Sai Talaka ya Dara: Na sha Alwashin karya farashin shinkafa warwas>>Inji BUA
Shugaban rukunin kamfanonin kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya alƙawarta sake rage farashin shinkafa da sauran kayan abinci, wanda ya ce tun shekarar da ta gabata yake ta sauka.
Abdul Samad Rabiu ya bayyana haka ne ranar Alhamis jim kaɗan bayan ganawarsa ta Tinubu a fadar shugaban ƙasar.
Shugaban na BUA ya yaba wa Tinubu kan bayara da damar shigo da wasu kayan abinci da ya yi, yana mai bayyana matakin da 'kyakkyawa'' da ya ce ya taimaka wajen karyewar farashin kayan abinci a ƙasar.
A watan Yulin 2024 ne gwamnatin Shugaba Tinubu ta bayayna dakatar da karɓar kudin fito na shigo da kayan abinci a wani mataki na magance hauwarar farashin kayayyaki.
BUA ya zargi masu sayen kayyaki domin ɓoyewa da haddasa tashin farashin.
Ya ce da zarar lokacin girbe amfanin gona ya yi, sai wasu ...








