Tuesday, December 23
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Da yawan ‘yan majalisa basa iya biyan Kudin makarantar ‘ya’yansu>>Inji Sanata Na’Allah

Da yawan ‘yan majalisa basa iya biyan Kudin makarantar ‘ya’yansu>>Inji Sanata Na’Allah

Duk Labarai
Tsohon sanata daga jihar Kebbi Sanata Bala Ibn Na'Allah ya bayyana cewa da yawan 'yan majalisa bayan sun bar majalisar basa iya biyan kudin makarantar 'ya'yansu. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan jaridar Trust TV. Yace yawanci 'yan majalisa idan suka yi ritaya bayan shekara daya zaka ga basa iya biyan kudin makarantar 'ya'yansu. Yace wannan yana faruwane musamman ga wadanda dama can basu da wata sana'a sai siyasar. Yace yawanci mutane suna tsammanin wasu manyan kudi ne ake samu a majalisar Amma a gaskiyar zahiri ba haka bane.
Kalli Bidiyo: Cikin sheshshekar kuka wannan matar tana rokon Dan Allah wani ya fito ya aureta, tace Wallahi ta tuba ba zata kara yin rawar badala a intanet ba, tace kuma zata baiwa duk wanda ya yadda ya aureta naira Miliyan 20

Wannan matar dake da shekaru sama da 40 ta fito tana kuka tana cewa ta tuba da rawar badala da take yi a kafafen sada zumunta. Matar tace yanzu mijin aure take nema. Tasha Alwashin bayar da Naira Miliyan 20 ga duk wanda zai aureta: Kalli Bidiyon a kasa: https://twitter.com/Teeniiola/status/1916953355559047646?t=yHCWKxtVQd6mqw5KWpM6uQ&s=19 Ko kana ciki?
Wayyo Allah Na, Ina Ta Dakon Soyayyar Rarara Ashe Ba Da Ni Za A Yi Ba, Kuma Abun Da Ya Fi Damuna Shine Bai Ma San Ina Yi Ba, Kuma Allah Ya San Ina Kaunarsa, Inji Hajiya Suraiyat A. Nasir Daga Adamawa

{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wayyo Allah Na, Ina Ta Dakon Soyayyar Rarara Ashe Ba Da Ni Za A Yi Ba, Kuma Abun Da Ya Fi Damuna Shine Bai Ma San Ina Yi Ba, Kuma Allah Ya San Ina Kaunarsa, Inji Hajiya Suraiyat A. Nasir Daga Adamawa Masu karatu wace shawara za ku ba ta?
‘Yan Bìndìgà sun kàshè babban Limamin juma’a na Masallacin juma’a na farko a garin Maru jihar Zamfara da ‘ya’yansa 2

‘Yan Bìndìgà sun kàshè babban Limamin juma’a na Masallacin juma’a na farko a garin Maru jihar Zamfara da ‘ya’yansa 2

Duk Labarai
Rahotanni daga karamar Hukumar Maru dake jihar Zamfara na cewa 'yan Bindiga sun kashe babban limamamin masallacin juma'a na farko a garin watau Malam Salisu Suleiman Liman tare da 'ya'yansa 2. Tun ranar February 13, 2025 ne aka sace liammin tare da wasu mutane. Me kawo rahotanni akan harkar tsaro, Bakatsinene ya tabbatar da hakan.
Da Duminsa:An kori ma’aikata yaran Mele Kolo Kyari daga NNPCL

Da Duminsa:An kori ma’aikata yaran Mele Kolo Kyari daga NNPCL

Duk Labarai
A wani shiri na sauya fasalin gudanar da kamfanin mai na kasa, NNPCL An kori manyan ma'aikatan kamfanin wanda yawanci yaran Tsohon shugaban kamfanin ne watau Mele Kolo Kyari. Wadanda aka kora sun hada da Bala Wunti, Ibrahim Onoja, da Lawal Sade wadanda aka yi amanannar na hannun damar Mele Kolo Kyari ne. Hakanan Rahoton yace an kuma kori ma'aikata 200 daga kamfanin na NNPCL.
Ku Daina Gudun Talauci, Wani lokacin Talauci ma Wata Rahama ce daga Allah>>Kakakin Majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya baiwa ‘yan Najeriya shawara

Ku Daina Gudun Talauci, Wani lokacin Talauci ma Wata Rahama ce daga Allah>>Kakakin Majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya baiwa ‘yan Najeriya shawara

Duk Labarai
Kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa Talauci na iya zama wata rahama daga Allah. Ya bayyana hakanne a wata hira da aka yi dashi daga Vatican, fadar Fafaroma inda suka je jana'izar Fafaroma Francis. Yace idan mutum yana dashi ya samma dan uwansa, har ya bayar da misali da fafaroman inda yace ya mutu ya bar dala $100 kawai.
Kalli Bidiyo yanda Matasa ‘yan Izala suka rude suna ta tambayar ta yaya ake shiga Darika bayan da suka ga wata Budurwa na juya mazaunanta a wajan da Hallara ta yi girgiza

Kalli Bidiyo yanda Matasa ‘yan Izala suka rude suna ta tambayar ta yaya ake shiga Darika bayan da suka ga wata Budurwa na juya mazaunanta a wajan da Hallara ta yi girgiza

Duk Labarai
Bidiyon wata budurwa na juya mazaunanta a wajan wani taron Mandiri ya dauki hankula sosai. Matasa, musamman na Izala na ta tambayar ta yaya ake shiga Darika bayan kallon wannan Bidiyon. https://twitter.com/bapphah/status/1916967455844433943?t=bTFFrYl_0k11wdPMYFyftA&s=19 Mutane sun bayyana ra'ayoyinsu daban-daban kan lamarin.
Na yi nadamar yin takara tare da Atiku saboda mutanen mu basu son dan Arewa>>Inji Ifeanyi Okowa wanda yawa Atiku Abubakar mataimaki a takarar shugaban kasa ta 2023 bayan ya koma APC daga PDP

Tsohon Gwamnan jihar Delta kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa a shekarar 2023 a karkashin jam'iyyar PDP, Ifeanyi Okowa ya bayyana cewa yayi dana sanin yin takarar shugaban kasa tare da Atiku. Okowa ya bayyana hakane bayan da ya canja jam'iyya daga PDP zuwa APC. Yace a wancan lokacin mutanensa sun nuna basa son yayi wannan takara a matsayin mataimakin Atiku amma duk da haka ya karba. Yace ko a lokacin da suke yakin neman zabe ya lura cewa mutanen su basa son dan Arewa ya sake zama shugaban kasa amma ya ki kulasu. Yace amma yanzu yana dana sani kan kin bin abinda mutanensa ke so.