Sunday, February 22
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Majalisar Dinkin Duniya da kika kaini kara bata isa ta kirani in je ba, hakan ma da kika yi kin kara aikata wani laifinne>>Sanata Godswill Akpabio ya gayawa Sanata Natasha Akpoti

Majalisar Dinkin Duniya da kika kaini kara bata isa ta kirani in je ba, hakan ma da kika yi kin kara aikata wani laifinne>>Sanata Godswill Akpabio ya gayawa Sanata Natasha Akpoti

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Kakakin majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa, Majalisar mata ta majalisar Dinkin Duniya da Sanata Natasha Akpoti ta kaishi kara bata da hurumin da zata iya kiransa ya gurfana a gabanta. Ya bayyana hakanne ta bakin me magana da yawunsa, Eseme Eyiboh inda ya kara da cewa, lamarin na cikin gidane dan haka babu wanda ya isa ya saka musu baki. Yace majalisar bata da hurumin a matsayin Najeriya ta kasa me cin gashin kanta tace zata shiga wannan lamari. Saidai...
Sai da Buhari ya amince sannan na bar APC zuwa SD, Saboda babu wani abun da nake yi ba tare da na sanar da shi ba>>El-Rufai

Sai da Buhari ya amince sannan na bar APC zuwa SD, Saboda babu wani abun da nake yi ba tare da na sanar da shi ba>>El-Rufai

Duk Labarai
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce bai bar jam'iyya mai mulki ta APC ba har sai da tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya amince da batun barinsa jam'iyyar APC da komawa jam'iyyar SDP. "Da saninsa na bar APC. Sai da na je ranar Juma'a na faɗa masa cewa zan bar jam'iyyar. Saboda babu wani abun da nake yi ba tare da na sanar da shi ba. Ko lokacin da nake gwamnan Kaduna da zan naɗa kwamishoni sai da na kai masa jerin sunayen domin ya duba ya gani ko a ciki akwai wanda ya taɓa zagin sa. Bayan ya duba ya ce ba matsala Allah ya yi albarka. Duk abin da zan yi sai na yi shawara da shi." In ji Malam El-Rufai. Ko El-Rufa'i na da ubangida na siyasa? Da BBC ta tambayi Malam Nasiru El-Rufai ko yana da ubagida a siyasa? Sai ya ce ba shi da shi amma kuma yana da...
Rashin kunyarta da rashin bin dokar majalisa ce tasa muka dakatar da ita ba zargin da takewa Sanata Godswill Akpabio ba>>Majalisar Dattijai ta mayarwa da majalisar Dinkin Duniya martani kan dakatar da Sanata Natasha Akpoti

Rashin kunyarta da rashin bin dokar majalisa ce tasa muka dakatar da ita ba zargin da takewa Sanata Godswill Akpabio ba>>Majalisar Dattijai ta mayarwa da majalisar Dinkin Duniya martani kan dakatar da Sanata Natasha Akpoti

Duk Labarai
Majalisar Dattijai ta mayarwa da taron mata 'yan majalisa na Duniya dake gudana a majalisar Dinkin Duniya dake New York City na kasar Amurka martani kan dakatar da sanata Natasha Akpoti. Sanata Natasha Akpoti da majalisar dattijai ta dakatar ta halarci taron inda ta gabatar da korafin dakatar da ita da aka yi, duk da majalisar tace mata ba abinda ya tarasu a wajan kenan ba amma ta sha alwashin ji daga bakin majalisar dattijai ta Najeriya kamin daukar mataki. A martanin majalisar dattijai ta Najeriya wanda shugaban majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele ya aikewa majalisar Dinkin Duniya kuma 'yar majalisar wakilai dake halartar taron, wadda kuma itace shugabar kwamitin kula da harkokin mata da jin dadi na majalisar watau, Honorable Kafilat Ogbara ta karanto ta kishi cewa. Muna sanar ...
Duk da karar da Sanata Natasha Akpoti ta kai majalisar Dinkin Duniya, Majalisar Dattijai tace dakatarwar data mata na nan daram ba Fashi

Duk da karar da Sanata Natasha Akpoti ta kai majalisar Dinkin Duniya, Majalisar Dattijai tace dakatarwar data mata na nan daram ba Fashi

Duk Labarai
Majalisar dattijai tace dakatar war datawa Sanata Natasha Akpoti na nan Daram ba fashi. Ta bayyana hakane bayan zaman da manyan majalisar suka yi inda aka so kafa kwamiti dan warware matsalar dake tsakanin Sanata Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti. Saidai sanata Adams Oshiomhole ya bayyana cewa, janye dakatarwar da akawa Sanata Natasha Akpoti zai nuna cewa majalisar na da rauni dan haka kamata yayi jaddada dakatarwar da aka mata. Hakan kuwa aka yi inda sanata Danjuma Goje da Abdul Ahmed Ningi, da sauransu duk suka amince da wannan matsaya. Hakan na zuwane bayan da sanata Natasha Akpoti ta kai maganar gaban majalisar Dinkin Duniya.
Peter Obi ba zai bika zuwa SDP ba, APC zai dawo>>Fadar Shugaban kasa ta gayawa El-Rufai

Peter Obi ba zai bika zuwa SDP ba, APC zai dawo>>Fadar Shugaban kasa ta gayawa El-Rufai

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{"square_fit":1},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":true,"containsFTESticker":false} Fadar shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ta gayawa tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai da ya koma Jam'iyyar SDP cewa, Peter Obi ba zai bishi zuwa sabuwar Jam'iyyar tasa ba. Me baiwa shugaban kasa shawara ta musamman akan harkar sadarwa, Daniel Bwala ne ya bayyana haka yayin ganawar da aka yi dashi a gidan Talabijin na TVC. Daniel Bwala ya kawo misalin wasu 'yan Jam'iyyar Labour party da suka koma APC irin su Valentine Ozigbo, da Balami inda ya...
Ba abinda ya tara mu anan kenan ba amma Mun ji naki bayanin, ki dakata mu ji daga bakin wanda kike zargi, watau Sanata Godswill Akpabio kamin mu yanke hukunci>>Majalisar Dinkin Duniya ta gayawa Sanata Natasha Akpoti

Ba abinda ya tara mu anan kenan ba amma Mun ji naki bayanin, ki dakata mu ji daga bakin wanda kike zargi, watau Sanata Godswill Akpabio kamin mu yanke hukunci>>Majalisar Dinkin Duniya ta gayawa Sanata Natasha Akpoti

Duk Labarai
Majalisar mata ta majalisar Dinkin Duniya ta bayyanawa Sanata Natasha Akpoti cewa, ta ji zargin da takewa kakakin majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio sannan zata so ji daga bakin sanata Godswill Akpabio din da majalisar dattijai ta Najeriya kamin sanin matakin da ya kamata ta dauka. Kakakin majalisar, Tulia Ackson ce ta gayawa Sanata Natasha Akpoti haka bayan da ta gama bayyana korafinta. Ta cewa sanata Natasha Akpoti maganar da ta yi bata cikin abinda ya tarasu a majalisar amma duk da haka zasu ji daga bakin majalisar dattijai ta Najeriya da kuma wanda ake zargi, Sanata Godswill Akpabio kamin su dauki mataki. A jiya ne dai Sanata Natasha Akpoti ta kai kakakin majalisar kara a gaban kwamitin mata na majalisar Dinkin Duniya.
Zargin Da Natasha ke yi wa Sanata Godswill Akpabio cikin cokaline, An gano munanan abubuwan da ake zargin Sanata Akpabio da aikatawa wanda suka dame zargin da Natasha ke masa

Zargin Da Natasha ke yi wa Sanata Godswill Akpabio cikin cokaline, An gano munanan abubuwan da ake zargin Sanata Akpabio da aikatawa wanda suka dame zargin da Natasha ke masa

Duk Labarai
Kafar Gistlover da aka sani da yiwa shahararrun mutane Tonon silili ta bankado munanan ayyukan da ake zargin Kakakin majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio da aikatawa. Kafar tace tana da takardu da shaidar duk zargin da takewa Sanata Godswill Akpabio. Da farko dai tace Zargin da Sanata Natasha Akpoti kewa Akpabio cikin cokaline idan aka kwatanta abinda ake zarginsa dashi. Kafar tace Sanata Akpabio lokacin yana Gwamnan jihar Akwa-Ibom ya rika yin lalata da kwamishinoninsa, ciki hadda matan aure. Sannan yakan rikewa dan kwangila kudi ko takardu yace sai ya kai masa matarsa yayi lalata da ita. Hakanan Matarsa, 'ya'ya 4 mata ta haifa inda take neman da Namiji ido rufe, dalilin hakane yasa aka boyeta a kasar Amurka na tsawon watanni 9, aka siyo jariri daga gidan da ake hai...
Ana samun kudi a Najeriya amma yawancin ‘yan kasar basa samun kasonsu inda mafi yawa ke cikin bakin Talauci>>Bincike

Ana samun kudi a Najeriya amma yawancin ‘yan kasar basa samun kasonsu inda mafi yawa ke cikin bakin Talauci>>Bincike

Duk Labarai
Wani bincike da aka gudanar ya nunar da cewa ana samun kudi sosai a Najeriya amma mafi yawancin 'yan kasar basa shaida hakan. Rahotan wanda kamfanin dillancin Labaran Najeriya, NAN ya ruwaito yace duk da kudin da Najeriya ke samu amma mafi yawancin 'yan kasar watau kaso 63 cikin 100 na fama da matsanancin Talauci. Rahoton yace mafi yawanci matane suka fi fuskantar matsalar Talauci inda kuma basa samun ilimi yanda ya kamata.
Yawancin ‘yan Najeriya basa wuce shekaru 54 suke mutuwa>>Bincike

Yawancin ‘yan Najeriya basa wuce shekaru 54 suke mutuwa>>Bincike

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wani bincike ya bayyana cewa, yawancin 'yan Najeriya basa wuce shekaru 54 suke mutuwa. Kamfanin dillancin Labaran Najeriya, NAN ne ya ruwaito wannan bincike wanda ya alakanta hakan da rashin lafiya irin su cutar Kanjamau, Tarin TB, cutar Malaria da sauransu. Rahoton yace mata sun fi maza dadewa a Najeriya kamin su mutu inda su mafi yawanci suke mutuwa suna da shekaru 54.9, maza na mutuwa suna da shekaru 54.6. Saidai duk da haka wannan yawan shekaru yayi kasa da irin wan...
Zamu kawo man fetur da ya fi na Dangote sauki daga kasashen waje>>Inji ‘Yan kasuwar Man fetur na Najeriya

Zamu kawo man fetur da ya fi na Dangote sauki daga kasashen waje>>Inji ‘Yan kasuwar Man fetur na Najeriya

Duk Labarai
'Yan kasuwar man fetur din Najeriya sun sha Alwashin kawo man fetur din da ya fi na Dangote sauki daga kasashen waje. A matatar man Dangote, yana baiwa 'yan kasuwar man a kan farashin sari na Naira 825 kan kowace lita. Saidai 'yan kasuwar sun ce farashin sari da suke siyo man fetur din daga kasashen waje ya fadi zuwa Naira 774.72 akan kowace lita wanda hakan yasa ake sayar da man fetur din akan farashin Naira 800 a gidajen man fetur. 'Yan kasuwar sun ce farashin sari na Naira 774.72 da suke saro man fetur din daga kasashen waje ya nuna ana samun saukin Naira 50.28 akan kowace lita idan aka kwatanta da farashin sari da Dangote ke basu man fetur din. Wannan sauki da ake samu ne yasa da yawan 'yan kasuwar ke son daina siyan man a hannun Dangote inda suke son komawa siyowa daga kas...