Tuesday, December 16
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Dama Ance Almajirine: Bidiyon yanda Garzali Miko ke loma da abinci ya dauki hankula

Dama Ance Almajirine: Bidiyon yanda Garzali Miko ke loma da abinci ya dauki hankula

Duk Labarai
An ga tauraron mawakin Hausa da Fina-finan Hausa, Garzali Miko yana loma da abinci. Lamarin ya dauki hankula inda akai ta mamakin ganin Cele kamarsa yana cin abinci haka a bainar jama'a. Mutane sun bayyana mabanbanta ra'ayoyi akan lamarin. Kalli Bidiyon: https://www.tiktok.com/@kb_international/video/7503462197612268806?_t=ZM-8wIZ78X0GYv&_r=1 Saidai shi bai damu ba.
Ashe Gaba da Gabanta: Kalli Bidiyon yanda Soja Boy me wakar Badala ya gamu da wata da ta fishi iya Rashin Kunya

Ashe Gaba da Gabanta: Kalli Bidiyon yanda Soja Boy me wakar Badala ya gamu da wata da ta fishi iya Rashin Kunya

Duk Labarai
Tauraron Me wakar badala, Soja Boy ya hadu da wata me suna Fatima wadda yace ta fi karfinsa. Soja Boya ya hadu da Fatima ne a Live da yake yi a Tiktok. Ta yi ta masa maganganun batsa wanda a karshe dai ya saki kari yace ta fi karfinsa. Kalli Bidiyon anan: https://www.tiktok.com/@just_plt_umar/video/7502220924490403078?_t=ZM-8wIXBT6H56t&_r=1 Da yawa sun ce ashe gaba da gabanta.
Idan kuna son kanku da Arziki kada ku baiwa dan Arewa tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a 2027 idan kuwa kuka yi hakan to mutuwa zaku yi murus>>Wike ya gargadi jam’iyyar PDP

Idan kuna son kanku da Arziki kada ku baiwa dan Arewa tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a 2027 idan kuwa kuka yi hakan to mutuwa zaku yi murus>>Wike ya gargadi jam’iyyar PDP

Duk Labarai
Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike ya gargadi jam'iyyar PDP da cewa kada su baiwa dan Arewa tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2027. Ya bayyana hakane a yayin ganawa da manema labarai a Abuja. Wike yace irin wannan abin kashe jam'iyya yake. Yace misali yanzu ita APC idan Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kammala wa'adinsa a shekarar 2031, dan Kudu zata baiwa ya tsaya takara, to a wancan lokacin kuma sai PDP tace itama tunda APC ta ba dan kudu bari ta ba dan Arewa? Ana zargin dai Wike da Atiku yake duk da be kira suna ba.
Yanzu-Yanzu: Bàm ya fashe a Dogon Waya kan titin  Damboa-Maiduguri

Yanzu-Yanzu: Bàm ya fashe a Dogon Waya kan titin Damboa-Maiduguri

Duk Labarai
Rahotanni da muke samu na cewa Bam ya fashe a Dogon Waya kusa da Maiduguri dake kan titin Damboa zuwa Maiduguri. Bam din ya kashe Wani fashinjan motar wanda namiji ne sai kuma Direban motar da wata mata sun jikkata. Direban na dauke da Tumaki ne da yawa wadanda suka sun mutu, kamar yanda kafar Malik Samuel ta Ruwaito. https://twitter.com/Sazedek/status/1921934917950230765?t=rhAXbmg8y1JjXieC9Snytw&s=19 Allah ya kyauta.
Dan majalisar dokokin jihar Kano ya fice daga NNPP zuwa APC

Dan majalisar dokokin jihar Kano ya fice daga NNPP zuwa APC

Duk Labarai
Dan majalisar dokokin jihar Kano ya fice daga NNPP zuwa APC. Dan majalisar dokoki ta jihar Kano mai wakiltar mazabar Sumaila, Hon. Zubairu Hamza Masu, ya fice daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC. A cikin wata wasikar murabus da ya aike wa Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Ismail Falgore, Hon. Masu ya bayyana rikice-rikicen cikin gida da shari'o’in da suka addabi NNPP a matsayin babban dalilinsa na barin jam’iyyar. Kakakin Majalisar, wanda ya karanta wasikar a zauren majalisar yayin zaman ranar Litinin, ya sanar da murabus din Masu daga jam’iyyar tun daga ranar 12 ga Mayu, 2025, tare da tabbatar da cikakken biyayyarsa ga jagorancin jam’iyyar APC daga matakin mazaba har zuwa jiha da kasa baki daya. Dan majalisar ya kara da cewa wasu mutane da dama daga matakin jiha da na kasa su...
Kalli Hoto: An ga gawar wata Budurwa da aka kàshè aka yanke mata al’au7ra

Kalli Hoto: An ga gawar wata Budurwa da aka kàshè aka yanke mata al’au7ra

Duk Labarai
Mutanen garin Abeokuta jihar Ogun sun tashi da wani abin mamaki inda aka ga gawar wata mata akan titin OGTV. An gano cewa bayan kasheta an kuma yanke mata al'aura. Lamarin ya farune ranar Talata inda tuni aka kaiwa 'yansanda korafi. Ba'a dai gano wanda suka yi wannan aika-aika ba amma an yi amannar cewa tsafi ne suke son yi musamman da al'aurarta da suka cire. Tuni aka kai gawarta Mutuware.
Shugaban kasar Korea ta Arewa ya aikewa da matashin shugaban kasar Burkina Faso, Ibrahim Traore da sojoji su bashi kariya bayan da aka yi yunkurin hambarar dashi

Shugaban kasar Korea ta Arewa ya aikewa da matashin shugaban kasar Burkina Faso, Ibrahim Traore da sojoji su bashi kariya bayan da aka yi yunkurin hambarar dashi

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Burkina Faso na cewa, shugaban kasar Korea ta Arewa, Kim Jong un ya aikewa da shugaban kasar, Ibrahim Traore da sojoji dan su bashi kariya. Hakan na zuwane bayan da aka yi yunkurin kifar da gwamnatinsa inda wasu rahotanni suka ce an baiwa hadiman Shugaba Traore makudan kudade su hambarar dashi amma suka kiya.
Kalli Kwalliyar da Rahama Sadau ta yi zuwa wajan Bikin Rarara

Kalli Kwalliyar da Rahama Sadau ta yi zuwa wajan Bikin Rarara

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau kenan a wadannan hotunan nata data sha kwalliya wadda da itace ta je wajan bikin Rarara da A'ishahumaira.
Ana kiran EFCC ta kama Tubabben tsageran Niger Delta, Tampolo bayan da aka ganshi yana wulakanta takardar Naira idan dai ba Talakawa kadai ake kamawa ba

Ana kiran EFCC ta kama Tubabben tsageran Niger Delta, Tampolo bayan da aka ganshi yana wulakanta takardar Naira idan dai ba Talakawa kadai ake kamawa ba

Duk Labarai
Jama'a na ta kira a kama Tubabben tsageran Niger Delta, Tampolo bayan ganinsa yana wulakanta takardar Naira. Da yawa sun kira EFCC ta kama Tampolo ta hukuntashi indai ba talakawa kadai ake hukuntawa ba idan sun wulakanta takardar Nairar. A baya dai EFCC ta kama mutane irin su Murja Kunya, Bobrisky da sauransu inda ake zarginsu da wulakanta Naira.
Jami’ar MAAUN ta rufe gidajen kwanan ɗalibai mata bisa zargin aikata rashin tarbiyya

Jami’ar MAAUN ta rufe gidajen kwanan ɗalibai mata bisa zargin aikata rashin tarbiyya

Duk Labarai
Hukumar gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha American University of Nigeria (MAAUN) ta ba da umarnin gaggawa na rufewa tare da janye amincewa da gidajen kwanan dalibai mata na Al-Ansar Indabo da ke Hotoro da titin UDB a birnin Kano. Wata sanarwa daga Mataimakin Shugaban Jami’ar mai kula da Rayuwar Dalibai, Dr. Hamza Garba, a ranar Lahadi, ya bayyana cewa wannan matakin rufe gidajen kwanan wani bangare ne na kokarin da jami’ar ke yi domin tabbatar da kwanan dalibai cikin aminci, tsaro da tsafta, da kuma ci gaba da nuna matsayinta na kin yarda da duk wata dabi’a ta lalata daga kowanne ɗalibi. “Na samu umarni daga hukumar gudanarwa na rubuta wannan sako don sanar da iyaye da dalibanmu masu daraja cewa jami’a ta janye amincewarta da GIDAJEN KWANAN DALIBAI MATA NA AL-ANSAR INDABO da ke titin ...