Ji yanda Karamin yaro dan shekaru 18 ya dirkawa ‘yan mata 10 ciki a cikin watanni 5, An kaiwa Kwamishiniyar mata ta jiharsa Korafin yaron tace lamarin yafi karfinta
Wani matashi dan shekaru 18 ya dirkawa mata 10 ciki a cikin watanni 5.
Yaron an kaishi wajan wani dan kasuwane dan ya koya masa kasuwanci daga kauyensu a jihar Anambra, saidai watanni 3 da kaishi wajan me gidan nasa ya dirkawa diyar me gidan ciki sannan ya dirkawa dayar yarinyar shagon me gidan ciki itama.
Dalilin hakane me gidan ya tattara mai kayansa ya koreshi ya mayar dashi kauye.
Saidai watanni biyu bayan komawarsa kauyen, a camma ya dirkawa 'yan mata 8 ciki.
Mahaifiyarsa ce da kanta ta kaiwa kwamishiniyar mata da walwala ta jihar, Ify Obinabo korafi inda tace dan nata ya zamar mata annoba da ta ganshi da mace sai ta ji gabanta na faduwa.
Kwamishiniyar matar tace ta sa yaron a gaba inda ta tambayeshi ko akwai wani magani da yake amfani dashi ne wajan yaudarar mata k...








