Zamu yi dukkan me yiyuwa koma menene indai bai sabawa doka ba mu kayar da Tinubu zabe>>Inji Peter Obi
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false}
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour party a zaben shekarar 2023, Peter Obi ya bayyana cewa, zasu yi dukkan mai yiyuwa dan ganin sun kayar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zabe a shekarar 2027.
Obi ya bayyana hakane a yayin hirar da aka yi dashi a Channels TV ranar Lahadi.
Obi yace idan ya samu zama shugaban kasa zai kawo bin doka da oda a Najeriya.
Yace kuma zai nada mutane da suka cancanta a mukamai daban-daban.
Yace kuma ba zai zama Ministan Man fetur ba.
...








