Hotunan Yayar Gwamnan Jihar Katsina Kuma Mai Ɗakin Tsohon Shugaban Kasa, Malam Umaru Musa Yar'adua, Hajiya Hauwa Radda A Wajen Bikin Diyar Gwamnan Katsina A Ranar Asabar Da Ta Gabata.
2027 : Allah ne ya fad@ Mani cewa nine shugaban kasa mai zuwa__Fasto Tunde
Daga Barista Nuraddeen Isma'eel
"Babban malamin addinin kirista a Nijeriya Fasto Tunde, ya shaidawa mabiyan shi a cikin coci cewa, Allah ya fada mashi kuma yaji da kyau! Akan cewa shine shugaban kasar Nijeriya mai zuwa a zaben kakan bana mai zuwa ta 2027 .
"Biyo bayan sanar da shi da Allah yayi, yasa baiyi kasa a gwiwaba na wurin zuge miliyan 100 a domin sayen fam din Takarar shugaban kasar Nijeriya."
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya cewa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu idan da gaske yake maganar daina amfani da abubuwan da aka kera a kasashen waje to ya daina amfani da motocin Alfarmar da yake hawa ya koma Amfani da motar Innoson da ake kerawa a jihar Anambra.
Ya bayyana hakanne bayan da shugaba Tinubu ya baiwa ma'aikatun gwamnati umarnin su daina shigo da kayan da ake yin irin su a Najeriya.
Saidai Atiku yace wannan duk yaudara ce wadda 'yan Najeriya sun saba ji, yace idan Gwamnatin da gaske take, ta fara daga kan kanta.
Yace kamata yayi shugaba Tinubu ya fara da kanshi, ya daina amfani da motocin Alfarma da yake amfani dasu ya koma amfani da motocin Innoson ko makamantansu da ake kerawa a Najeriya.
Yace ministocin Buharin ma haka ya kamata su ...
Wannan ɗaya dagga cikin wa "yanda suka rasa rayukansu a harin "yan bindiga a jiya da misalin karfe 5pm AGARIN BURMUKAI, DANGULBI, MARU, ZAMFARA STATE OF NIGERIA
Mai martaba Sarkin Daura Alhaji Umar Farouk ya bayyana cewa ba domin kuɗi Masarautar ke nade-naden sarauta ba, suna yi ne domin neman Aljannah.
An jiyo Sarkin ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen yada labarai, ya yin da masarautar ke naɗa wani muƙami. Mene ne ra'ayoyin ku?
Me za ku ce?
Kungiyar dake ikirarin jìhàdì ta Ansaru ta je kusa da babban birnin tarayya Abuja ta kafa sansani.
Rahoton yace kungiyar wadda ta balle daga Bòkò Hàràm ta kuma kafa sansanoni 8 a cikin jihar Kogi.
Wasu daga cikin sansanonin kungiyar na tsakanin Obajana da Kabba wanda hakan yasa manyan mutane dake wucewa ta wajan biyan kudi masu yawa dan samarwa kansu tsaro yayin wucewa ta wajan.
Rahoton yace babban wajan horas da 'yan kungiyar na kilomita 93 ne tsakaninsa da babban birnin tarayya, Abuja.
Kokarin jinn ta bakin hukumomin tsaro kan lamarin ya ci tura.
Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu ya bayyanawa ma'aikatun wutar Lantarki na kasa cewa Gwamnati ba zata sake amincewa da rashin samar da wutar lantarkin ba.
Ya bayyana hakane bayan amincewa da sabon daftarin gyaran wutar.
Yace kuma an samar da wani sabon tsari na baiwa ma'aikatan wutar Lantarkin horaswa ta musamman. Inda yace nan da shekaru 10 za'a magance matsalar karancin ma'aikata a hukumar wutar lantarkin.
Raɗe-raɗin dawowar Kwankwaso jam'iyyar APC mai mulki, na cigaba da fitowa fili.
An samu rudani a sakateriyar jam’iyyar APC, a ranar Talata, bayan da Shugaban jam’iyyar na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da Ministan Jiha na Harkokin Gidaje da Ci gaban Birane, Yusuf Ata, suka yi sabani kan daowawar Kwankwaso jam'iyyar APC.
Yayin da Minista Ata ke cewa Kwankwaso – wanda kuma tsohon Ministan Tsaro ne – ya rasa karbuwa a Kano kuma siyasar sa na dab da mutuwa, Ganduje ya ce APC ba lallai ta ki karbansa ba, yana mai cewa “aboki a lokacin bukata, aboki ne na gaskiya.”
Ata, yayin da yake zantawa da manema labarai bayan ganawa da Ganduje a sakateriyar jam’iyyar da ke Abuja, ya bayyana cewa matsin lambar siyasar da Kwankwaso ke ciki ne ke sa shi kokarin dawowa APC, yana mai cewa har Kw...
Tauraron mawakin Hausa, Dauda Kahutu Rarara ya kuma dauki hotuna da uwargidansa bayan na amarya, A'isha Humaira da suka karade kafafen sadarwa.
https://www.tiktok.com/@mrsrarara/video/7501307799503146245?_t=ZM-8w9HQQia779&_r=1
An ga Rarara da Uwargidansa suna buga soyayya a hotunan da ya saki.