Manyan Malaman Cocin Katolika 2 da ake tsammanin zasu gaji Fafaroma Francis an samesu da zargin yin rufa-rufa game da cin zàràfìn yara ta hanyar yin làlàtà dasu
Manyan Malaman cocin Katolika 2 da ake tsammanin na daga cikin wanda zasu gaji Fafaroma Francis ana zarginsu da yin rufa-rufa game da binciken cin zarafin kananan yara.
Malam sune Cardinal Pietro Parolin dan kasar Italiya, sai Cardinal Luis Antonio dan kasar Philippines.
Wata kungiya dake saka ido kan irin wannan lamari ta kasar Amurka, The American watchdog Bishop Accountability ce ta bayyana hakan inda tace duka malaman biyu ana zarginsu da yin rufa-rufa wajan binciken malaman cocin da aka kama da lalata da kananan yara.
Daya daga cikin shuwagabannin wannan kungiya me suna Anne Barrett Doyle ta bayyana cewa, an kaiwa Cardinal Pietro Parolin korafe-korafen cin zarafin yara ta hanyar lalata dasu da suka faru a kasashen Duniya daban-daban amma sai yayi rufa-rufa yaki bin diddigin ...








