Ganyen gwaiba na maganin infection
Ana amfani da Ganyen Gwaiba wajan magance matsaloli daban-daban na jikin dan Adam.
Kuma infection musamman na gaban mata na daya daga cikin abubuwan da ake amfani da ganyen gwaiba wajan magance su.
Saidai amfani da ganyen gwaiba wajan magance infection na mata a gargajiyance ne kadai ake hakan kuma ana yi ne ta hanyar dakashi ko markadashi a shafa a gaban macen.
Hakanan a wani kaulin ana amfani dashi wajan magance kaikayin gaba na mata, shima ba turawa ake yi cikin gaban ba, shafawa ake yi.
Saidai duka wannan a kimiyyar lafiya ba'a tabbatar dashi ba amma kuma ba'a bayyana wata illa da amfani da ganyen gwaban ke da ita ba wajan magance infection.
Ma'ana mutum zai iya gwadawa da neman dacewa, saidai a bi a hankali kada a yawaita amfani da ganyen kwaban saboda duk kyawun abu i...





