Kalli Bidiyo: Bayan ya bayar da hakuri kan bidiyonsa da aka gani yana rabawa ‘yansanda kudi, An kuma kara ganin dan Chinar nan yana watsawa ma’aikatansa kudi a wajan hakar ma’adanai
Dan kasar Chinar nan da kwanakin baya aka ganshi a wani Bidiyo da ya yadu sosai yana rabawa 'yansandan Najeriya kudi wanda har daga baya ya fito ya bada hakiri, ya sake aikata laifin.
A wannan karin, ganinsa aka yi yana watsawa ma'aikatansa kudi a kasa suna rububi a wajan hakar ma'adanai.
https://twitter.com/thecableng/status/1916889365088784551?t=4ZnGGNlAc-i4iQe5INZGVw&s=19
Wannan dai cin zarafin Naira ne kamar yanda hukumar EFCC ta Haramta yin hakan.
Abin jira a gani shine wane hukunci ne hukumomi zasu dauka a kansa.








