Sanata Ali Ndume daga jihar Borno yayi kira ga sarakunan dake karkashin mazabarsa da kada su yadda da sabuwar dokar haraji ta shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Ya bayyana hakane a yayin da ya kai ziyara Masarautar Askira, inda yace dalilinsa na kin amincewa da dokar harajin shine wahalar da mutane ke ciki, dan hakane yake kira da sarakunan da suma kada su amince da ita.
Yayi kira ga matasa da su tashi su rungumi harkar noma inda yace a daina dogaro da gwamnati da Albashi dan kuwa albashin Naira dubu 70 ba zai sayi buhun shinkafa ba dake Naira dubu 100 ko buhun wake dake Neman kaiwa Naira dubu dari 200.
Ya jinjinawa mutanen garin Gwoza saboda jajircewar da suka nuna duk da matsalar tsaron da suke fama da ita inda yace babu yanda za'a yi a rika kawo musu hare-hare ba tare da masu b...
Tsohon kakakin majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawal ya bayyana cewa, mutane na cikin matsin rayuwa kuma rabon kayan abinci ba shi bane mafita.
Ya bayyana hakane a wata sanarwa da ya fitar ta bakin kakakinsa, Ezrel Tabiowo bayan da ya je mazabarsa dake jihar Yobe ya raba kayan tallafi.
Yace kamata yayi a samarwa mutane hanya da zasu dogara da kansu amma rabon abinci zai kawo sauki ne kawai na dan lokaci wanda kuma wahalar zata ci gaba.
Saidai yace kamin su kai ga wancan matsayi, su dake da halin bayarwa zasu ci gaba da bada tallafin dan saukakawa mutane rayuwa.
Yayi kira ga masu rike da madafan iko dasu dauki matakan da zasu kawowa Al'umma saukin rayuwa.
Biyo bayan fara dawo da ci gaba da aikin matatar man fetur ta Warri, 'yan kasuwar man fetur sun bayyana kyakykyawan zatom cewa, farashin man fetur din zai sauka.
'Yan kasuwar sun ce yanzu gasa tsakanin masu matatun man fetur na cikin gida zata yi tsanani ta yanda dole za'a sauke farashin man fetur din.
Sun bayyana hakane ranar Litinin bayan fara aikin matatar man fetur ta Warri.
Kamfanin man fetur na kasa, NNPCL ya bayyana cewa, zai fara fitar da man fetur din zuwa kasashen waje dan samun kudin shiga.
Hakan na zuwane wata daya bayan da matatar man fetur da Fatakwal ta fara aiki.
Wani Bidiyo na wata mata data je kasar Saudiyya tana neman mijin aure ya dauki hankula.
An ga matar tana rokon Allah ya basu mazaje na gari kuma ya musu maganin matan da basu son mazan su su kara aure.
https://twitter.com/abu_twinss/status/1873417995084853639?t=dCJ0iopYxyj4cI2IO7ZqgQ&s=19
Kalli Bidiyon anan
A cikin Bidiyon, An jita tana fadar cewa, Allah muna son Aure amma matan sun hana, Allah ka yi mana maganinsu.
Wani magidanci a kasar Afrika ta kudu ya saki matarsa biyo bayan sumbatarta da mawakin kasar Amurka, Chris Brown yayi.
Mutumin me suna Lusaka dan kimanin shekaru 42 ya gamu da takaici ne bayan ganin hotunan sumbatar matarsa da Chris Brown din yayi.
Kwanannan dai Chris Brown din ya je kasar Afrika ta kudu inda yayi wasa sannan kuma ya gana da masoyansa inda a canne ya hadu da matar me shekaru 34.
Mijin yace abinda matar ta aikata rashin girmamashi ne kuma ya yiwa aurensu bacin da ba zai gyaru ba. Yace kuma abinda matar ta yi bai kamata ace matar aure ta aikata hakan ba.
Mijin dai yawa matar magana dan ya mata fada amma sai ta gaya masa cewa, wannan ba wani abin tada hankali bane.
Wata matar aure ta dauki hankula a kafafen sada zumunta bayan bidiyon data wallafa na korafi akan mijinta inda tace baya barinta ta huta, yana yawan neman Jima'i.
https://www.youtube.com/watch?v=LAF3JqC7sJ4
Tace kuma idan ta gaya masa ya hakura sai yayi fushi.
Ƙungiyar masu kamfanonin sadarwa a Najeriya ta yi gargadin cewa za a iya fuskantar katsewar network matuƙar ba a sauya tsarin yadda suke cajar kuɗaɗe a fannin sadarwa ba duk da yadda suke gudanar da ayyukansu ke ƙara tsada.
Shugaban ƙungiyar masu kamfanonin sadarwa da ke da lasisi a Najeriya Gbenga Adebayo ne ya bayyana hakan a yau Litinin cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce ɓangaren sadarwa na tsaka maki wuya saboda tashin gauron zabi da ake fuskanta sakamakon tashin farashin kayayyaki, da rashin tabbas a kasuwar musayar kudi da kuma tashin farashin makamashi.
Cikin sanarwar Mista Adebayo yace duk da ƙalubalen da ake fuskanta na gudanarwa, har yanzu ba su ƙara kuɗaɗen da suke cajar mutane ba, wani abu da yake barin masu kamfanonin cikin mawuyacin hali wajen kiyaye ingancin aikin d...
Wata budurwa mai suna Hafiza Rufaisa daga Gombe ta zama zakara a gasar karatun kur'ani ta kasa da aka kammala a Kebbi. Ta Samu kyautar motar, kudi, da sauransu.
Wani fata zaku mata mabiya shafin Gombe.
Daga Muhammad Chigari kumo
Alhamdu Lillah Addinin Musulunci ya samu ƙaruwa, wata budurwa ƴar kimanin shekaru 16 ƴar ƙabilar Igbo ta karɓi addinin Musulunci da sanyin safiya, ta canza suna zuma Maryam.
Kuma tace ba zata iya komawa gidan su ba saboda suna iya kashe ta, don haka ana neman wanda zai aure ta ya riƙe ta tare da koyar da ita addinin Musulunci.
Don Allah ana roƙon ƴan'uwa al'ummar Musulmi duk wanda yaci karo da wannan labarin ya taima wajen tura shi zuwa sauran groups ko Allah zai sa a samu wanda zai iya riƙe ta bisa amana