Kalli Bidiyon yanda aka jefi shugaban kasar Kenya da Takalmi
Gwamnatin Kenya ta bayyana jifa da takalmi da aka yi wa shugaban ƙasar, William Ruto a wani gangamin siyasa a ranar Lahadi, a matsayin “abun kunya”.
Bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta ya nuna yadda takalmin ya bugi hannun shugaban ƙasar na hagu, a yayin da ya ke magana.
https://twitter.com/citizentvkenya/status/1919295562660098502?t=JznCzRShAKV-GnuJ17gZpg&s=19
Mai magana da yawun gwamnatin ƙasar, Isaac Mwaura, ya yi Alla-wadai da lamarin tare da kiran a kama waɗanda suka aikata hakan.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ya ce “me zai faru idan dukkanmu muka fara jifar juna da takalma? Wane tarbiyya muke koya wa ƴaƴan mu?” Ya kuma buƙaci a girmama muƙamin shugaban ƙasa.
Kafofin watsa labarai a Kenya na bayar da rahoton cewa an kama mutum uku dangane da lam...








