Zai yi wuya Kwankwaso ya marawa Tinubu baya a 2027 – Buba Galadima
Zai yi wuya Kwankwaso ya marawa Tinubu baya a 2027 - Buba Galadima.
Buba Galadima, jigo a jam’iyyar NNPP kuma na kusa da tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce zai yi matuƙar wuya Kwankwaso ya haɗa kai da jam’iyyar domin mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaɓen 2027.
Galadima ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels , inda ya zargi gwamnatin Tinubu da nuna adawa ga Kwankwaso ta hanyar goyon bayan Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, duk da cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta tsige shi.
Ya ce Kwankwaso ba ya buƙatar dogaro da APC a siyasa, yana mai tunatar da cewa ya kayar da jam’iyyar a Kano a baya.
“Kwankwaso bai taɓa gaya min cewa zai mara wa Tinubu baya a 2027 ba,” in ji shi.
Galadima ya ƙar...








