Saturday, December 20
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Bidiyo yanda fadawan sarkin Katsina suka fasa kofar taro suka shigar da sarkin bayan da aka kulle kofar dakin Taron da aka yiwa Tinubu Maraba a jihar

Kalli Bidiyo yanda fadawan sarkin Katsina suka fasa kofar taro suka shigar da sarkin bayan da aka kulle kofar dakin Taron da aka yiwa Tinubu Maraba a jihar

Duk Labarai
Wasu rahotanni sun ce bayan da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya shiga dakin taron da aka mai tanadi dan yi masa maraba a jihar Katsina, An kulle dakin taron. Saidai daga baya Me martaba sarkin Katsina ya isa wajen inda fadawa suka iske kofar a kulle. Saidai sun fasa gilashij kofar inda suka shigar da Sarki wajan Taron. Kalli Bidiyon: https://twitter.com/northern_blog/status/1919398029473284233?t=eIgHj3fbuZ8VxrkeyPlTSw&s=19 Da yawa dai sun jinjinawa Fadawan.
Kasar Israyla ta amince da kwace gaba dayan yankin Gaza ya koma karkashin kulawa da ikonta, dan haka ta kirawo tsaffin sojojinta dan yin wannan aiki

Kasar Israyla ta amince da kwace gaba dayan yankin Gaza ya koma karkashin kulawa da ikonta, dan haka ta kirawo tsaffin sojojinta dan yin wannan aiki

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa kasar Israela ta amince da matakin kwace gaba dayan yankin Gaza ya koma karkashin mulkinta. Dan hakane ta kirawo duka sojojinta da suka yi ritaya dana karta kwana dan gudanar da wannan gagarumin aikin. Israela dai bata bayyana zuwa yaushene zata rike zirin na gaza ba watau saidai abinda Allah yayi. Kasar ta Israela tace a wannan sabon mataki zata bari a shiga da kayan agaji cikin Gaza amma zata saka ido ta tabbatar basu fada hannun kungiyar Hamas ba.
Kadan ya hana in daina karanta Jarida da kallon labarai, Saboda Wahalar da nake ganin ‘yan Najeriya a ciki>>Shugaba Tinubu

Kadan ya hana in daina karanta Jarida da kallon labarai, Saboda Wahalar da nake ganin ‘yan Najeriya a ciki>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, saura kiris ya daina jin labarai da karanta jaridu saboda yanda yake ganin 'yan Najeriya a cikin wahala. Ya bayyana hakane a ziyarar da ya kai jihar Katsina. Yace amma duk da haka ya dage ya tsaya tsayin daka dan tabbatar da ganin ya dora Najeriya a turbar gaskiya. Shugaba Tinubu yace kuma zuwa yanzu an fara ganin sakamakon matakan da ya dauka. Inda yace lamura sun fara dawowa daidai
WhatsApp zai daina aiki a wadannan wayoyin, Karanta kaga ko taka na ciki

WhatsApp zai daina aiki a wadannan wayoyin, Karanta kaga ko taka na ciki

Duk Labarai
Rahotanni sun ce manhajar WhatsApp da ake amfani da ita wajan Chatin da kasuwanci da sada zumunta zata daina aiki a cikin wayoyi kirar iPhone guda 3. Masu irin wadannan wayoyi saidai ko su canja waya ko kuma su yi upgrading Operation System dinsu. Kamfanin Meta wanda shi ke da WhatsApp yace daga yanzu wayoyi masu manhajar iOS 15.1 zuwa sama ne kawai zasu iya amfani da WhatsApp. Hakan na nufin wayoyin iPhone 5s, iPhone 6, da iPhone 6 Plus duk ba zasu iya yin amfani da WhatsApp ba. Kakakin WhatsApp ya shaida cewa a duk shekara sukan duba su ga wace waya ce ta fi tsufa wadda kuma babu mutane da yawa dake amfani da ita sai su dakatar da WhatsApp akanta. Sunce wadannan wayoyi basu da manhajojin tsaro da ya kamata. Wadannan wayoyi dai an yisu ne tsawon shekaru sama da 10 kuma ...
Lauyoyin Jihar Zamfara Sun Goyi Bayan Gayyatar Gwamna Dauda A Gaban Majalisa Kan Ŕikicin Majalisar Ďokoki

Lauyoyin Jihar Zamfara Sun Goyi Bayan Gayyatar Gwamna Dauda A Gaban Majalisa Kan Ŕikicin Majalisar Ďokoki

Duk Labarai
Lauyoyin Jihar Zamfara Sun Goyi Bayan Gayyatar Gwamna Dauda A Gaban Majalisa Kan Ŕikicin Majalisar Ďokoki. Kungiyar lauyoyin Jihar Zamfara ta bayyana goyon bayanta ga matakin da Majalisar Wakilai ta Nijeriya ta dauka na gayyatar Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, da shugabannin majalisar dokokin jihar domin su bayyana kan rikicin da ke kara tsananta a majalisar dokokin jihar da kuma tabarbarewar tsaro a fadin jihar da ke arewa maso yammacin Nijeriya. Wannan kungiya, wadda ke da matsayi a fannin kare doka da tsarin mulki, ta bayyana kiran a matsayin matakin da kundin tsarin mulki ya amince da shi, bisa tanade-tanaden sashe na 88 da 89 na Kundin Tsarin Mulki na 1999, wanda ya ba Majalisar Tarayya damar gudanar da bincike kan batutuwan da suka shafi jama’a da kuma kiran jami’ai mas...
Kalli Bidiyon yanda aka jefi shugaban kasar Kenya da Takalmi

Kalli Bidiyon yanda aka jefi shugaban kasar Kenya da Takalmi

Duk Labarai
Gwamnatin Kenya ta bayyana jifa da takalmi da aka yi wa shugaban ƙasar, William Ruto a wani gangamin siyasa a ranar Lahadi, a matsayin “abun kunya”. Bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta ya nuna yadda takalmin ya bugi hannun shugaban ƙasar na hagu, a yayin da ya ke magana. https://twitter.com/citizentvkenya/status/1919295562660098502?t=JznCzRShAKV-GnuJ17gZpg&s=19 Mai magana da yawun gwamnatin ƙasar, Isaac Mwaura, ya yi Alla-wadai da lamarin tare da kiran a kama waɗanda suka aikata hakan. A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ya ce “me zai faru idan dukkanmu muka fara jifar juna da takalma? Wane tarbiyya muke koya wa ƴaƴan mu?” Ya kuma buƙaci a girmama muƙamin shugaban ƙasa. Kafofin watsa labarai a Kenya na bayar da rahoton cewa an kama mutum uku dangane da lam...