Tuesday, March 17
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Mun gano cewa El-Rufai na kokarin Tadewa Tinubu kafa ya hanashi zarcewa a 2027, saidai abin da ke mana dadi ‘yan Arewa basu tare ashi>>APC

Mun gano cewa El-Rufai na kokarin Tadewa Tinubu kafa ya hanashi zarcewa a 2027, saidai abin da ke mana dadi ‘yan Arewa basu tare ashi>>APC

Duk Labarai
Jam'iyyar APC ta mayar da martani akan maganganu da avubuwan da tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ke yi. Kakakin APC, Ajibola Basiru ne ya bayyana hakan a wata ganawa da yayi da manema labarai inda yace abinda ke damun El-Rufai shine da bai samu ya zama minista a Gwamnatin Tinubu ba. Yace daga nan ne sai El-Rufai ya koma sukar Gwamnatin Tinubun, yace amma abinda ke musu dadi shine a Arewar ma shi ba wani me fada aji bane. Ya kara da cewa, El-Rufai na ta kokari ne kawai yaga ya kawo tarzoma da raba kai tsakanin Arewa da kudu, ta wannan hanyar ne yake son yin suna. Tsohon Gwamnan na Kaduna dai sunansa ya fito a cikin mutanen da Tinubu yaso ya nada a matsayin ministoci amma da yaje majalisa sai ya kasa tsallake tantancewar da aka yi kokarin yi masa. bayan ...

Akwai yiyuwar fadawa matsalar karancin man fetur a Najeriya saboda masu dakon man sun fusata sun daina dauka

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, akwai yiyuwar Najeriya ta fada matsalar karancin man fetur saboda masu dakon man fetur din sun dakata da dakonsa. Direbobi masu dakon man fetur din sun dakata da dakon man ne saboda zargin cin zarafinsu da ake yi da sukawa hukumar gwamnatin jihar Legas da ma'aikatar sufuri ta tarayya. Hakanan suma masu kamfanonin sadarwa sun yi gargadin cewa, za'a iya samun matsalar sabis idan direbobin dakon man suka daina daukar man saboda dashi suke amfani wajan gudanar da ayyukansu. Jaridar Punchng ta bayyana cewa a ranar Asabar da Lahadi da suka gabata direbobin man sun ki daukar man fetur din. Shugaban kungiyar direbobi ta NARTO Yusuf Othman ya bayyana cewa wannan lamari yayi kamari dan kuwa mahukuntan jihar Legas na kama musu motoci suna tafiya dasu ofis, suna...
An kama magidanci da ya Kkàshè matarsa

An kama magidanci da ya Kkàshè matarsa

Duk Labarai
'Yansanda a jihar Edo sun kama wani magidanci me sunan Kelvin Izekor bisa zargin kashe matarsa. Makwabtansu sun bayyana cewa, Kelvin da matarsa, Success Izekor basu dade da yin aure. Bidiyon lamarin da ya faru ya karade shafukan sada zumunta inda aka ga 'yansanda sun dauke gawar matar da sarar adda akanta. Kakakin 'yansandan jihar, Moses Yamu ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace mafusatan matasa sun so kashe mijin amma zuwan 'yansanda suka yi nasarar kubutar dashi. Yace sun tafi da mijin dan gudanar da bincike inda yace sun kai matar Asibiti inda likita ya tabbatar da cewa ta mutu. Yace duk wanda aka samu da laifi za'a hukuntashi.
Ba’a isa a hanamu yin hukunci da shari’ar musukunci ba>>Musulman Yarbawa suka mayarwa da Gwamnoninsu Martani

Ba’a isa a hanamu yin hukunci da shari’ar musukunci ba>>Musulman Yarbawa suka mayarwa da Gwamnoninsu Martani

Duk Labarai
Shugaban kotun shari'ar Musulunci dake jihar Kwara, Justice Abdurraheem Sayi ya bayyana cew basa bukatar amincewar hukumin Gwamnati ko na sarakunan gargajiya kamin su kafa kotun shari'ar Musulunci. Yace duk masu adawa da kafa kotunan shari'ar musulunci a jihohin Yarbawa kiyayyar addinin ce kawai ta sasu hakan ba wani abuba. Ya bayyana hakane a yayin da yake gabatar da yawabi a jami'ar Legas akan maganar shari'ar Musulunci a jihohin Yarbawa. Ya bayyana cewa ko shugaban kasa, doka bata bashi damar hana samar da kotun shari'ar Musulunci ba. Yayi kira ga mahukunta a yankin dasu bayar da dama ga musulman dake so su aiwatar da shari'ar Musulunci domin dokokin jihohinsu basu baiwa musulmai irin wannan dama ba.
Kuma Dai: Bidiyon Tsiraici na wata ‘yar TikTok ya kara bayyana

Kuma Dai: Bidiyon Tsiraici na wata ‘yar TikTok ya kara bayyana

Duk Labarai
A yayin da a baya aka yi fama da bayyana bidiyoyin tsiraici na 'yan TikTok irin su Babiana da Hafsat baby, an yi tsammanin abin ya wuce. Saidai a yanzu ma an sake kumawa inda bidiyon tsiraici na wata shahararriyar 'yar TikTok ya sake bayyana. Saidai a wannan karin lamarin yayi Muni. Matashiyar me suna Aisha dake da dubban mabiya a kafar ta sada zumunta an gantane wani namiji wanda bai nuna fuskarsa ba yana lalata da ita. A yayin da Su Babiana da Hafsat baby daukar kansu suka yi su kadai tsirara, ita kuwa A'isha wanda ke lalata da itace ya dauketa hoton bidiyon a yayin da yake aikata lalatar da ita. Munin bidiyon yasa ba zamu iya wallafashi anan ba.
Kalli Bidiyo: Maganar Gaskiya Yawancin Masu Kallon Mu Ba Su Da Cikaķķen Ilmi, Inji Jarumar Finafinan Hausa, Zahra Diamond

Kalli Bidiyo: Maganar Gaskiya Yawancin Masu Kallon Mu Ba Su Da Cikaķķen Ilmi, Inji Jarumar Finafinan Hausa, Zahra Diamond

Duk Labarai
Tauraruwar fina-finan Hausa, Zahara Diamond ta shiga bakin 'yan kafafen sada zumunta inda aka ganta a wani faifan bidiyo tana fadar cewa, yawanci masu kallonsu basu da ilimi. Bidiyon dai gajerene wanda ba'a sami cikakken shi ba. Saidai duk da haka mutane sau mata zafafan raddi suke. https://www.tiktok.com/@kannywoobackup/video/7474399386768854327?_t=ZM-8uB3tqfyU0T&_r=1 Me za ku ce?
Kalli Bidiyon Kwallon da Neymar yaci daga Corner data dauki hankula sosai

Kalli Bidiyon Kwallon da Neymar yaci daga Corner data dauki hankula sosai

Duk Labarai
Tauraron dan kwallon Santos, Neymar Jr. Ya ciwa kungiyarsa kwallo daga Corner wadda ta dauki hankula 'yan kallo sosai. Neymar ya ciwa Santos kwallon ne a wasanninsa na farko-farko da ya bugawa kungiyar. https://www.tiktok.com/@cfc.zx0/video/7474739218237967638?_t=ZM-8uB0E9qwmxh&_r=1 Kamin ya ci kwallon, Abokan hamayya sun rika wa Neymar Ehon bama so wanda yace su ci gaba inda ya buga Kwallon ya basu mamaki.
Sai mun hada kai da ‘yan kudu dan ceto Najeriya daga halin da take ciki>>El-Rufai

Sai mun hada kai da ‘yan kudu dan ceto Najeriya daga halin da take ciki>>El-Rufai

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, sai Arewa ta hada kai da 'yan kudu dan ceto Najeriya daga halin data tsinci kanta. El-Rufai ya bayyana hakane a yayin ziyarar gaisuwar da ya kai Jihar Delta ta gaisuwar mutuwar Edwin Clark. El-Rufai wanda tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar yawa jagora zuwa jihar Delta yace Arewa ta sha hada kai da kudu dan cimma burikanta na siyasa.
Mahara sun shiga coci suka yankewa Fasto yatsu suka kuma harbeshi sannan suka sace mutane 6

Mahara sun shiga coci suka yankewa Fasto yatsu suka kuma harbeshi sannan suka sace mutane 6

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Delta sun bayyana cewa, wasu mahara sun shiga coci a garin Asagba Ogwashi dake karamar hukumar, Aniocha South ta jihar ina suka harbi fasto suka sace mutane 6. Kakakin 'yansandan jihar, Mr. Bright Edafe ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace tuni jami'ansu suka bazama daji dan bin sahun masu garkuwa da mutanen. Zuwa yanzu dai maharan basu kira 'yan uwan wadanda suka sace din ba. Tuni aka garzaya da faston zuwa Asibiti dan duba lafiyarsa.