Shugaba Tinubu zai kafa rundunar tsaro ta musamman a garin Zuru na jihar Kebbi
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai kafa rundunar tsaro ta musamman a garin Zuru na jihar Kebbi.
Gwamnan jihar, Nasir Idris ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yayin ziyarar ta'aziyya da ya kai kauyukan karamar hukumar Danko da Wasagu inda 'yan Bindiga suka kashe mutane 30.
Yace za'a kafa rundunar tsaronne dan inganta tsaro a jihar dama yankin baki daya.
Gwamnan yace yanzu haka ya yi kokarin an kai jami'an tsaro da makamai inda lamarin ya faru.








