Gwamnan Kano ya jagoranci tawogar Kano da Jigawa zuwa halartar jana’izar Dantata a Madina
Gwamnan Kano ya jagoranci tawogar Kano da Jigawa zuwa halartar jana'izar Dantata a Madina.
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya tashi daga Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano, inda yake jagorantar wata babbar tawaga domin halartar jana’izar fitaccen attajiri kuma dattijon kasa, marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantata, a birnin Madina mai alfarma, da ke Kasar Saudiyya.
Marigayin ya rasu da safiyar Asabar a birnin Abu Dhabi na Hadaddiyar Daular Larabawa.
Wannan bayanin na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.
Tawagar tana dauke da Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, tsohon gwamnan Jigawa Barr. Ali Sa’ad Birnin Kudu, da wasu manyan jami’an gwamnati da fitattun dattawa...







