Sunday, February 15
Shadow

Author: Bashir Ahmed

‘Yan majalisar jihar Rivers 2 sun ce sun janye daga yunkurin tsige Gwamna Fubar

‘Yan majalisar jihar Rivers 2 sun ce sun janye daga yunkurin tsige Gwamna Fubar

Duk Labarai
'Yan majalisar jihar Rivers 2 sun bayyana janyewa daga yunkurin tsige gwamnan jihar, Simi Fubara. 'Yan majalisar sun ce sun dauki wannan matakine biyo bayan kiraye-kirayen dattawa a ciki da wajen jihar ta Rivers su canja matsayarsu. Sun ce duk da gwamnan yayi laifi na karya dokar kundin tsarin mulki amma suna kira ga abokan aikinsu da su duba au sassauta a janye wannan matsaya. https://twitter.com/i/status/2010740601885741243
Dangote ya wadatar da Najeriya da man fetur, Mun daina shigo da man fetur daga kasashen waje>>Inji ‘Yan kasuwar man fetur

Dangote ya wadatar da Najeriya da man fetur, Mun daina shigo da man fetur daga kasashen waje>>Inji ‘Yan kasuwar man fetur

Duk Labarai
A karshe dai bayan dambarwar da akai ta yi tsakanin 'yan kasuwar man fetur da Dangote, 'yan kasuwar a yanzu sun ce sun yadda Dangote ya wadatar da Najeriya da man fetur din. Sun sha Alwashin daina shigo da man daga kasashen waje. Hakan na nufin Dangote zai zama me wuka da nama akan harkar man fetur a Najeriya.
Bayan da Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya baiwa Adam A. Zango mota, Shima Musa Mai Sana’a yace yana mika kokon bararsa wajan Kashim

Bayan da Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya baiwa Adam A. Zango mota, Shima Musa Mai Sana’a yace yana mika kokon bararsa wajan Kashim

Duk Labarai
Tauraron fina-finan Hausa, Musa Mai Sana'a ya bayyana cewa yana mika kokensa ga mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima akan cewa ya yiwa APC wahala amma har yanzu ba'a bashi komai ba. Ya bayyana cewa, dashi aka yi yakin neman zabe da komai amma ko sannu babu wanda yace masa. Dan haka yace yasan mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima mutum me me tausai shiyasa yake mika kokon bararsa a wajansa. https://www.tiktok.com/@maisanaakanotv/video/7592337982741368120?_t=ZS-930mxOR4nb6&_r=1 Ya bayyana hakane bayan da Mataimakin shugaban kasar ya baiwa abokin aikinsa, Adam A. Zango kyautar mota ta Naira Miliyan 80.
Kalli Bidiyon: Abin Kunyar da ‘yan Kungiyar Barcelona suka yi bayan sun lashe kofi da ake ta magana akai

Kalli Bidiyon: Abin Kunyar da ‘yan Kungiyar Barcelona suka yi bayan sun lashe kofi da ake ta magana akai

Duk Labarai
Bayan nasarar da Barcelona ta samu Akan Real Madrid inda aka ga taci Real Madrid 3-2 a daren jiya. A yayin da suke Murna, An ga Lamine Yamal yana Live a Instagram. Saidai an hango golan Barcelona, Wojciech Szczęsny yana zukar Tàbà. Nan da nan, Lamine Yamal ya dakatar da live din da yake yi. Lamarin ya jawo cece-kuce sosai. https://twitter.com/i/status/2010641777561362930