Saturday, April 25
Shadow

Author: Bashir Ahmed

An kama malamar makaranta da laifin yiwa dalibinta me shekaru 17 fyade har ta dauki ciki

An kama malamar makaranta da laifin yiwa dalibinta me shekaru 17 fyade har ta dauki ciki

Duk Labarai
Wata malamar makaranta a garin Rochdale Shawnee Nicole Despain me shekaru 26 na fuskantar tuhuma bayan da aka sameta da laifin yiwa dalibinta me shekaru 17 fyade. Malamar na karantarwa ne a makarantar Rockdale High School dake jihar Texas ta kasar Amurka. Da farko dai ta musanta zargin. Saidai daga baya an gano sakonnin soyayyar da suka rika aikawa juna ita da dalibin nata hadda ma hotunansa tsirara a wayarta. Sannan ta boyewa mijinta bata gaya mai cewa cikin da take dauke dashi ba nashi bane na dalibinta ne sai da aka yi bincike aka gano hakan. Malamar dai zata iya fuskantar hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari amma a yayin yanke hukunci, Alkali ya yanke mata hukuncin daurin talala na shekaru 10 sannan an kwace lasisinta na aikin koyarwa.
Har yanzu Hukumar HISBAH ta Kano ta kasa kwato Shafinta na Facebook da aka mata kutse ana ta saka hotunan batsa

Har yanzu Hukumar HISBAH ta Kano ta kasa kwato Shafinta na Facebook da aka mata kutse ana ta saka hotunan batsa

Duk Labarai
Shafin Facebook na hukumar HISBAH ta Kano har yanzu yana hannun wani bata gari da ya musu kutse kuma yace saka hotunan batsa a kansa. Tun a watan Augusta na shekarar 2024 ne dai aka yiwa shafin kutse inda Hukumar HISBAH din ta rasa iko dashi, yanzu watanni 6 kenan. Shugaban HISBAH, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace bangaren fasahar zamani na HISBAH suna kan kokarin dawo da shafin hannun hukumar. Saidai har yanzu shiru kake ji. Da Sahara Reporters suka tuntubi hukumar ta HISBAH tace har yanzu tana kan kokarin kwato shafin daga hannun bata garin da suke da iko dashi.
An kama mutane 2 da yiwa yarinya me shekaru 12 fyàd a jihar Yobe

An kama mutane 2 da yiwa yarinya me shekaru 12 fyàd a jihar Yobe

Duk Labarai
'Yansanda a jihar Yobe sun kama mutane 2 da ake zargin sun yiwa yarinya me shekaru 12 fyade a jihar. Lamarin ya farune a kauyen Jalingo dake karamar hukumar Tarmuwa ta jihar. Kakakin 'yansandan jihar, SP Dungus Abdulkarim ya tabbatar da faruwar lamarin a Damaturu ranar Litinin. Ya kara da cewa lamarin ya farune ranar 15 ga watan Fabrairu da misalin karfe 3:30 na rana inda wanda ake zargin suka ja yarinyar zuwa daji suka zakke mata. Ya kara da cewa, sun jiwa yarinyar ciwo inda aka kai ta Asibiti sannan kuma an kama wadanda ake zargin.
Dan Shugaban kasa, Seyi Tinubu ya bayar da tallafin Naira Miliyan 100 ga dalibai a jihar Borno

Dan Shugaban kasa, Seyi Tinubu ya bayar da tallafin Naira Miliyan 100 ga dalibai a jihar Borno

Duk Labarai
Dan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, Seyi Tinubu ya bayar da tallafin Naira Miliyan 100 ga dalibai da ambaliyar ruwa da aka yi a jihar Borno a watan Satumba na shekarar data gabata ya shafa. Dalibai daga makarantun gaba da sakandare 6 ne suka amfana da tallafin wanda ya hada da buhunan shinkafa, Taliya, Gishiri, Magi, Man Girki da sauransu. Da yake kaddamar da rabon tallafin, Seyi Tinubu yace ya bayar da tallafinne dan karfafa gwiwar daliban su koma da ci gaba da karatu a makarantunsu. Babban me baiwa shugaban kasar shawara akan harkar dalibai, Hon. Sunday Adebayo ne ya wakilci dan shugaban kasar inda yace gidauniyar NOELLA Foundation da Seyi Tinubu da abokansa ne suka bayar da tallafin. Ya kara da cewa an zabi daliban ne da lamarin yafi shafa kamin raba musu tallafin.
Shugaba Tinubu ya kashe Naira Biliyan 36 wajan Tafiye-Tafiye a shekarar 2024

Shugaba Tinubu ya kashe Naira Biliyan 36 wajan Tafiye-Tafiye a shekarar 2024

Duk Labarai
Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta a kashe Naira Biliyan 36.3 wajan tafiye-Tafiye a shekarar 2024 data gabata. Kafar Open Treasury Portal ce ta bayyana hakan a wasu bayanai data tattara inda tace shugaban ya kashe kudadenne wajan tafiye-Tafiye zuwa kasashen waje. Bayanan sunce idan aka hada da kudaden da shugaban kasar ya kashe a tafiye-Tafiyen da yayi na cikin gida, ya kashe jimullar Naira Biliyan 83 kenan. Yawan kudaden da shugaban ke kashewa wajan tafiye-Tafiyen sun sakawa 'yan Najeriya damuwa musamman ma lura da yanda gwamnati ke kukan karancin kudin gudanar da ayyuka. Peter Obi a kwanakin baya yayi kira ga shugaba Tinubu da ya rage yawan tafiye-Tafiyen da yake yi.
Hukumomi a jihar Anambra zasu fara kamen mata masu shigar banza

Hukumomi a jihar Anambra zasu fara kamen mata masu shigar banza

Duk Labarai
Wata hukumar tsaro a jihar Anambra ta bayyana aniyarta na fara kamen mata dake shigar banza wanda ke yawo babu rigar nono ko dan kamfai a cikin mutane. An nadi sautin sanarwar inda aka rika yayatashi a kafafen sadarwa. Hukumar tsaron ta bayyana cewa, Gwamnan jihar, Chukwuma Soludo ne ya bayar da umarnin yin hakan, saidai gwamnatin jihar bata fitar da sanarwa ba game da lamarin. Sanarwar tace mata masu saka dan kamfai kadai suma za'a fara kamasu.
Kalli Hotuna:An tsinci gawar jariri sabuwar haihuwa a Tudun Murtala, Kano

Kalli Hotuna:An tsinci gawar jariri sabuwar haihuwa a Tudun Murtala, Kano

Duk Labarai
'Yan Bijilante sun tsinci gawar jariri sabuwar haihuwa a Tudun Murtala Tagarji dake Kano. 'yan Bijilanten sun fita aiki ne da dare inda suka ga kwali a cikin wani rami an ajiye, nan suka budeshi suka ga ashe gawar jariri ne a ciki. Kwamandan Bijilante din, Sulaiman Rabiu ne ya tabbatar da haka inda yace sun tsinci gawar jaririnne da misalin karfe 2 na daren ranar Asabar. Yace sun dauki gawar zuwa ofishinsu inda suka kira me unguwa ya gani kamin daga baya su kai jaririn zuwa ofishin 'yansanda. 'Yansandan sun gaya musu cewa su tafi da gawar zuwa Asibiti dan a dubata inda likitoci suka tabbatar jaririn ya mutu. Sulaiman yace sun yiwa jaririn sallah inda aka binneshi kamar yanda addinin Musulunci ya tanada. Daga baya dai ya jawo hankalin iyaye da su rika saka ido akan 'ya...
Fusatattun Matasa sun Bankawa jami’in NDLEA wuta ya kone kurmus a Kaduna

Fusatattun Matasa sun Bankawa jami’in NDLEA wuta ya kone kurmus a Kaduna

Duk Labarai
Fusatattun matasa a garin Gadan Gayan dake karamar hukumar Igabi jihar Kaduna sun bankawa wani jami'in hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA me suna Aliyu Imran wuta ya kone kurmus. Lamarin ya farune bayan da Aliyu me mukamin Assistant Superintendent of Narcotic 1 tare da abokan aikinsa suka bi wani da ake zargi da safarar kwaya inda ya tsere a mota. Saidai garin gujewa ma'aikatan motar wanda ake zargin ta yi hadari inda hakan yayi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 3. Daga nan ne dai Aliyu yayi kokarin kwantar da tarzomar inda anan fusatattun matasa suka dakeshi tare da caka masa wuka. Anan 'yansanda suka daukeshi suka kaishi Asibiti, saidai daga baya matasan sun bishi har asibitin inda suka janyoshi suka banka mai wuta ya kone kurmus. Lamarin ya farune a ranar ...
Kuma Dai: Jirgin saman yakin sojojin Najariya ya kara Kkàshè farar hula 6 a katsina bisa kuskure

Kuma Dai: Jirgin saman yakin sojojin Najariya ya kara Kkàshè farar hula 6 a katsina bisa kuskure

Duk Labarai
Jirgin yakin sojojin Najariya ya kashe farar hula 6 a kauyen Zakka dake karamar hukumar Safana ta jihar Katsina bisa kuskure. Hakan ya farune bayan da wasu 'yan Bindiga suka kai hari ofishin 'yansanda suka kashe 'yansanda 2. Harin ya farune ranar Asabar data gabata inda sojojin suka wurga bama-bamai akan wasu bukkoki dake wajen garin na Zakka. Wasu shaidu 3 sun tabbatar da faruwar lamarin ga majiyarmu. Kamfanin dillancin labaran AFP ya tabbatar da faruwar lamarin.