A karshe dai shugaba Tinubu ya sakawa sabbin dokokin Haraji hannu, Ji Bayani dalla-dalla abinda suka kunsa
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanya hannu kan sababbin dokokin haraji huɗu a wani mataki na sauya fasalin tsarin karɓa da tattara haraji na ƙasar.
Gwamnatin ta ce sabbin dokokin za su sauƙaƙa tsarin, da rage wahalhalun haraji kan ɗaiɗaikun mutane da kamfanoni, da kuma taimakawa wajen inganta karɓar haraji.
"Sauye-sauyen za su taimaki masu ƙaramin ƙarfi tare da tallafa wa ma'aikata ta hanyar ƙara yawan abin da suke samu,'' kamar yadda Shugaba Tinubu ya bayyana a watan da ya gabata lokacin bikin cika shekara biyu a kan mulki.
Ya ƙara da cewa: "Sauye-sauyen sun cire muhimmman abubuwa kamar abinci da ilimi da kula da lafiya daga tsarin biyan harajin VAT. Haka nan, sabon tsarin ya keɓe karɓar rance da sufuri da makamashin da ba ya gurɓata muhalli, duka wadannan ba za su biya harajin...








