Sunday, March 22
Shadow

Author: Bashir Ahmed

DA ƊUMI-ƊUMINSA: Zanga-zanga Ta Barke A Birnin Tarayyar Abuja

DA ƊUMI-ƊUMINSA: Zanga-zanga Ta Barke A Birnin Tarayyar Abuja

Duk Labarai
Gungun Malaman Firamare da sauran ma'aikatan ƙananan hukumomin Abuja sun gudanar da zanga-zangar lumana a kan tituna, kan rashin biyan su mafi ƙarancin albashi, da sauran haƙƙoƙin da suke bin shugabannin ƙananan hukumomi 6 da ke Abuja. Sun gudanar da zanga-zangar ne a yau Alhamis a ƙarƙashin ƙungiyar malaman makaranta ta NUT, da kuma ƙungiyar ma'aikatan ƙananan hukumomi ta NULGE.
Ƴansanda biyu sun jikkata yayin artabu da ƴandaba a Kano

Ƴansanda biyu sun jikkata yayin artabu da ƴandaba a Kano

Duk Labarai
Ƴansanda biyu sun jikkata yayin artabu da ƴandaba a Kano. Ƴansanda biyu, Abdullahi Ibrahim da Yahaya Saidu, sun samu raunuka yayin wani kazamin fada da wasu gungun 'yan fashi da makami a jihar Kano. Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Kano, SP Abdullahi Kiyawa, ya fitar wa manema labarai a Kano a jiya Laraba. “Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta amsa kiran gaggawa a ranar 22 ga Afrilu, 2025, da misalin karfe 1 na rana dangane da wani gungun ‘yandaba da ake zargi Halifa Baba-Beru daga unguwar Gwammaja, karamar hukumar Dala, ya na jagoranta. “An rawaito cewa gungun yandaban na dauke da muggan makamai kuma su ka rika kai hari kan al'umma a unguwar Gwammaja, Dala LGA, Kano. “Lokacin da ‘yansanda suka isa wurin, sai yan...
Gwamnatin Tinubu zara dawo da shirin ciyar da dalibai na tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari

Gwamnatin Tinubu zara dawo da shirin ciyar da dalibai na tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari

Duk Labarai
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da cewa za ta sake ɗaddamar da shirin ciyar da ɗalibai a makarantu, ranar 29 ga watan Mayu. Ƙaramin Ministan ma'aikatar jin-ƙai da rage talauci, Dr Yusuf Sununu ne ya bayyana hakan a ranar Larabar da ta gabata yayin wata ganawa da ƙungiyoyi masu zaman kansu da kuma jami’an gwamnati a Abuja. Sununu ya sanar da cewa za a sake kaddamar da shirin ne domin murnar cikar shugaba Bola Tinubu shekara ta biyu akan karagar mulki. Ya ce shirin na da nufin magance yunwa da kuma inganta ɓangaren ilimi a faɗin ƙasar baki ɗaya. ''Shirin na nufin amfanar yara miliyan 10 kuma zai iya ƙara yawan yaran da ke shiga makarantu da kashi 20 cikin 100 sannan kuma ya bunƙasa hazaƙar yara a ɓangaren karatu da kashi 15 cikin 100 ,” in ji shi. Sake ƙaddamar da shirin ...
Dalla-Dalla: Ji Yanda Kawu sumaila ya fadi dalilan da suka sa ya koma APC

Dalla-Dalla: Ji Yanda Kawu sumaila ya fadi dalilan da suka sa ya koma APC

Duk Labarai
Bayan jan ƙafa na tsawon lokaci, ɗaya daga cikin ƴan majalisar dattawa na jam'iyyar NNPP Sanata Abdurahman Kawu Sumaila ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC. Matakin na zuwa ne bayan shafe watanni ana takun saƙa tsakanin Sanatan da jam'iyyarsa ta NNPP a jihar Kano. A makon da ya gabata ne Sanata Kawu Sumaila ya jagoranci wata tawagar yanmajalisar tarayya na NNPP inda suka gana da shugaban jam'iyyar APC mai mulki kuma tsohon gwamnan jihar Kano. A hirar da ya yi da BBC, Sanatan ya bayyana dalilansa na ficewa daga jam'iyyar NNPP, inda ya tabbatar da cewa ya ɗauki matakin ne domin samar da ci gaba ga al'ummar mazaɓarsa. Ya ce ''Wasu daga cikin dalilan da za su sa mu fice shi ne yankin da muka fito. Ya za mu iya samar wa mutanen yankin mu wani abu da zai amfanar da su, kuma ai ita siya...
Yajin aikin ma’aikatan NIMET ya hana wasu jirage tashi a Najeriya

Yajin aikin ma’aikatan NIMET ya hana wasu jirage tashi a Najeriya

Duk Labarai
Harkokin sufurin jiragen sama na fuskantar cikas a filayen tashi da saukar jiragen sama na cikin gida yayin da ma'aikatan hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMET) ke gudanar da yajin aikin kan rashin ingancin yanayin aiki. Yajin aikin da ya yi kwana biyu yana gudana ya haifar da maƙalewar fasinjoji a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja, da filin jirgin Murtala Muhammed da ke Legas da sauran filayen jiragen sama da ke faɗin ƙasar. Kamfanin sufurin jiragen sama mafi girma a Najeriya, Air Peace ya sanar da dakatar da ayyukansa sakamakon yajin aikin. Kamfanin ya sanar da cewa ya yanke shawarar dakatar da sufurin jiragensa ne saboda kiyaye rayukan fasinjojinsa. Kafar yaɗa labarai ta Channels ta rawaito cewa a filin jirgin saman Legas, kamfanin XEJET da Aero Contractors, d...
Tsadar Rayuwa: Yanzu Tukunyar Shinkafa dafa duka Sai an kashe mata Naira 25,000 ake samun yanda ake so>>Inji SBM

Tsadar Rayuwa: Yanzu Tukunyar Shinkafa dafa duka Sai an kashe mata Naira 25,000 ake samun yanda ake so>>Inji SBM

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, a yanzu tukunyar shinkafa dafa duka wadda mutane 5 zasu iya ci a gida sai an kashe mata Naira 25,486 kamin ta bada abinda ake so. Hakan ya nuna an samu karin kaso 20 cikin 100 na farashin dafa shinkafar idan aka kwatanta da farashin dafata a watan Sarumba na shekarar 2024 wanda a wancan lokacin Naira 21,300 ake kashewa wajan Dafa shinkafar. SBM na fitar da bayanai akai-akai kan farashin dahuwar shinkafa kasancewarta itace abu mafi saukin sarrafawa a gidajen 'yan Najeriya. Kuma wannan farashi da suka bayyana suna maganar shinkafa ce wadda ta ji komai tun daga nama mai Albasa da komai dai da ake hadawa shinkafa dafa duka irin su kayan miya magi da sauransu. Sun alakanta hauhawar farashin da tashin farashin kayan masarufi wanda hauhawar farashin man fe...
Saurari Sabuwar Wakar Hamisu Breaker da Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta hana Saurare saboda Haramun ce tana karfafa Zìnà

Saurari Sabuwar Wakar Hamisu Breaker da Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta hana Saurare saboda Haramun ce tana karfafa Zìnà

Duk Labarai
Sabuwar Wakar Hamisu Breaker Ta Amanata ta gamu da fushin hukumar Hisbah a jihar Kano i da aka Haramta Saurarenta a jihar savoda tana karfafa Zìnà. Bayan da hutudole yawa wakar sauraren tsanaki da kuma bincike kan lamarin, mun gano cewa a wakar Hamisu ta Amanata ba mace, duka muryarsa ce. https://www.tiktok.com/@prince_abdool/video/7493982702161448197?_t=ZM-8vncFNyuyXt&_r=1 Inda matsalar take itace yanda mata ke kwaikwayon abinda ya fada daidai inda yake fara cewa "Mai Kishina ina sonki...." har zuwa karshe suna dorawa a kafafen sada zumunta. Misali kamar wannan ta kasa: https://www.tiktok.com/@khairatupcomingbackup/video/7495827859122982149?_t=ZM-8vnbxrfEPn3&_r=1 Wakar dai ba ta wani yi suna sosai ba, amma idan ba sa'a ba, wannan dakatarwar da Hisbah ta wa wa...
Hukumar Hizbah Ta Jihar Kano Ta Haramta Sauraron Wakar Hamisu Breaker Mai Suna ‘Amanata’ inda tace Zìnà wayar ke nunawa dan haka Haramunne sauraronta

Hukumar Hizbah Ta Jihar Kano Ta Haramta Sauraron Wakar Hamisu Breaker Mai Suna ‘Amanata’ inda tace Zìnà wayar ke nunawa dan haka Haramunne sauraronta

Duk Labarai
Hukumar Hizbah Ta Jihar Kano Ta Haramta Sauraron Wakar Hamisu Breaker Mai Suna 'Amanata' Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta yi kira ga matasa da su ƙauracewa sauraron waƙar Amanata ta Hamisu Breaker, tana mai cewar wannan waƙar haramun ce baki ɗaya. Mataimakiyar Babban Kwamandan Hisbah a ɓangaren Mata Dakta Khadija Sagir Sulaiman ce ta bayyana hakan, ta ce, waƙar ta fito ƙarara tana nuna źìña daga yadda mata suke hawa suna irin wani lanƙwashe-lanƙwashe da karya murya.
Wata Sabuwa: A yayin da suke shirin kulla alaka me karfi dan kwace mulki a 2027, an gano cewa Gwamnonin PDP sun daina daukar wayoyin Atiku da El-Rufai idan sun kirasu

Wata Sabuwa: A yayin da suke shirin kulla alaka me karfi dan kwace mulki a 2027, an gano cewa Gwamnonin PDP sun daina daukar wayoyin Atiku da El-Rufai idan sun kirasu

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa a yayin da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ke shirin kulla alaka me karfi dan kayar da Tinubu a zaben shekarar 2027, Gwamnonin PDP sun daina daga wayarsu idan sun kirasu. Wani Jigo a jam'iyyar APC, Ayekooto Akindele ne ya bayyana hakan. Yace Gwamnonin PDP irinsu Ademola Adeleke basa daukar wayar Atiku da El-Rufai da rana a yanzu. Yana martanine kan rahoton dake cewa, Gwamnonin PDP din sun hada kai da Tinubu dan bashi goyon baya ya zarce a shekarar 2027. Ya kara da cewa, Babu yadda Atiku da El-Rufai zasu iya hana Tinubu zama shugaban kasa a shekarar 2027.