Monday, December 22
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Sanata Kalu ya fasakwai inda ya Bayyana masu daukar nauyin Ayyukan tà’àddàncì a Najeriya

Sanata Kalu ya fasakwai inda ya Bayyana masu daukar nauyin Ayyukan tà’àddàncì a Najeriya

Duk Labarai
Sanata Orji Uzor Kalu dake wakiltar mazabar Abia North a majalisar Dattijai ya bayyana cewa wasu 'yan siyasa ne da manyan ma'aikatan Gwamnati da 'yan Kasuwa ke daukar nauyin ayyuka Kungiyar Bòkò Hàràm. Ya bayyana hakanne a hirar da aka yi dashi a gidan Talabijin na Channels TV. Yace kuma masu yin hakan suna yi ne dan kawai su hana shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu iya gudanar da Gwamnatinsa yanda ya kamata. Yace amma ba ta haka bane ake karbar mulki, yace yawanci suna yi ne dan su kwace mulki daga hannun Tinubu ba kudi bane a gabansu.
Gwamnatin Tarayya zata biya bashin Naira Tiriliyan 2 na kudin wutar lantarki

Gwamnatin Tarayya zata biya bashin Naira Tiriliyan 2 na kudin wutar lantarki

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ta fara amincewa da batun biyan bashin Naira Tiriliyan 2 na wutar lantarki da akw binta. Hakan kokarine na samar da ingantacciyar wutar Lantarki a Najeriya. Na kusa da me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar makamashi, Eriye Onagoruwa ce ta bayyana hakan a wajan wani taron masu ruwa da tsaki na harkar wutar da aka gudanar. Tace gwanatin na duba muhimmancin hakan wajan samar da wutr Lantarki me karfi. Inda tace gwamnatin na kokarin ganin ta samar da wata hanya ta bashi dan biyan wannan bashi musaman lura da karancin kudin da gwamnatin ke fama dashi.
Kalli Bidiyon: Mutum daya ya rasu, 69 sun jikkata yayin girgizar kasa a Turkiyya

Kalli Bidiyon: Mutum daya ya rasu, 69 sun jikkata yayin girgizar kasa a Turkiyya

Duk Labarai
Girgizar kasa ta faru a kasar Turkiyya inda mutane 69 suka jikkata. Yawanci wadanda suka jikkatar sun diro ne daga benaye saboda fargabar kada gidan da suke ciki ya rushene. Saidai mutum daya ya mutu. Karfin girgizar kasar ya kai maki 6.2 kamar yanda masana suka sanar. https://twitter.com/geotechwar/status/1929690994091741373?t=qa7qPmG2xXaNo2yyCcmrog&s=19 Kasar Turkiyya dai na daga cikin kasashe masu yawan fuskantar Ambaliyar ruwa.
Da Duminsa: Wani Dan Bìndìgà da yafi Bèllò Tùrjì rashin Imagi da hadari ya bayyana, ji mummunar ta’asar da ya aikata

Da Duminsa: Wani Dan Bìndìgà da yafi Bèllò Tùrjì rashin Imagi da hadari ya bayyana, ji mummunar ta’asar da ya aikata

Duk Labarai
Rahotanni sun ce wani dan Bindiga me suna Dan Sadiya ya bayyana inda aka bayyana shi da cewa yafi Bello Tùrji illa. Rahoton yace ya jagoranci kai hare-hare a jihar Zamfara wanda suka yi sanadiyyar kashe fararen hula da kuma kona kauyuka. A cikin wasu Bidiyon da ya saki an ga ya nuna motar APC ta sojojin Najeriya da ya kwace wadda ake amfani da ita ana harbo jirgin sama. An yi kira ga jami'an tsaro da su gaggauta daukar mataki akansa. https://twitter.com/Edrees4P/status/1929462831486804314?t=oL_F3FzI0FsqZR9Rrwi0EQ&s=19 Ko kuna ganin wane mataki ya kamata a dauka akansa?
Da Dumisa: Kasar Sifaniya ta bi sahun kasar Afrika ta kudu wajan kai karar kasar Israyla kan kìsàn kiyashin da takewa Falasdiynawa

Da Dumisa: Kasar Sifaniya ta bi sahun kasar Afrika ta kudu wajan kai karar kasar Israyla kan kìsàn kiyashin da takewa Falasdiynawa

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Spain na cewa kasar ta bi sahun kasar Afrika ta Kudu wajan kai karar kasar Israyla kotun Duniya saboda zargin kisan kiyashi da Israyla kewa Falasdinawa. Kasar Sifaniya dai ta dade tana kira ga kasashen Turawa da su kakabawa kasar Israyla takunkumi saboda kisan da takewa falasdinawa. A kwanannan ne dai Birnin Barcelona na kasar ya yanke dukkan wata hulda da kasar Israela saboda kisan da sukewa Falasdiynawa. Kasar Afrika ta kudu itace kasa ta Farko a Duniya data fara kalubalantar kasar Israela saboda kisan da takewa Falasdiynawa.
Nine kashin bayan Nasarar Tinubu ya zama shugaban kasa, Kuma idan PDP ta isa ta dakatar dani>>Wike

Nine kashin bayan Nasarar Tinubu ya zama shugaban kasa, Kuma idan PDP ta isa ta dakatar dani>>Wike

Duk Labarai
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa, shine kashin bayan nasarar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi nasarar zama shugaban kasa a shekarar 2023. Ya kuma bayyana aniyarsa ta goyon bayan shugaba Tinubun a zaben shekarar 2027. Saidai hakan baiwa jam'iyyun adawa dadi ba inda suke ta sukarsa. Jam'iyyun da suka soki Wike kan bayyana ci gaba da goyon bayan shugaban kasa Bola Tinubu sun hada da NNPC, PDP, CUPP. Wike ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu ne a wata ganawa da yayi da manema labarai a Abuja ranar Litinin. Wike yace bai aikata laifin yiwa jam'iyyarsa ta PDP zagon kasa ba inda ya kalubalanci jam'iyyar da cewa idan kuma ya aikata laifin to su dakatar dashi. Saidai mataimakin shugaban matasa na jam'iyyar PDP na kasa, Timothy Osadolor ya gayawa '...
A karshe dai da suka ga ba zasu iya hanata ba, Yanzu kasar Amurka tace ta yadda kasar Iran ta ci gaba da kokarin mallakar makamin kare dangi amma bisa sharudin ta daina gaggawa wajan inganta Makamin Uraniyum, ta rika yi a hankali

A karshe dai da suka ga ba zasu iya hanata ba, Yanzu kasar Amurka tace ta yadda kasar Iran ta ci gaba da kokarin mallakar makamin kare dangi amma bisa sharudin ta daina gaggawa wajan inganta Makamin Uraniyum, ta rika yi a hankali

Duk Labarai
Rahotanni dake fitowa daga tattaunawar kasar Iran da kasar Amurka akan shirin mallakar makamin kare dangi na kasar Iran din na cewa an samu sauyi. Rahoton yace, a yanzu kasar Amurka ta amince kasar Iran ta ci gaba da inganta makamashin Uraniyum da zai bata damar mallakar makamin Nokiliya. Saidai sharadi shine kada ta rika yin hakan da gaggawa kamar yanda take yi a yanzu. Hakan na zuwane bayan da labarai suka bayyana cewa kasar ta Iran ta inganta makamin Uraniyum zuwa matakin kaso 60 cikin 100 wanda kiris ya rage mata ta kai matakin 90 cikin 100 wanda shine zai bata damar mallakar makamin kare dangi. Hakanan a baya, kasar Iran ta rika yin watsi da bukatocin kasar Amurka na cewa ta daina inganta makamashin Uraniyum. Wannan dai ba karamar nasara bace ga kasar Iran musamman i...
Mutumin Bauchi Zai Kai Ragon Sallah Gidan Tinubu

Mutumin Bauchi Zai Kai Ragon Sallah Gidan Tinubu

Duk Labarai
Mutumin Bauchi Zai Kai Ragon Sallah Gidan Tinubu A Legas Bayan Yunkurin Da Bai Kai Ga Nasara Ba. {"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Khamis Musa Darazo, wani masoyin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu daga jihar Bauchi, ya shirya kai wa shugaban kasa ragon Sallah a Legas a matsayin alamar godiya bisa amincewar da ya yi da lasisin hakar mai a Kolmani. A wata hira da aka yi da shi ranar Litinin, Khamis ya shaida wa Vanguard cewa bayan tattaunawa da dattawa, ya yanke shawarar kai ragon zuwa jiharsa ta asali — Legas, da f...
Yadda shan shìshà ke iya hana mata haihuwa

Yadda shan shìshà ke iya hana mata haihuwa

Duk Labarai
Hukumar lafiya ta duniya ta yi kira ga gwamnatoci da su haramta ko taƙaita amfani da sabon salo na nau'ukan tabar sigari masu ɗanɗano da ƙamshi kamar shisha da sigari mai amfani da wutar lantarki wato e-sigarrete da hookah da dai sauransu. Hukumar ta yi wannan kira ne saboda munanan illolin da ta ce ta gano da ke tattare da sigarin ga mashayanta wajen kamuwa da cututtuka masu alaƙa da lafiyar huhu da sauransu. Hukumar ta kuma gano cewa sabon salon sigarin masu ɗanɗano da ƙamshi ne ke jan hankalin matasa har ta zame musu jiki. Likitoci sun yi ƙarin haske kan illar da wannan sigari mai sabon salo da danginta ke haifarwa, inda suka yi nuni da cewa sinadarin da ke cikin tabar na iya haifar da matsalar numfashi har ma idan ba a yi sa'a ba ya kai ga mutuwa. Farfesa Maimuna Aminu Kani...