Saturday, July 11
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Likitoci dubu 30 ake dasu a Najeriya

Likitoci dubu 30 ake dasu a Najeriya

Duk Labarai
shugaban kungiyar Likitoci ta Najeriya, Professor Bala Audu ya bayyana cewa, Likitoci dubu 30 ne ake dasu a Najeriya. Ya bayyana hakane a wajan wani taron kungiyar likitocin da ya wakana a Jihar Katsina. Yace a shekaru 5 da suka gabata, Likitoci dubu 15 ne suka bar Najeriya zuwa kasashen Waje. Yace kowane Likita daya yana ganin marasa Lafiya dubu 8. Wanda a ka'ida marasa lafiya dari shida ne ya kamata ace kowane likita na gani.
Ana ta yiwa wani Fasto dariya bayan da yace an masa Wahayin Barcelona ce zata ci Inter Milan amma hakan bai faru ba

Ana ta yiwa wani Fasto dariya bayan da yace an masa Wahayin Barcelona ce zata ci Inter Milan amma hakan bai faru ba

Duk Labarai
Wani fasto na ta shan suka da dariya bayan da yace an masa Wahayin Barcelona ce zata ci wasan Champions League tsakanin ta Inter Milan amma hakan bai faru ba. Ya gayawa mabiyansa cewa PSG da Barcelona ne zasu buga wasan karshe kuma Barcelona ce zata dauki kofin. An dai ta yada Bidiyon wannan ikirari nasa kamin buga wasan. https://www.youtube.com/watch?v=lVc0oSMuyCs Saidai bayan buga wasan, An cire Barcelona. Da yawan kiristoci sun bayyana cewa dama faston karyane.
Wannan matar me suna Valentina Gomez ‘yar kasar Amurka nason a haramta Addinin Musulunci a cikin kasar Amurka

Wannan matar me suna Valentina Gomez ‘yar kasar Amurka nason a haramta Addinin Musulunci a cikin kasar Amurka

Duk Labarai
Wata mata me tsatstsauran ra'ayi me suna Valentina Gomez ta nemi a hana Addinin Islama a cikin jihar Texas. Ta bayyana hakane a yayin da ta je wajan wani taron musulmai ta afka musu da zagi da cin zarafi. Dama dai matar ta yi suna sosai wajan rashin kunya da nuna kiyayya ga Addinin Musulunci. Saidai da yawan Amurkawan basu yadda da wannan ra'ayin nata ba.
Bayan da ya sha matsa a hannun DSS, Shugaban Kungiyar daliban Najeriya a karshe ya yadda ya karyata kansa kan zargin da yawa dan shugabab kasa, Seyi Tinubu cewa ya sa an masa dukan kawo wuka

Bayan da ya sha matsa a hannun DSS, Shugaban Kungiyar daliban Najeriya a karshe ya yadda ya karyata kansa kan zargin da yawa dan shugabab kasa, Seyi Tinubu cewa ya sa an masa dukan kawo wuka

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} A karshe dai, Shugaban Kungiyar daliban Najeriya, Atiku Abubakar Isah ya fito ya wanke dan shugaban kasa, Seyi Tinubu kan zarge-zargen da ya masa. A baya dai An ga Bidiyon Atiku yana cewa Seyi Tinubu ya masa tayin karbar Naira Miliyan 100 dan ya goyi bayan babansa, Bola Ahmad Tinubu. Yace amma yaki amincewa shine Seyi Tinubun ya dauki nauyin 'yan daba suka lakada masa duka. Saidai bayan wannan zarge-zargen ne hukumar 'yansandan farin kasa, DSS suka kama shugaban daliban, kam...
‘Yan Bìndìgà sun kàshè soja me mukamin Kyaftin da wani soja daya a Borno

‘Yan Bìndìgà sun kàshè soja me mukamin Kyaftin da wani soja daya a Borno

Duk Labarai
''Yan Bindiga da ake kyautata zaton mayakan Bòkò Hàràm ne sun kashe soja me mukamin Kyaftin a garin Izge na karamar hukumar Gwoza ta jihar. Lamarin ya farune da safiyar ranar Laraba da misalin karfe 1 na dare. Hakanan aun kuma kashe soja daya. Sarkin Gwoza, Alhaji Mohammed Shehu Timta ya tabbatar da faruwar lamarin. Saidai sojojin da 'yan Bijilante da mutanen Gari sun yiwa 'yan Bòkò Hàràm din Rubdugu inda suka kashe 3 daga ciki, sauran suka tsere suka bar makamansu da Mashina 10. Sojoji dai na bin sahun wanda suka tsere.
Gwamna Zulum ya hana sayar da giya a jihar Borno

Gwamna Zulum ya hana sayar da giya a jihar Borno

Duk Labarai
Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya bayar da umarnin haramta sayar da barasa ko kuma giya a Maiduguri babban birnin jihar. Zulum ya ce an ɗauki matakin ne saboda yadda ake samun ƙaruwar rikici tsakanin masu adawa da juna a ƙungiyoyin asiri, da karuwanci, da ta'ammali da miyagun ƙwayoyi, da kuma ayyakan daba. "Na ji daɗi da na ga sojoji da ƴansanda da sauran ɓanagarorin tsaro na nan, saboda mafi yawan wadan nan abubuwa... wasu ne daga cikin sojojin da aka sallama daga aiki, da sauran jami'an tsaro da aka kora, da ma wasu daga cikin jami'an soji da ke aiki, da ma fararen hula," in ji Zulum. "Babu wani sabon abu a wannan doka, idan har muna son mu tsaftace birnin Maiduguri, to babu wanda za a bari."
Yan Nigeria kuji tsoron Allah ku daina Zargin Tinubu da cire Tallafin Man fetur, Saboda Bola Tinubu Ba shine ya cire Tallafin Man fetur Ba, Buharine>>inji Kawu Sumaila

Yan Nigeria kuji tsoron Allah ku daina Zargin Tinubu da cire Tallafin Man fetur, Saboda Bola Tinubu Ba shine ya cire Tallafin Man fetur Ba, Buharine>>inji Kawu Sumaila

Duk Labarai
Yan Nigeria kuji tsoron Allah ku daina Zargin Tinubu da cire Tallafin Man fetur, Saboda Bola Tinubu Ba shine ya cire Tallafin Man fetur Ba Yakamata yan Su Sannan Wannan, inji Kawu Sumaila Kada ku yanke Hukunci Naƙin ƙara Zaɓar Bola Tinubu Sabida cire Tallafin Man fetur Sam-Sam Tinubu Ba shine ya cire Tallafin Man fetur Ba Shi kawai Bayyanawa Yayi. Menene ra'ayinku?