Iran ta kashe Miliyoyi wajan harbawa Israyla makamai amma Israyla ta kashe Biliyoyi wajan taresu>>Zakzaky
Shugaban kungiyar 'yan Uwa Musulmi ta Najeriya wadda aka fi sani da shi'a, Ibrahim Zakzaky ya bayyana cewa, kasar Iran Miliyoyin kudade ta kashe wajan kaiwa kasar Israyla hare-hare.
Saidai yace ita kuma Israylan ta kashe Biliyoyi ne wajan tare wadannan hare-haren.
https://www.tiktok.com/@abubakarj.labbaika/video/7515847622884642054?_t=ZM-8xE9vT3lwDV&_r=1
Ya bayyana hakanne a wani faifan Bidiyon sa da aka gani yana jawabi akan yakin da ya barke tsakanin kasar Israyla da Iran.








