusa a jihar Kano, wanda Sheikh Ibrahim Khalil ya jagoranta.
Mun gano Dalibai na karyar cewa su Zabaya ne dan su yi satar Amsa>>Hukumar Jarabawar JAMB

Mun gano Dalibai na karyar cewa su Zabaya ne dan su yi satar Amsa>>Hukumar Jarabawar JAMB

Duk Labarai
Hukumar shirya jarabawar share fagen shiga Jami'a JAMB ta bayyana cewa, ta gano wata dabarar satar Amsa wadda dalibai ke karyar cewa su zabayane dan yin satar Amsar. Shugaban hukumar, Professor Ishaq Oloyede ne ya bayyana hakan inda yace yawan daliban da suka yi rijistar Jarabawar a matsayin Zabaya sun yi yawa, shiyasa suka ce bari su yi bincike. Yace da suka yi bincike sai suka gano ashe wata fasahar zamani ce aka zo da ita ta satar amsa wadda kuma idan daliban basu yi karyar cewa, su Zabaya bane ba za'a barsu su rubuta jarabawar ba. Yace daga baya sun gano irin wadannan dalibai kuma ya jawo hankalin sauran daliban su kaucewa irin wannan lamari.
Zamu dasa Bishiyoyi Biliyan 20 a Najeriya cikin shekara daya>>Gwamnatin Tarayya

Zamu dasa Bishiyoyi Biliyan 20 a Najeriya cikin shekara daya>>Gwamnatin Tarayya

Duk Labarai
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa, Gwamnatin tarayya zata gina bishiyoyi biliyan 20 a Najeriya a damuna me zuwa. Ya bayyana hakane a kasar Ethiopia a yayin ziyarar da ya kai kasar bayan kai ziyara yankin da suke noma ya ga irin wannan tsari. Shettima ya bayyana cewa, dasa Bishiyoyin abune dake bukatar tsarawa da kuma wahala amma idan aka dage za'a iya yi, kamar yanda gashi kasar ta Ethiopia ta yi. Shettima ya kuma jinjinawa kasar Ethiopia bayan da ta zama kasa me cin gashin kanta ta fannin noman Alkama inda yace a baya suna sayen Alkamar Dala Biliyan $1 duk shekara amma yanzu ta wadacesu har ma sayarwa da makwabta suke. Yace hadaka tsakanin Najeriya da kasar Ethiopia zai taimaka aosai wajan ci gaban yankin Africa.
Gwamnatin tarayya zata gyarawa ma’aikata tsarin Kiwon Lafiya

Gwamnatin tarayya zata gyarawa ma’aikata tsarin Kiwon Lafiya

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta sanar da shirin gyarawa ma'aikatan ta tsarin kiwon lafiyarsu. Gwamnatin tace hakan ya zama dole musamman lura da hauhawar farashin magunguna. Gwamnatin ta bayyana hakane a yayin gwaji kyauta da kawa ma'aikatan a lokacin bikin satin ma'aikata a Abuja. Shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya, Mrs Didi Walson-Jack ce ta bayyana hakan a wajan inda tace kula da lafiyar ma'aikatan na da muhimmanci musamman lura da muhimmancin aikin da suke. Tace tsarin da ake kai a yanzu ya zama tsohon yayi yana da kyau a sake dubawa dan sabuntashi.
Wata Sabuwa: Ashe Ashe Daloline ake zargin Ganduje ya karba ya tafka magudin zabe shiyasa Tinubu ya tursasa masa sauka, ji cikakken labarin

Wata Sabuwa: Ashe Ashe Daloline ake zargin Ganduje ya karba ya tafka magudin zabe shiyasa Tinubu ya tursasa masa sauka, ji cikakken labarin

Duk Labarai
Bayan da shugaban jam'iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ajiye mukaminsa da kuma bayyana cewa zai kula da lafiyarsa ne. Bayanai na ci gaba da fitowa kan ainahin dalilin da yasa ya sauka daga mukamin nasa. Rahoton majiyarmu yace Ganduje ya Zaben babban birnin tarayya, Abuja da aka yi, an zargi Ganduje da karbar kudi ya baiwa wanda yafi bayar da kudi takarar zabe. Rahoton yace bayan kammala zaben ne wasu suka shigar da korafi inda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yasa a yi bincike. Bayan gabatarwa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da sakamakon binciken ne sai ya kira taron kungiyar Gwamnonin APC inda ya shaida musu halin da ake ciki. Sannan aka nada wasu wakilai daga cikin gwamnonin ciki hadda Mai Mala Buni suka samu Ganduje suka gaya masa ya sauka girma da arziki ko a...