Shugaba Tinubu ya taya Tsohon Shugaban kasa, Abdulsalam Abubakar murnar cika shekaru 83
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya taya tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalam Abubakar me ritaya murnar cika shekaru 83 da haihuwa.
A sanarwar da ya sanyawa hannu ranar Lahadi, Shugaba Tinubu ya bayyana Abdulsalam Abubakar a matsayin mutum me dattako wanda ke son zaman lafiya.
Yace yayi rayuwa me kyau wadda tasa ma'aikatan gwamnati da yawa ke son yin koyi dashi.








