Tuesday, December 23
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Matan Yarbawa sun yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu Alkawarin samar masa da kuri’u Miliyan 1

Matan Yarbawa sun yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu Alkawarin samar masa da kuri’u Miliyan 1

Duk Labarai
Wata Kungiyar matan yarbawa a jihar Osun ta yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu Alkawarin kuri'u Miliyan 1 a zaben 2027. Kungiyar tace shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne zabinta a zaben 2027. Matan ta bakin wakiliyarsu a jihar Osun, Adesola Ayangbil sun bayyana cewa, sun fara yakin neman zabe ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu gida'gida kamin zuwa zaben shekarar 2027. Sun bayyana hakane a ofishin yakin neman zaben Tinubu da Shettima. Sun ce sun yaba da shugabancin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a shekaru 2 da suka gabata.
Tinubu ya tseratar da Najeriya daga fadawa matsalar Talauci>>Inji Gwamnan Anambra

Tinubu ya tseratar da Najeriya daga fadawa matsalar Talauci>>Inji Gwamnan Anambra

Duk Labarai
Gwamnan jhar Anambra, Charles Soludo ya bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya tseratar da Najeriya daga fadawa kangin Talauci. Ya bayyana hakane a cikin jawabinsa na ranar 'yanci inda yace tsare-tsaren tayar da komar tattalin arziki na gwamnatin shugaban kasar na aiki yanda ya kamata. Yace tattalin arzikin Najeriya a yanzu ya dauki saiti kuma za'a iya ganin tabbacin hakan ta hanyar yabo da shugaban kasar ke samu daga hukumomin Duniya irin su IMF da bankin Duniya da sauransu. Soludo yayi kira ga jam'iyyun Siyasa da su hada kai a muradi na bai daya na ci gaban kasa.
Ko makaho yasan ina aiki a kasarnan>>Shugaba Tinubu

Ko makaho yasan ina aiki a kasarnan>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, Ko mahako yasa yana ayyukan ci gaba a Najeriya. Shugaban ya bayyana hakane yayin kaddamar da titin Apo-Wasa dake Abuja. Shugaban yace Najeriya haka take shekarun 1960 ko kuwa haka take a shekaru 3 da suka gabata? Amma 'yan Adawa babu me yabawa sai suka. Shugaban ya baiwa 'yan Adawa shawarar su mayar da hankali wajan gyara matsalarsu kamin zaben 2027 dan kada wani ya zargeshi da yin magudi. Kakakin majalisar Dattijai, Godswill Akpabio ne ya wakilci shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a wajan kaddamar da titin.
GA WANI DARASI DA YA FARU YAU: Wannan hoton wani iyali kenan da suka yi bankwana da kasar India da nufin za su je cika burinsu na komawa kasar Ingila da zama ashe ajali ke kiransu

GA WANI DARASI DA YA FARU YAU: Wannan hoton wani iyali kenan da suka yi bankwana da kasar India da nufin za su je cika burinsu na komawa kasar Ingila da zama ashe ajali ke kiransu

Duk Labarai
GA WANI DARASI DA YA FARU YAU: Wannan hoton wani iyali kenan da suka yi bankwana da kasar India da nufin za su je cika burinsu na komawa kasar Ingila da zama ashe ajali ke kiransu A Yau ta ruwaito bayanai sun nuna mijin mai suna Pratik Joshi kwarren mai masanin kwamfuta ne wanda ya dade yana mafarki kwashe iyalansa su koma Ingila da zama. Sannan matarsa sunan ta Dr. Komi Vyas wacce ta ajiye aikinta tayi bankwana da da su akan mafarkinta na komawa Ingaila da zama ya tabbata…. Kwatsam yau sun hau jirgin sama har suka yi wannan hoto suka tura wa dangi a matsayin bankwana sun bar kasa sai jirginsu kirar Air India Flight 171 ya yi hatsari kuma kusan duka fasinjoji fiye da 200 dake jirgin suka mutu Allah sarki rayuwa ashe duniyar ma za su bari! Allah ya jikan mamatanmu!
Ni Dai Ban San Inda Sauran ‘Yan Matan Fim Suka Samo Na Su GLK Din Ba, Amma Ni Tawa Baby Na Ne Ya Siya Min, Inji Samha M. Inuwa

Ni Dai Ban San Inda Sauran ‘Yan Matan Fim Suka Samo Na Su GLK Din Ba, Amma Ni Tawa Baby Na Ne Ya Siya Min, Inji Samha M. Inuwa

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Ni Dai Ban San Inda Sauran 'Yan Matan Fim Suka Samo Na Su GLK Din Ba, Amma Ni Tawa Baby Na Ne Ya Siya Min, Inji Samha M. Inuwa
Bayan da suka ta yi yawa, Ministan Abuja, Nyesom Wike yace baya dana sanin Sakawa babban dakin Taron Najeriya sunan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

Bayan da suka ta yi yawa, Ministan Abuja, Nyesom Wike yace baya dana sanin Sakawa babban dakin Taron Najeriya sunan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

Duk Labarai
'Yan Najeriya, Musamman kungiyoyin fafutuka, sun yi Allah wadai da sakawa babban dakin taron Najeriya dake Abuja sunan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Ministan Abuja, Nyesom Wike ya canjawa babban dakin taron sunane bayan da ya gyarashi. An gano akalla gurare 7 da suka hada da barikin sojoji da filin jirgin sama da sauransu wadanda aka sakawa sunan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Lamarin yasa abin ya fara damun mutane musamman masu fafutukar kare hakkin al'umma suka fara suka. Saidai a martaninsa, Wike Ya bayyana cewa duk me suka ya je yayi ta yi, yace ya ji wasu na cewa, wai ba Tinubu ne ya gina dakin taron ba. Yace to gurare da yawa da aka sakawa sunayen manyan mutane, kamar su Filin jirgin sama na Murtala Muhammad da Nnamdi Azikwe ai duk ba su ne suka ginasu ba. ...
An ga fastocin yakin neman zaben tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan a kafafen sada zumunta, Ya mayar da martani

An ga fastocin yakin neman zaben tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan a kafafen sada zumunta, Ya mayar da martani

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana fastocin yakin neman zaben tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan a kafafen sada zumunta inda aka ga yana neman tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2027. An ga fastocinne a kafar Instagram. Shafin da ya wallafa labarin na dauke da sunan tsohon shugaban kasar ne inda ya soki gwamnati me ci. Saidai da aka Tambayi kakakin Jonathan din me suna Ikechukwu Eze ya musanta cewa ba Jonathan ne ya ke yakin neman zabeba, bashi ma amfani da shafin Instagram. Ba wannan ne karin farko da ake amfani da sunan tsohon shugaban kasar ana nuna yana neman sake tsayawa takarar shugaban kasa ba, ko da a shekarar 2023 ma an samu wasu suka rika amfani da sunansa suna cewa ya fito takarar shugaban kasa.
Gwamnatin Tarayya da hadin kan kasar China zata tayar da kamfanin karafa na Ajakuta

Gwamnatin Tarayya da hadin kan kasar China zata tayar da kamfanin karafa na Ajakuta

Duk Labarai
Gwamnatin Tarayya a ranar Juma'a ta bayyana aniyarta ta son tayar da kamfanin Karafa na Ajakuta dan kirkiro ayyukan yi ga matasa. Gwamnatin tace Tuni ta fara hadaka da kamfanonin kasar China da kuma neman kudi dan tayar da kamfanin da ya dade a lalace. Hakan na cikin shirin ministan Karafa, Shuaibu Audu wanda a yanzu haka yake jagorantar wata tawaga daga Najeriya zuwa kasar China dan jawo hankalin masu zuba Jari zuwa Najeriya. Hadimin Ministan, Lizzy Okoji ya bayyana cewa, tuni tawagar ta fara ganawa da kamfanonin kasar China irin su Sino Steel, da Fangda Steel da Jingye Steel. Ministan yace dawo da kamfanin karafan na Ajakuta ya ci gaba da aiki na daya daga cikin abubuwan da gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta sanya a gaba kuma zasu cimma nasara kamin karshen mulkins...
Kasar Pakistan ta bayyana goyon baya ga Ìràn

Kasar Pakistan ta bayyana goyon baya ga Ìràn

Duk Labarai
Kasar Pakistan ta bayyana cewa, tana goyon bayan kasar Iran a ci gaba da gumurzun da suke da kasar Israyla. Pakistan ta yi Allah wadai da hare-haren da kasar ta Israyla ta kaiwa Iran inda a wasu rahotannin ta bayyana cewa, a shirye take ta goyi bayan Iran a wannan rikici. A jiyane dai yaki ya barke tsakanin Israyla da Iran inda Israyla ta fara kaiwa Iran hari inda ta kashe manyan sojojinta da dayawa daga cikin masana kimiyyar ta. Kasar dai ta zargi Iran da yunkurin mallakar makamin Kare dangi wanda tace ba zata amince da hakan ba. Israyla ta kaiwa Iran hare-hare akan tashar inganta makamin kare danginta. Saidai daga baya itama iran ta yi ramuwar gayya.
An gano Majalisar tarayya ta cusa jimullar Naira Tiriliyan 10.96 a cikin kasafin kudin Najeriya cikin shekaru 4

An gano Majalisar tarayya ta cusa jimullar Naira Tiriliyan 10.96 a cikin kasafin kudin Najeriya cikin shekaru 4

Duk Labarai
Wasu kungiyoyin fafutuka sun yi Allah wadai da majalisar tarayya saboda cusa jimullar Naira Tiriliyan N10.96tn a cikin kasafin kudin Najeriya a tsakanin shekarun 2021 zuwa 2025. Kungiyoyin sun bayyana hakan da cewa bai dace ba inda suka nemi hukumomin yaki da rashawa da cin hanci na Najeriya dasu yi bincike kan wannan zargin. Kungiyoyin da suka yi wannan zargin sune the Socio-Economic Rights and Accountability Project, da kuma the Centre for Anti-Corruption and Open Leadership. Kungiyar BudgIT ce ta fara yin wannan bincike inda tace jimullar ayyukan da aka cusa a cikin kasafin kudin sun kai 30,632.