Friday, December 19
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Ku rika Sadaka, Tana jawo Alkhairai da yawa>>Inji Tsohon shugaban kasa, Obasanjo

Ku rika Sadaka, Tana jawo Alkhairai da yawa>>Inji Tsohon shugaban kasa, Obasanjo

Duk Labarai
Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya baiwa 'yan Najeriya shawarar su rika yin sadaka inda yace tana jawo Alkhairai da yawa. Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakane ranar Juma'a a wajan kaddamar da fara gyaran wani masallacin dake Kobiti, Abeokuta, jihar Ogun. An kaddamar da fara shirin gyaran masallacin a Dakin karatu na Obasanjon dake Abeokuta. A jawabin da yayi lokacin bude kaddamar da aikin, Obasanjo yace sada wadda kowane mutum na iyayi ba tare da la'akari da addini ko karfin tattalin arziki ba, tana jawo Alkhairai da yawa.
Wata Sabuwa:Ana rade-radin an hana mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima shiga fadar shugaban kasa har hakan tasa fadar shugaban kasar yin magana

Wata Sabuwa:Ana rade-radin an hana mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima shiga fadar shugaban kasa har hakan tasa fadar shugaban kasar yin magana

Duk Labarai
Wasu rahotanni sun bayyana cewa, an hana mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima shiga fadar shugaban kasar dake Abuja. Saidai a martanin da fadar shugaban kasar ta fitar ta bakin me magana da yawun shugaban kasar, Stanley Nkwocha yace wannan magana karyace da wasu suka kirkira dan cimma wata manufa. Ya kara da cewa babu wani abu me kama da wannan da ya faru a fadar shugaban kasar. Yace hankalin mataimakin shugaban kasar na kan aikin da yake gabansa na gina kasa. Hakanan ya kawo bayanai akan wata karya da aka yada a baya ta fastar yakin neman zaben shugaban kasar da mataimakinsa wanda yace basu da alaka dashi.
Ba Allah ne ya zabi Tinubu ba ya zama shugaban Najeriya, da Karfin Tsiya ya kwace mulki>>Inji Fasto Chukwuemeka Odumeje

Ba Allah ne ya zabi Tinubu ba ya zama shugaban Najeriya, da Karfin Tsiya ya kwace mulki>>Inji Fasto Chukwuemeka Odumeje

Duk Labarai
Babban Fasto Chukwuemeka Odumeje wanda yayi kaurin suna wajan jawo cece-kuce, yace ba Allah ne ya zabi shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya zama shugaban Najeriya ba. Yace shugaba Tinubu da karfin tsiya ya kwaci mulkin. Ya bayyana hakane a wani faifan Bidiyon da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta. https://www.youtube.com/watch?v=zKtaV9Rxm70?si=I8mQqojn9WIMRgoN Ya musanta abinda mafi yawan addinai suka aminta dashi na cewa duk wanda ka ga ya zama shugaba to zabin Allah ne, yace game da Tinubu abin ba haka yake ba.
Da ace Tinubu na da wayau, da ba zai tsaya takarar shugaban kasa ba a 2027 dan kuwa faduwa zai yi>>Inji Datti Ahmad

Da ace Tinubu na da wayau, da ba zai tsaya takarar shugaban kasa ba a 2027 dan kuwa faduwa zai yi>>Inji Datti Ahmad

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam'iyyar Labour party, Datti Ahamad ya bayyana cewa, da dai ace shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na da wayau, da ya hakura da tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2027. Ya bayyan hakane a hirar da aka yi dashi a Arise TV inda yace dukkan alamu sun bayyana cewa, jam'iyyar APC faduwa zata yi. Yace kuma shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba zai cikawa 'yan Najeriya alkawuran da ya dauka ba. Yace Buhari bai cika alkawuran da ya dauk...
Azumi na kara min karfin Sha’awa>>Inji Tauraruwar BBN, Uriel

Azumi na kara min karfin Sha’awa>>Inji Tauraruwar BBN, Uriel

Duk Labarai
Tsohuwar tauraruwar BBN, Uriel Oputa ta bayyana cewa, Azumi na kara mata karfin sha'awa. Ta bayyana hakane a wani rahoto na jaridar Punchng. Ta hayyana cewa ta fara yin Azumi ne wanda take karyawa da misalin karfe 6 na yamma bayan da ta fara samun matsalar rashin narkewar abinci kuma bata samun shiga bayi yanda ya kamata. Tace kuma tasan tana cin abinci me gina jiki, dan hakane sai ta yanke shawarar fara Azumin. Tace data fara azumin ta ji jikinta ya dawo daidai sannan har karfin sha'awarta ya karu sosai.
Wata Sabuwa:Ji yanda na kusa da Buhari ke nuna basu tare da Tinubu

Wata Sabuwa:Ji yanda na kusa da Buhari ke nuna basu tare da Tinubu

Duk Labarai
A wani lamari mai kama da na ba-zata a fagen siyasar Najeriya, sunan tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ne ya sake dawowa yake amo, musamman bayan alamu sun fara nuna akwai ɓaraka a tsakanin makusantansa. Alamu sun fara bayyana ne a lokacin da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar SDP, inda ya ce da amincewar tsohon shugaban ƙasar ya sauya sheƙar ta siyasa. Sai dai daga baya Buhari ya fito ta bakin kakakinsa, Garba Shehu, cewa shi ɗan APC ne, kuma yana alfahari da kasancewarsa ɗan jam'iyyar, inda ya ce yana godiya ga magoya bayan APC, sannan zai yi duk mai yiwuwa domin samun nasararta. Sai dai daga lokacin aka samu wata goguwar siyasa ta tashi a ƙasar, inda aka fara maganar jiga-jigan ƴansiyasar ƙasar za su koma ...
Har yanzu akwai Talauci sosai a Najeriya, dan kuwa mutane da yawa har yanzu basu amfana da mulkin Tinubu ba>>Inji Hukumar IMF

Har yanzu akwai Talauci sosai a Najeriya, dan kuwa mutane da yawa har yanzu basu amfana da mulkin Tinubu ba>>Inji Hukumar IMF

Duk Labarai
Hukumar bayar da lamuni ta Duniya, IMF ta bayyana cewa, har yanzu akwai talauci sosai a Najeriya. Hukumar tace har yanzu Najeriya na fuskantar rashin tabbas game da tattalin arziki duk da gyare-gyaren data gudanar. Shugaban hukumar a Najeriya, Axel Schimmelpfennig ya bayar da tabbacin cewa, Najeriya ta dauki matakai masu muhimmanci wajan tayar da komadar tattalin arziki amma matsalar itace kidaden shiga da take samu zasu samu tangarda musamman saboda faduwar farashin danyen mai a kasuwannin Duniya. Saidai IMF tace har yanzu da yawan 'yan Najeriya basu amfana da tsare-tsaren na gwamnatin ba inda da yawa ke fama da talauci sannan matsalar tsaro na karuwa.
Na baiwa Jami’an tsaro umarni da kakkausar murya su gaggauta kawo karshen matsalar tsàròn Najeriya>>Shugaba Tinubu

Na baiwa Jami’an tsaro umarni da kakkausar murya su gaggauta kawo karshen matsalar tsàròn Najeriya>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, ya baiwa jami'an tsaron Najeriya umarnin su gaggauta kawo karshen matsalar tsaron da ake fama da ita ba tare da jinkiri ba. Shugaban wanda yanzu haka yana kasar Faransa, ya bayyana hakane a sanarwar taya kiristoci murnar bukin Easter. Shugaban yace karuwar matsalar tsaro da kashe-kashe na kwanannan ya matukar dameshi inda yace yana bayar da tabbacin samar da tsaro. Sannan kuma ya mika sakon jaje ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa dasu inda yace yasan irin radadin da suke ji. Shugaba yace ya kuma baiwa jami'an tsaro umarnin su gaggauta kawo karshen matsalar tsaro a kasarnan.