Tuesday, April 21
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Abin Kunya: Kalli yanda aka bar Gurin da aka warewa Najeriya a taron kasashe dake gudana a Birnin Tokyo na kasar Japan ba kowa, yayin da sauran kasashen Duniya suke tsaye a wajen nasu

Abin Kunya: Kalli yanda aka bar Gurin da aka warewa Najeriya a taron kasashe dake gudana a Birnin Tokyo na kasar Japan ba kowa, yayin da sauran kasashen Duniya suke tsaye a wajen nasu

Duk Labarai
Wani dan Najeriya me suna Idris Ayo Bello ya bayyana yanda da ya halarci wajan taron ci gaban Afrika da aka gudanar a birnin Tokyo na kasar Japan da kuma abin kunyar da ya gani. Yace wajan da aka warewa Najeriya ta tsaya babu kowa a wajan. Yace da ya ga abin yayi yawa, shine da kansa ya je wajan ya tsaya ya kuma rika amsa tambayoyi akan kasuwancin Najeriya da ci gabanta da wasu 'yan kasashe ke yi. Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dai ya halarci wajan taron, kuma rahotanni sun bayyana cewa, an tanadi mutanen da zasu tsaya a irin wannan waje dan wakiltar Najeriya.
EFCC zata fara binciken tsohon shugaban NNPCL, Mele Kolo Kyari kan zargin satar Dala Biliyan $7.2 na gyaran matatun man fetur

EFCC zata fara binciken tsohon shugaban NNPCL, Mele Kolo Kyari kan zargin satar Dala Biliyan $7.2 na gyaran matatun man fetur

Duk Labarai
Hukumar hana yiwa tattalin arziki kasa zagon kasa, EFFC ta bayyana cewa, zata fara binciken tsohon shugaban NNPCL, Mele Kolo Kyari kan zargin satar Dala Biliyan $7.2 na gyaran matatun man Najeriya. Hakan na zuwane bayan da tuni kotu ta kulle asusun ajiyarsa na banki guda 4 dake dauke da makudan kudade. Rahoton Daily Trust yace tuni aka fara binciken wasu na kusa da Kyari inda EFCC tace tana son samun isassun bayanai akanshi kamin ta fara bincikenshi. Game da cewa, Kyari baya Najeriya, Hukumar tace wannan ba matsala bane da zarar sun bukaci kamashi ko bincikenshi kamashi ba abune me wuya ba.
Dan majalisar dokoki na majalisar jihar Nasarawa, Musa Gude ya dauki hankula saboda nada masu taimaka masa guda 106

Dan majalisar dokoki na majalisar jihar Nasarawa, Musa Gude ya dauki hankula saboda nada masu taimaka masa guda 106

Duk Labarai
Dan majalisar wakilai na majalisar jihar Nasarawa, Musa Gude ya nada masu taimaka masa guda 106. Ya bayyana hakane a hirar da yayi da kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN inda yace ya nada mutane 106 a matsayin masu taimaka masa ne dan ya tallafawa rayuwarsu. Yace daga ciki akwai wadanda yake biya albashin Naira Dubu 10 har zuwa Dubu 100. Dan majalisar wanda a jam'iyyar SDP yake daga mazabar Uke/Karshi yace ya tallafawa mutane a bangarori daban-daban da suka hada da Noma, ilimi, da sauransu.
Zamu Tùbè kayan mu, mu yi Tumbur mu nuna komai mu yi zànga-zànga tsyrara idan ba a daina rushe mana gidaje ba>>Inji Matan Legas

Zamu Tùbè kayan mu, mu yi Tumbur mu nuna komai mu yi zànga-zànga tsyrara idan ba a daina rushe mana gidaje ba>>Inji Matan Legas

Duk Labarai
Mata a birnin Legas sun yi barazanar yin zanga-zangar tsirara dan tursasa daina rushe musu gidaje. Matan daga yankin Ilaje sun yi zanga-zangar lumana zuwa majalisar dokokin jihar ta Legas inda suka nemi taimakon gwamnan jihar, Babajide Sonwo Olu da kakakin majalisar Dokokin jihar,Mudashiru Obasa su saka baki a daina rushe musu gidaje. Sun zargi sarakunan gargajiyarsu da yi musu kwacen gidaje. Daya daga cikin matan wadda dattijuwa ce, ta fito inda take barazanar cewa, zasu yi zanga-zanga tsirara idan ba a daina rushe musu gidaje ba. Shima shugaban mazauna yankin na Ilaje, Rafael Irowainu ya bayyana cewa wasu sarakuna na amfani da sunan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu suna rushe gidaje dan su yi gine-gine. Ya kara da cewa, amma basu yadda shugaba ne ya aika mutanen ba.
Sai an kawo mana dauki, Lamuran tsaro sun ta’azzara>>Inji Gwamnan riko na jihar Katsina, wanda Gwamna Radda ya barwa jihar a hannunsa

Sai an kawo mana dauki, Lamuran tsaro sun ta’azzara>>Inji Gwamnan riko na jihar Katsina, wanda Gwamna Radda ya barwa jihar a hannunsa

Duk Labarai
Gwamnan riko na jihar Katsina wanda gwamna Dikko Radda ya barwa jihar a hannunsa Malam Faruk Lawal-Jobe ya yi kira ga gwamnatin tarayya data kawo musu dauki a jihar game da tabarbarewar lamuran tsaro. Wannan kira nasa na zuwane bayan harin da 'yan Bindiga suka kai unguwar Muntau dake garin Malunfashi a jihar Katsina suka kashe mutane akalla 13 dake sallar Asuba. Hakanan maharan sun rika harbin kan mai uwa da wabi inda kuma suka sace mutane 60, kamar yanda kafar Rariya ta tuwaito. Hakan na zuwane a yayin da Gwamna Dikko Radda ke kasashen Turawa nema Lafiya amma an hangoshi a wasu hotuna yana daukar hoton garin da yaje. Gwamnan rikon, Malam Faruk Lawal-Jobe ya nemi gwamnatin tarayya data kawowa jihar dauki lura da yanda lamuran tsaro suka tabarbare tare da neman Shugaban kasa ya ...