Rahotanni sun bayyana cewa, majalisar tarayya zata yi zama na musamman dan karrama tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari.
Majalisar zata yi wannan zaman ne ranar Laraba.
Manoman shinkafa da masara a Najeriya na fargabar za su iya tafka asara sakamakon tsadar taki da sauran kayan aikin noma.
Wasu manoman kuwa sun hakura da noman shinkafar kacokan sun koma noman wani abu daban, saboda a cewarsu tsadar taki ba za ta bari su samu riba ba.
Wannan dai na zuwa ne duk da iƙirarin da gwamnatin tarayya ta yi na cewa ta rage farashin takin zamani ga manoma a sassan ƙasar don tallafawa harkokin noma.
Wani manomi a jihar Jigawa, Alh. Muhammad Idris ya shaida wa BBC cewa ya kashe kuɗi har naira miliyan ɗaya da dubu ɗari takwas wajen siyan taki da zai yi noma da shi da kuma kuɗin banruwa a kowacce kadada.
"Duk da kuɗin da na kashe wajen noma, gaskiyar magana itace babu ribar da zan samu idan aka yi la'akari da tsadar taki da ya tashi da kuma shi kansa shinkaf...
Rahotanni sun bayyana cewa, Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya Biwa mahaifinsa, Joshua Nlemanya Wike dan shekaru 90 fili a Abuja.
Rahoton yace Wike ya baiwa mahaifin nasa filinne a Guzape II wanda darajarsa ta kai ta Naira Miliyan 400.
Hakanan bayan mahaifinsa akwai 'yan uwansa maza da mata da abokai da ya baiwa filayen a Abuja.
Hakan na zuwa ne kwanaki bayan da aka zargi Wike da baiwa 'ya'yansa filaye a Abujan, zargin da ya karyata yace Atiku ne ke son bata masa suna.
Rahoton yace mutane 38 ne Wike ya baiwa ma'aikatansa yace a basu filaye, ma'aikatan da yawa sun yi mamakin wannan abu, kamar yanda peoplesgazette ta ruwaito.
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{"square_fit":1},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":true,"containsFTESticker":false}
Kasar Saudiyya ta bude ban daki ga direbobi masu kai sakonni wanda ke da AC watau Na'urar sanyaya daki.
An bude ban dakinne a Al Khobar kuma shine irinsa na farko.
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false}
Bayan da ta kutsa kai da karfin tsiya cikin farfajiyar majalisar Dattijai An kuma hana Sanata Natasha Akpoti shiga ainahin cikin zauren majalisar inda su Akpabio ke zaune.
Sai dai data ga haka, ita da magoya bayanta sun ja da baya sun koma inda suka fito.
https://twitter.com/TheNationNews/status/1947635909077127430?t=xG8kF_D5giCzLcBcsoKGGQ&s=19
https://twitter.com/TheNationNews/status/1947635768119136434?t=ULzpUVqnpg7HZ0c8nEIhkg&s=19
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai zaba a shekarar 2027.
Gwamnan ya bayyana hakane bayan wani zama da aka yi tsakanin sarakunan gargajiya da manyan ma'aikatan gwamnati na jihar da sauran masu ruwa da tsaki.
Gwamnan yace dukansu a jihar sun yanke shawarar goyon bayan shugaban kasa Bola Tinubu a zaben shekarar 2027 me zuwa a matsayin dansu.
Gwamnan ya bayyana hakane a shafinsa na X.
Dalilan da su ka sanya za mu yi Tinubu a 2027- Sarkin Daura
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false}
Sarkin Daura a Jihar Katsina, Umar Faruq-Umar, ya ce zai mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya ya yi tazarce a 2027 saboda girmamawar da shugaban ya yi wa masarautar Daura da kuma Jihar Katsina ta hanyar yi wa wanda ya gada, tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, jana'izar ban-girma.
Sarkin ya bayyana goyon bayansa ne a fadarsa da ke Daura a ranar Asabar yayin da ya tarbi tawagar matan gwamnonin Najeriya, ƙarƙashin jagorancin...
Bayan da aka hanata shiga, Sanata Natasha Akpoti ta kutsa da karfin tsiya cikin majalisar Dattijai.
Da farko dai Sanata Natasha Akpoti ta je majalisar ne akan motocin ta inda aka tare motocin aka hanasu wucewa.
Tana tarene da magoya bayanta ciki hadda A'isha Yesufu.
Sanata Natasha Akpoti daga baya ta sauka inda ta taka a kafa zuwa cikin majalisar.
Magoya bayan Sanata Natasha Akpoti sun rika ture jami'an tsaron inda suka samarwa Sanata Natasha Akpoti hanya ta taka zuwa cikin majalisar a kafa.
Magoya bayan sun take mata baya suna rera wakokin yabo.
Majalisar dai ta dakatar da sanata Natasha Akpoti na tsawon watanni 6.
https://twitter.com/thecableng/status/1947623189825155358?t=KE11cWiyw5H89tH0iy2R0w&s=19
Rahotanni daga majalisar Dattijai dake Abuja na cewa, jami'an tsaro sun hana sanata Natasha Akpoti shiga cikin majalisar.
Dama dai tuni aka jibge jami'an tsaro a wajen majalisar Dattijai dan hana sanata Natasha Akpoti shiga majalisar.
Hakan na zuwane bayan da Sanata Natasha Akpoti ta sanar da cewa zata koma majalisar a yau, Talata biyo bayan hukuncin kotu da ya bata damar yin hakan.
https://twitter.com/thecableng/status/1947619399499649509?t=1-L6pcmeKvgg6nLGDQkUYQ&s=19
Kamfanonin samar da wutar lantarki a Najeriya sun ce suna iya dakatar da ayyukansu na samar da wuta saboda tarin bashin da ya haura naira tiriliyan 5.2 da har yanzu gwamnati ba ta biya su ba, wanda ke barazana ga cigaban aikinsu na samar da lantarki a ƙasar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Shugabar ƙungiyar kamfanonin samar da lantarkin, Dr. Joy Ogaji, ta bayyana cewa kamfanonin sun jima suna nuna kishin kasa ta hanyar ci gaba da samar da wuta duk da rashin biyan su kuɗaɗensu, amma yanzu sun gaji.
Ta ce akwai sabon bashi da ya kai naira tiriliyan 1.2 daga wutar da aka samar a farkon rabin shekarar 2025, wanda ya ƙaru kan bashin da suke bin gwamnati zuwa naira tiriliyan 5.2.
Wannan ya haɗa da naira tiriliyan 2 daga shekarar 2024 da kuma bashin da aka gada tun daga 2015 da ya ...