Atiku Abubakar ya bayyana cewa ba zai bar jam’iyyar PDP ba amma ya fadi dabarar da zasu yi amfani da ita dan kawar da Gwamnatin Tinubu
Madugun Adawar Siyasa A Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cewa yana nan daram a cikin jam’iyyar PDP, kuma ba shi da niyyar ficewa daga cikinta. Ya bayyana hakan ne a wata ganawa da mata mambobin Kwamitin Amintattu na jam’iyyar (BoT) da suka kai masa ziyara domin neman hanyoyin ceto jam’iyyar daga rushewa gaba daya.
A cewar Atiku, rahotannin da ke cewa yana shirin barin PDP zuwa wata jam’iyya kamar SDP ba su da tushe balle makama, kuma an kirkire su ne domin rikita shirin kafa kawancen jam’iyyun adawa da ake yi. Ya jaddada cewa yana nan a matsayin cikakken memba na PDP, kuma yana jagorantar yunkurin kafa kawancen jam’iyyun adawa domin kalubalantar jam’iyyar APC a zaben 2027.
A wata ganawa da aka yi a Abuja, Atiku y...







