An sami rashin fahimta tsakanin ƴan majalisa da ministan tsaron Najeriya kan tsaro
Ministan tsaron Najeriya, Mohamamd Badaru Abubakar ya ce sauya dabarun tsaro ne abun da ya kamata a mayar da hankali ba wai taro kan tsaro ba, da majalsair dattawwan ƙasar ta nemi a yi ba.
Haka kuma ya musanta zargin da majalisar wakilan ƙasar ta yi na cewar ƴan bindigar na amfani da makaman da suka fi na jam'an tsaron ƙasar.
A ranar Talata ne dai majalisar dattawan Najeriya suka buƙaci da a shirya wani taro kan harkokin tsaro, don samar da hanyoyin magance matsalar.
Sai dai a yayin ganawa da manema labarai na ministoci da ya gudana a jihar Laraba ministan tsaron na Najeriya Mohammad Badaru Abubakar ya ce sakae dabarun yaƙi da mastaalr tsaro ya kamata a yi ba wai taro ba a halin da ake ciki a ƙasar.
"Idan ka yi taron ƙasa kan tsaro, mutane za su zo, su fadi abin da suke so, mu ...








