Kada Ki Kuskura Ki Sake Shigowa Majalisa, Gargaɗin ‘Yan Majalisar Dattaawa Ga Sanata Natasha, Bayan da tace ranar Talatar nan zata koma majalisar
Kada Ki Kuskura Ki Sake Shigowa Majalisa, Gargaɗin 'Yan Majalisar Dattaawa Ga Sanata Natasha
Daga Muhammad Kwairi Waziri
A wata sabuwar sabani da ke kara dagula lamura a Majalisar Dattawa, wani sashe na majalisar ya fitar da gargadi mai zafi ga Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, inda suka ce:
“Kar ki kuskura mu ga ƙafarki a majalisar dattijai domin har yanzu ki na ƙarƙashin dakatarwarmu.”
Wannan gargadi na zuwa ne kwanaki bayan Sanata Natasha ta sanar da shirinta na komawa kujerarta a majalisar ranar Talata mai zuwa. Majalisar ta nuna cewa akwai hukuncin dakatarwa da har yanzu ba a janye ba, kuma duk wani yunkuri nata na komawa za a ɗauka a matsayin sabawa doka da ka’ida.
Sai dai har yanzu ba a fitar da cikakken bayani daga ofishin shugaban majalisar kan ainihin dalilin dakatar...








