Sunday, March 15
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Bidiyo da hotuna masu daukar hankali, Sabuwar cuta ta sake bullowa daga kasar China, hankalin Duniya ya tashi, Najeriya ma ta fara killace mutanen dake zuwa daga kasar China a filin Jirgi

Bidiyo da hotuna masu daukar hankali, Sabuwar cuta ta sake bullowa daga kasar China, hankalin Duniya ya tashi, Najeriya ma ta fara killace mutanen dake zuwa daga kasar China a filin Jirgi

Duk Labarai
Wata sabuwar cuta ta sake bulla a kasar China me suna HMPV Virus. Cutar kamar dai Corona Virus itama na da alaka da sarkewar numfashi amma tafi kama kananan yara 'yan kimanin shekaru 14. A kasar Chinan, an dawo da irin dokar da aka yi lokacin da cutar CoronaVirus tazo, watau saka Face Mask da yin nesa-nesa da juna da sauransu. Saidai wani abin jin dadi shine wannan sabuwar cutar bata kai Coronavirus illa ba. A ranar Lahadi, Gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwar fara daukar matakin killacewa da kuma binciken lafiya ga dukkan mutanen da suka shigo Najeriya daga kasar China. Wannan cuta dai na zuwane shekaru 5 bayan bullar cutar Coronavirus. A kasar China, Asibitoci aun cika da mutanen da suka kamu da wannan sabuwar cuta inda ake ta yada hotuna da bidiyo a kafafen sada zu...
Kwamishina a jihar Kano ya ajiye muƙamin sa

Kwamishina a jihar Kano ya ajiye muƙamin sa

Duk Labarai
Kwamishinan Ma'aikatar Sanya Idanu a ayyukan gwamnati, Mohammed Diggol ya ajiye aiki. Labarin hakan ya fito ne ta bakin mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa a Ranar Lahadi a wata sanarwa da ya fitar a Kano. Tun da dare, Diggol shi ne Kwamishinan Ma'aikatar Sufuri kafin daga bayan gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya canja masa ma'aikata. Sai dai kuma kwanaki kadan da bashi sabuwar ma'aikatar Sa'id Diggol ya sanar da ajiye aiki a matsayin Kwamishina a gwamnatin Abba. Dawakin-Tofa ya ce Gwamna Abba ya karbi takardar ajiye muƙamin, inda ya kuma godewa Diggol tare da yi masa fatan alheri s rayuwarsa.
Mutumin da ya auri mata 3 a rana daya, yayi bayanin yanda zai gamsar da kowacce daga cikinsu a gado

Mutumin da ya auri mata 3 a rana daya, yayi bayanin yanda zai gamsar da kowacce daga cikinsu a gado

Duk Labarai
Mutumin da ya auri mata 3 a rana daya Arube Otor ya bayyana dalilinsa na yin hakan da kuma yanda zai gamsar dasu a gado. A hirarsa da jaridar Punchng ya bayyana cewa mahaifinsa ma mata da yawa ya aura kuma a gida daya suka zauna ba zaka gane banbanci tsakaninsu ba. Yace dan haka shima shiyasa yake son yayi gadon mahaifinsa. Yace dama yana da mata daya kamin auren matan 3 kuma nan gaba yana sonya kara auren guda biyu. Ya kara da cewa, game da maganar kwana, kowacce zata rika zuwa tana masa kwana 3 a turakarsa har kwanan kowacce ya zagayo.
Babban Fasto a Najeriya, Enoch Adebayo ya yi karin haske kan maganar cewa ya musulunta

Babban Fasto a Najeriya, Enoch Adebayo ya yi karin haske kan maganar cewa ya musulunta

Duk Labarai
Babban Fasto na cocin RCCG, Pastor Enoch Adebayo ya yi martani kan wani hotonsa da ke yawo a kafafen sada zumunta dake nunashi a kasar Saudiyya yaje aikin Hajji. Yayi martanin ne ranar Asabar, 4 ga watan Janairu a yayin bikin shiga sabuwar shekara. Yace nasan kunga hotona da aka nunani kamar Alhaji,... daga nan aka fashe da shewa a cocin nasa, saidai bai sake cewa komai ba, ya ci gaba da sha'aninsa. Da ganin wannan hoto dai na bogene.
Kasar Jamus ta Bude daukar ‘yan Najeriya aiki, tana neman mutane 400,000, duba yanda zaku nemi wannan damar aiki

Kasar Jamus ta Bude daukar ‘yan Najeriya aiki, tana neman mutane 400,000, duba yanda zaku nemi wannan damar aiki

Duk Labarai
Kasar Jamus dake Nahiyar Turai ta bude damar daukar 'yan Najeriya da sauran kasashen Duniya aiki inda take neman mutane akalla 400,000. Ana daukar aikinne na mutane masu basira ta kafar yanar gizo. Ofishin kula da harkokin kasashen waje na kasar Jamus din ne ya fitar da wannan sanarwar a ranar 1 ga watan Janairu. Wadanda ke son yin aiki a kasar ta Jamus ko haduwa da iyalansu dake can ko yin karatu duka na iya neman zuwa kasar. Ministar Harkokin waje ta kasar Jamus din, Annalena Baerbock ta bayyana cewa, ta wannan hanyar, zasu samu kwararrun ma'aikata da zasu taimakawa karfafa tattalin arzikinsu.
Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya yi karin haske kan maganar komawarsa PDP

Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya yi karin haske kan maganar komawarsa PDP

Duk Labarai
A dazu ne rade-radi suka watsu sosai a kafafen sada zumunta cewa, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya yanki katin shiga Jam'iyyar PDP a Unguwar Sarki Kaduna. A wancan lokacin ba'aji wata sanarwa daga bakinsa ba ko Jam'iyyar ta PDP. Mutane da yawa sun bayyana ra'ayoyi mabanbanta akan labarin inda wasu ke ganin hakan ba abin mamaki bane ganin yanda Gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta APC ta mayar da El-Rufai saniyar ware. Idan dai za'a iya tunawa, Gwamna El-Rufai na daya daga cikin na gaba-gaba da suka dage sai Tunubu ya zama shugaban kasa kuma bayan an kafa Gwamnatin Tinubu, ya bayar da sunanshi cikin wadanda zai baiwa Ministoci amma Sai El-Rufai ya kasa tsallake tantancewar majalisa. Tun bayan nan ne dai aka fara takun saka tsakanin El-Rufai da Gwamnatin Tinu...
Kamfanin BUA yayi magana kan Kammala matatar man fetur din da yake ginawa a Akwa-Ibom

Kamfanin BUA yayi magana kan Kammala matatar man fetur din da yake ginawa a Akwa-Ibom

Duk Labarai
Kamfanin BUA ya yi karin haske kan rahotanni dake yawo suna cewa ya kusa kammala matatar man fetur da yake ginawa a jihar Akwa-Ibom. Rahotanni sun bayyana cewa, aikin gina matatar ya kai kaso 90 cikin 100. Saidai a sanarwar da kamfanin ya fitar, yace wannan ikirarin ba gaskiya bane, tabbas yana kan aikinsa na gina mamatar man fetur din wadda zara rika samar da ganga 200,000 duk kullun amma maganar an kai kaso 90 cikin 100 na ginata ba gaskiya bane. Kamfanin ya kara da cewa, bayan Mamatar man fetur din akwai kuma tashoshin gas na CNG da zai gina.
Hotuna: Hukumar NDLEA ta kama wani dan fim yana Safarar Kwàyà

Hotuna: Hukumar NDLEA ta kama wani dan fim yana Safarar Kwàyà

Duk Labarai
Hukumar hana sha da fataucin miyagun Kwayoyi NDLEA ta kama wani dan fim din Najeriya me suna Emeka Emmanuel Mbadiwe da miyagun kwayoyi. An kamashi ne ranar Juma'a, 27 ga watan Disamba na shekarar 2024. An kama Emeka ne bayan da ya aika yaronshi ya je filin jirgin sama na Murtala Muhammad dake Legas dan karbomai kwayar da aka aiko masa daga kasar Amurka. Tuni dai aka tasa keyarsa dan ci gaba da bincike.
TIRƘASHI: Na Tsani Katsalaɲdan A Rayuwata, Døn Haka Babu Wanda Ya Isa Ya Hana Ni Buɗe Gashin Kaina, Saboda Ni Yin Magana Ne Ma Ke Sa Na Yi Abu, Koda Abinda Na Yi Ba Mai Kyau Ba Ne, Muddin Za A Ce Na Daina Ni Kuma A Wannan Lokacin Ne Ma Zan Fara, Inji Jarumar Finafainan Hausa, Nafisat Abdullahi

TIRƘASHI: Na Tsani Katsalaɲdan A Rayuwata, Døn Haka Babu Wanda Ya Isa Ya Hana Ni Buɗe Gashin Kaina, Saboda Ni Yin Magana Ne Ma Ke Sa Na Yi Abu, Koda Abinda Na Yi Ba Mai Kyau Ba Ne, Muddin Za A Ce Na Daina Ni Kuma A Wannan Lokacin Ne Ma Zan Fara, Inji Jarumar Finafainan Hausa, Nafisat Abdullahi

Duk Labarai
TIRƘASHI: Na Tsani Katsalaɲdan A Rayuwata, Døn Haka Babu Wanda Ya Isa Ya Hana Ni Buɗe Gashin Kaina, Saboda Ni Yin Magana Ne Ma Ke Sa Na Yi Abu, Koda Abinda Na Yi Ba Mai Kyau Ba Ne, Muddin Za A Ce Na Daina Ni Kuma A Wannan Lokacin Ne Ma Zan Fara, Inji Jarumar Finafainan Hausa, Nafisat Abdullahi. https://www.tiktok.com/@nafisatabdullahifan/video/7455341851034275078?_t=ZM-8soiodKtVQL&_r=1 Me za ku cre?