Ƴansanda a Kano sun kama mutane 9 bayan rykycyn
Ƴansanda a Kano sun kama mutane 9 bayan rikicin da ya faru kan zargin kisan kai a Garko.
Rundunar ’Yansanda ta Jihar Kano ta ce ta kama mutane tara da ake zargi da hannu a tashin hankali da ya faru a karamar hukumar Garko bayan wani lamari na kisan kai.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, lamarin ya faru ne a ranar 4 ga Satumba, 2025, lokacin da jami’an 'yansandan, shiyyar Wudil su ka kama wasu mutane uku da ake zargi da kisan kai, sannan aka kai su caji-ofis na Garko domin bincike.
Sai dai a ranar 5 ga Satumba, jama’a dauke da sanduna da duwatsu suka farmaki ofishin, suna zanga-zangar mutuwar wanda aka kashe, tare da kokarin kashe wadanda ake tsare da su.
Harin ya jawo konewar motar sintirin ’yansanda, lalata motoci uku na...








