Sunday, December 21
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Mùtùwàr ‘yan Kwallon Kano, da Mùtùwàr mutane a Ambaliyar ruwan Jihar Naija, Kunki dakar mataki, kun bari mutane na ta mùtùwà>>Atiku Abubakar ya caccaki Gwamnatin Tinubu

Mùtùwàr ‘yan Kwallon Kano, da Mùtùwàr mutane a Ambaliyar ruwan Jihar Naija, Kunki dakar mataki, kun bari mutane na ta mùtùwà>>Atiku Abubakar ya caccaki Gwamnatin Tinubu

Duk Labarai
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin tarayya inda yace basu dauki matakan da ya kamata ba gashi mutane na ta mutuwa. Ya bayyana hakane a sakon ta'aziyya ga iyalan 'yan kwallon Kano 22 da suka rasu a hadarin Mota. Inda yace ba iyalansu kadaine suka yi asararsu ba, hadda ma Najeriya baki daya. Ya kuma bayyana Alhinin rasuwar mutane sama da 100 a ambaliyar ruwan garin Mokwa dake jihar Naira inda yace abin takaici ne. Atiku ya baiwa Gwamnatin tarayya shawarar ta dauki matakan kula da titinan Najeriya dan rage ko kawar da yawaitr hadurra. Sannan ya nemi da a dauki matakan hana ambaliyar ruwa musamman yanzu da ake fuskantar yawaitar ruwan sama.
Kasar Saudiyya ta dakatar da bayar da Bizar zuwa aiki ga ‘yan Najeriya

Kasar Saudiyya ta dakatar da bayar da Bizar zuwa aiki ga ‘yan Najeriya

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Kasa Saudiyya ta dakatar da bayar da Bizar aiki ga 'yan Najeriya da sauran kasashe masu yawa. Kasashen da wannan lamari ya shafa sun hada da Indonesia, Iraq, Jordan, Yemen, India, Pakistan da Bangladesh. Sauran sune Egypt, Algeria, Sudan, Ethiopia, Tunisia da Morocco. Rahoton yace, Ma'aikatar kula da ci gaba al'umma da kasar Saudiyyar ne ta sanar da hakan. Kuma an dauki wannan mataki ne dan baiwa mahajjata damar gudanar da aikin Hajji, idan aka kammala aikin Hajji nan da karshen watan Yuni za'a ci gaba da bayar da bizar.
Shekaru 2 sun yi kadan ace za’a duba a ga na yi kokari ko ban yi ba, Kamata yayi sai nan da shekaru 10 zuwa 12 kamin ace za’a min hukunci kan mulkin Najeriya>>Tinubu

Shekaru 2 sun yi kadan ace za’a duba a ga na yi kokari ko ban yi ba, Kamata yayi sai nan da shekaru 10 zuwa 12 kamin ace za’a min hukunci kan mulkin Najeriya>>Tinubu

Duk Labarai
A yayin da ya cika shekaru 2 da mulki, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, shekaru 2 sun yi kadan ace za'a duba a ga yayi kokari ko bai yi kokari ba. Yace yawanci masana sun ce sai an shekara 10 zuwa 12 idan aka samu canji sannan a duba a ga ko an samu ci gaba ko ba'a samu ba. Ya bayyana hakanne ta bakin kakakinsa, Bayo Onanuga. Shugaban yace nan ba da jimawa ba 'yan Najeriya zasu ga alfanun matakan gyara tattalin arziki da ya dauka.
Sanata Natasha Akpoti zata gurfana a gaban kotu bisa karar da Gwamnatin Tarayya ta kaita na bata suna

Sanata Natasha Akpoti zata gurfana a gaban kotu bisa karar da Gwamnatin Tarayya ta kaita na bata suna

Duk Labarai
A ranar Talata me zuwa ne ake sa ran Sanata Natasha Akpoti zata gurfana a gaban kotu. Rahotanni sun bayyana cewa, Lauyan Sanata Natasha, West Idahosa (SAN) ne ya bayar da tabbacin. Yace a matsayin sanata Natasha na 'yar kasa ta gari me bin doka, zata bayyana a gaban kotun kamar yanda aka bukata. Gwamnatin Tarayya ta shigar da karar Sanata Natasha Akpoti ne ta hannun wailinta, Mohammed Abubakar inda take zargin Natasha da bata suna. Gwamnatin ta yi zargin Sanata Natasha Akpoti tace wai kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello sun yi yunkurin kasheta. Sannan tace wai Sanata Godswill Akpabio yana safarar sassan jikin dan adam kamar yanda ta gayawa wata mata. Daga cikin shaidun da gwamnatin tarayya zata gabatar a wannan kar...
Ku yi hankali,Masu ikirarin Jìhàdì na son mamaye kasarku>>Kasar Amurka ta gargadi Najeriya

Ku yi hankali,Masu ikirarin Jìhàdì na son mamaye kasarku>>Kasar Amurka ta gargadi Najeriya

Duk Labarai
Kasar Amurka ta gargadi Najeriya da cewa, Masu ikirarin Jìhàdì na kokarin mamaye kasar. Amurka tace bama Najeriya kadai ba, masu ikirarin jihadin na son mamaye kasashe irin su Mali, Burkina Faso, da Niger. Kwamandan rundunar sojojin Amurka dake Africa, Gen Michael Langley ne ya bayyana hakan inda yace Hare-haren masu ikirarin Jìhàdì a Najeriya abin damuwane. Yace masu ikirarin jihadin nason yin Amfani da yankin kasashen African dan gudanar da safarar makamai da fasa Kwauri. Yankin na Sahel Africa na daga cikin wanda aka bayyana dake fuskantar mafi munin hare-haren masu ikirarin Jìhàdì.
ABIN MAMAKI: Ji yanda ake zargin ‘Yan Ķasar Indiýa Sùn Ķori ‘Ýan Nijeriya Daga Nìjeriya

ABIN MAMAKI: Ji yanda ake zargin ‘Yan Ķasar Indiýa Sùn Ķori ‘Ýan Nijeriya Daga Nìjeriya

Duk Labarai
ABIN MAMAKI: 'Yan Ķasar Indiýa Sùn Ķori 'Ýan Nijeriya Daga Nìjeriya. Ɗan jarida Nasiru Zango ya rubuta yana mai cewa wannan hoto da kuke gani dake nuna wasu matasa biyu da 'yan sandan Nijeriya ke neman su ruwa a jallo ba kayan kowa suka sata ba kuma ba su yiwa kowa komai ba, babban laifin su bai wuce kasancewar su jajirtattun matasa masu neman abin kan su ba ta hanyar da dokar Nijeriya ta tanada, sai kuma watakila dan sun kasance masu karamin karfi da suka ki yadda wani babban kamfani ya zo har kasar su yana kokarin murkushe su ba. Fiye da shekara kenan wani babban kamfani na 'yan asalin Indiya ya yi karar wadannan matasa wadanda sune suke da mallakin kamfanin ganyen shayin Y and Z kan cewar sun satar musu samfurin ganyen shayin su (kamar yadda Coca Cola suka taba yin karar Pop C...
Ku Godewa Allah: Rababa muke sayar muku da man fetur idan aka kwatanta da farashin man fetur din a sauran kasashen Africa>>Dangote ya gayawa ‘yan Najeriya

Ku Godewa Allah: Rababa muke sayar muku da man fetur idan aka kwatanta da farashin man fetur din a sauran kasashen Africa>>Dangote ya gayawa ‘yan Najeriya

Duk Labarai
Babban Attajirin Najeriya wanda ya mallaki matatar man fetur mafi girma a Nahiyar Africa, Aliko Dangote yacewa 'yan Najeriya suna cikin Alheri da sa'a dan kuwa suna sayen man fetur a farashi kasa da wanda sauran kasashen Africa ke saye. Dangote yace farashin man fetur a Najeriya yana ana sayar dashi ne kaso 55 cikin 100 kasa da farashin da ake sayarwa a sauran kasashe. Watau 'yan Najeriya na siyan man fetur din a farashib kaso 45 cikin 100 idan aka kwatanta da sauran kasashen Africa. Dangote yace kuma matatar mansa ta taimaka wajan rage farashin man fetur din a Najeriya daya tsaya a farashin tsakanin Naira 815 zuwa Naira 820 akan kowace lita. Dangote ya bayyana hakanne a yayin da shugaban Kungiyar ECOWAS, Dr Omar Touray da tawagarsa suka kai mai ziyara matatar tasa. Yace za...
Matar Wannan mutumin ta ràsù a ambaliyar ruwan data faru a Mokwa jihar Naija, hakanan jaririnsa da ‘yan uwansa 7 duk sun ràsù da kayan jikinsa kawai ya tsira

Matar Wannan mutumin ta ràsù a ambaliyar ruwan data faru a Mokwa jihar Naija, hakanan jaririnsa da ‘yan uwansa 7 duk sun ràsù da kayan jikinsa kawai ya tsira

Duk Labarai
Wannan mutumin me suna Adamu Yusuf ya rasa iyalansa guda 9, matarsa daya da jaririn dansa da 'yan uwansa 6 a ambaliyar ruwan da ta faru a Mokwa dake jihar Naija. Shi ya fitone daga Tiffin Maza daya daga cikin kauyukan da lamarin ya fi shafa. Yace da suka ji ruwan, sun fito waje inda yake kowa ya rike hannun kowa yace amma da ruwan yayi karfi sai ya tarwatsasu, yace yana ji yana gani haka ruwan ya tafi da iyalinsa. Yace shima Allah ne ya tseratar dashi saboda ya iya ruwa. Yace kayan dake jikinsa ma taimako aka bashi.
Tsohon Ministan Muhalli lokacin Buhari ya bar jam’iyyar APC

Tsohon Ministan Muhalli lokacin Buhari ya bar jam’iyyar APC

Duk Labarai
Tsohon Ministan Muhalli a zamanin Mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, watau Mohammed Abdullahi ya bar jam'iyyar APC. A karkashin Mulkin Buhari an nada Muhammad Abdullahi a matsayin karamin Ministan Kimiyya da Fasaha kamin daga baya aka mayar dashi ministan Muhalli. Ya bayyana barin jam'iyyar APC ne a wasikar da ya aikewa jam'iyyar reshen mazabar sa dake Uke ward karamar hukumar Karu, Jihar Nasarawa. Ya bayyana dalilai na kashin kansa ne suka sa ya bar jam'iyyar inda yace ya gode da damar da aka bashi ta gina jam'iyyar tare dashi. A baya kamin ya zama Ministan, ya rike mukamai da yawa a jihar Nasarawa ciki hadda babban sakataren gwamnati da Kwamishina.
Kasashen Larabawa sun yi Allah wadai da kasar Israyla saboda hanasu kaiwa Falasdiynawa ziyara da ta yi

Kasashen Larabawa sun yi Allah wadai da kasar Israyla saboda hanasu kaiwa Falasdiynawa ziyara da ta yi

Duk Labarai
Ministocin harkokin wajen ƙasashen Larabawa sun bayyana rashin jin daɗinsu ga gwamnatin Isra'ila, game da rashin amincewa da tawagar ƙungiyar ƙasashen ta ziyarci yankin da aka mamaye a Gaɓar Yamma da kogin Jordan don tattaunawa da shugaban Falasɗinawa. A wani taron manema labarai, ministan harkokin wajen Saudiyya, Yarima Faisal bin Farhan Al Sa'ud, ya ce matakin da Isra'ila ta ɗauka kamar watsi ne da tayin zaman lafiya. A ranar Asabar wani jami'in Isra'ila ya ce batun samar da ƙasar Falasɗinu ne manufar ziyarar. Cikin wata sanarwar haɗin-gwiwa, ƙasashen Masar da Qatar sun ce za su ruɓanya ƙoƙarinsu don a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza. Shugaban ƙungiyar ƙasashen Larabawa da ministoci huɗu sun gana da shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas ta kafar Intanet....