Abubuwan dake kawo ciwon mara
Abubuwa da yawa na kawo ciwon Mara. Masana ilimin kiwon lafiya sun bayyana cewa yawancin ciwon Mara yana samo asaline daga abubuwan cikin jikin mutum dake daidai mararsa.
Ga jadawalin Abubuwan dake kawo ciwon Mara kamar haka:
Kananan Hanji.
Mafitsara
Babban Hanji.
Appendix.
Ovaries ko ace ma'ajiyar kwayayen haihuwa na mata.
Mahaifa.
Mafitsara.
Bladder ko ace majiyar fitsari.
Sannan akwai wani abu da ake cewa Peritoneum Wanda ke baibaye da kayan cikin mutum yake taimaka musu wajan yin aiki yanda ya kamata.
Duka wadannan abubuwa idan suna ciwo, mutum zai iya jin ciwon a mararsa.
Hakanan koda Idan tana ciwo, zata iya harbawa Mara, suma golaye ko 'yayan maraina idan suna ciwo, zasu iya harbawa Mara.
Hakanan infection da gyambon ciki Wanda make kira da u...





