Friday, December 19
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Fadar shugaban kasa zata saka Solar saboda tsadar kudin Wutar Lantarki da rashin tabbas na wutar

Fadar shugaban kasa zata saka Solar saboda tsadar kudin Wutar Lantarki da rashin tabbas na wutar

Duk Labarai
Fadar shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu dake babban birnin tarayya Abuja ta ware Naira Biliyan 10 a cikin kasafin kudinta na shekarar 2025 dan hada sola. Hakan na zuwane yayin da kudin wutar Lantarki yake tashi sannan wutar ba samuwa take ba yanda ake bukata. Rahoton ya nuna za'a saka Solar a fadar shugaban kasar ta yanda fadar zata daina dogaro da wutar Lantarkin Najeriya ta koma amfani da hasken rana. 'Yan Najeriya da yawa da suka hada da kamfanoni tuni suka daina amfani da wutar Lantarkin inda suka koma amfani da hasken rana wajan samawa kansu wutar.
Ina alfahari cewa matan mahaifi na 39 kuma ƴaƴansa 147 ne – Ƴar Nijeriya mazauniyar Amurka

Ina alfahari cewa matan mahaifi na 39 kuma ƴaƴansa 147 ne – Ƴar Nijeriya mazauniyar Amurka

Duk Labarai
Wata ƴar Najeriya da ke zaune a Amurka, Gimbiya Adenubi Olagbegi-Apampa, wacce mahaifinta ke da mata 39 da ‘ya’ya 147, ta ce tana alfahari da fitowa daga irin wannan babban gida. Ta bayyana hakan ne a lokacin da take zantawa da manema labarai a wajen bikin bada kyautar wani gini mai suna Gimbiya Nubi Plaza Seliat na miliyoyin naira da ke Estate Lagelu, Ibadan. A cewarta, idan har ta samu dama ta sake zuwa, za ta ji dadin zama a wannan gidan yawan. Sabanin cewa irin wannan gidan yawan ba a raba shi da rikici, ta bayyana cewa duk ƴaƴan gidan nasu su na zaune lafiya da juna. Ta kuma bukaci ƴan Najeriya mazauna kasashen waje da kada su yi amfani da matsalar rashin tsaro su kaurace wa kasarsu. Ta lura da cewa rashin tsaro da cin hanci da rashawa da ya zama ruwan dare a Najeriya b...
Da Duminsa: Zanga-zanga ta barke a Jos, babban birnin jihar Filato saboda yawaitar Kàshè-Kàshè

Da Duminsa: Zanga-zanga ta barke a Jos, babban birnin jihar Filato saboda yawaitar Kàshè-Kàshè

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Filato na cewa, zanga-zanga ta barke a babban birnin jihar watau, Jos saboda yawaitar kashe-kashen 'yan Asalin Jihar da ake zargin 'yan Bindiga Fulani da aikatawa. Babban Limamin kirista, Rev. Polycarp Lubo ne ya jagoranci zanga-zangar wadda aka fara ta daga Titin Fawvwei Junction wanda hakan ya kawo tsaikon ababen hawa. Daya daga cikin masu zanga-zangar me suna Gyang Dalyop ya shaidawa kafar Punchng cewa, sun fito ne saboda basa jin dadin abinda ke faruwa na kashe-kashen a garuruwansu. Itama wata me suna Hannatu Philip tace suna kira ga hukumomi su dauki matakan kawo karshen lamarin kamin ya kazance. A wani lamari me alaka da wannan, Hutudole ya kawo muku cewa, a yau ne ake sa ran mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima zai kai ziyara jihar.
Zan Iya Siyar Da Gidana Domin Ganin Tinibu Ya Yi Nasarar Tazarce A Zaben 2027, Ra’ayin Muntasir Sulaiman

Zan Iya Siyar Da Gidana Domin Ganin Tinibu Ya Yi Nasarar Tazarce A Zaben 2027, Ra’ayin Muntasir Sulaiman

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Zan Iya Siyar Da Gidana Domin Ganin Tinibu Ya Yi Nasarar Tazarce A Zaben 2027, Ra'ayin Muntasir Sulaiman
Ana yada rade-radin cewa kasar Amurka ce ta kàshè Fafaroma, Fafaroma dai ya mutu ne awanni kadan bayan ganawa da mataimakin shugaban kasar Amurka, JD. Vance

Ana yada rade-radin cewa kasar Amurka ce ta kàshè Fafaroma, Fafaroma dai ya mutu ne awanni kadan bayan ganawa da mataimakin shugaban kasar Amurka, JD. Vance

Duk Labarai
Rahotanni na ta yawo musamman a kafafen sada zumunta inda ake zargin cewa, Kasar Amurka na da hannu a mutuwar fafaroma. Hakan ya farune bayan da Fafaroma ya mutu, awanni kadan bayan ganawar da yayi da mataimakin shugaban kasar Amurka, J.D. Vance. Saidai me yasa wasu ke zargin Amurkar da hannu a kashe Fafaroma? Fafaroma dai na daya daga cikin mutanen dake adawa da kisan Falasdinawa musamman fararen hula da suka hada da kananan yara da mata da Kasar Israela ke yi. Hakanan Fafaroma na kiran a kare hakkin 'yan Luwadi da Madigo, duk da yake da yawa daga cikin fastoci basa tare dashi akan hakan. Hakanan bayan da J.D. Vance yaje fadar Fafaroman, Fafaroman yaki ganawa dashi a hukumance. Saida aka kammala taro a hukumance sannan J.D. Vance ya je ya gana da Fafaroma. Saidai a sa...
‘Yan majalisar Tarayya sun karawa kansu hutun sati daya

‘Yan majalisar Tarayya sun karawa kansu hutun sati daya

Duk Labarai
'Yan majalisar tarayya da suka hada da Majalisar Dattijai data wakilai sun daga ranar da zasu dawo aiki zuwa 6 ga watan Mayu. 'Yan majalisar a baya sun shirya dawowa bakin aiki ranar 29 ga watan Afrilu saidai yanzu sun karawa kansu sati daya. Wakilin majalisar, Kamoru Ogunlana ne ya bayyana hakan ga sauran 'yan majalisar inda yace an sanar da hakanne saboda baiwa 'yan majalisar damar yin bikin ranar ma'aikata.
Shin da gaske akwai Baraka tsakanin Buhari da Tinubu? Ji bayani dalla-dalla

Shin da gaske akwai Baraka tsakanin Buhari da Tinubu? Ji bayani dalla-dalla

Duk Labarai
Gwamnan jihar Nasarawa da ke Najeriya, Abdullahi Sule ya ce wasu na son yin amfani da rashin "zuwan tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari Abuja" domin nuna cewa akwai ɓaraka tsakaninsa da shugaban ƙasar mai ci, Bola Tinubu. Gwamna Sule ya bayyana haka ne yayin da alamu suka bayyana cewa an samu ɓaraka tsakanin makusantan tsohon shugaban ƙasar, waɗanda suka kasance a jam'iyyar CPC, wadda Buhari ya jagoranta kafin shiga haɗakar da ta samar da jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar. A baya-bayan nan wani ɓari na ƴaƴan tsohuwar jam'iyyar ta CPC sun bayyana mubaya'arsu ga shugaban Najeriya Bola Tinubu, sai dai kwanaki kaɗan bayan hakan wasu ƴaƴan tsohuwar jam'iyyar kuma waɗanda ke da matuƙar kusanci da Buhari sun nesanta kansu daga mubaya'ar. Haka nan sauya sheƙar tsohon gwamnan jihar Kaduna...
Da Duminsa: Fafaroma Francis ya mutu

Da Duminsa: Fafaroma Francis ya mutu

Duk Labarai
Fadar Vatican ta sanar da mutuwar shugaban majami'ar katolika na duniya, Fafaroma Francis yana da shekaru 88 a duniya. A shekarar 2023 ne cocin ta zaɓi Fafaroman, wanda asalin sunansa shi ne Cardinal Jorge Mario Bergoglio a matsayin wanda zai jagorance ta, bayan saukar Fafaroma Benedict XVI daga kan muƙamin.
Yayin da aka yi sati 3 ba’a ga shugaba Tinubu ba, ‘yan Najeriya sun shiga damuwa inda suka tambayar ina shugaban kasar ya shiga ne lafiya kuwa?

Yayin da aka yi sati 3 ba’a ga shugaba Tinubu ba, ‘yan Najeriya sun shiga damuwa inda suka tambayar ina shugaban kasar ya shiga ne lafiya kuwa?

Duk Labarai
Tun bayan da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya tafi kasar Faransa a ranar 2 ga watan Afrilu, fadar shugaban kasar ta fitar da sanarwar cewa zai yi sati biyu ne. Saidai yayin da ake tsammanin zai dawo ranar 16 ga watan Afrilu, shugaban kasar bai dawo ba inda musamman 'yan Adawa suka fara tambayar ba'asi. Fadar shugaban kasar ta sake fitar da sanarwa inda tace shugaban kasar yana nan lafiya kuma yana gudanar da aiki daga can kasar Faransar da yake. Saidai hakan a cewar masana ya sabawa aiki inda bai kamata ace daga kasar Wajene shugaban kasar zai rika gudanar da gwamnati ba. Abubuwan da dama sun faru musamman bangaren matsalar tsaro inda aka yi kashe-kashe amma shugaban kasar bayanan inda daga can kasar Faransa ne ya baiwa jami'an tsaro umarnin cewa su magance matsalar da kakka...