Dakatarwar da Shugaba Tinubu yawa Gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara na Tangal-Tangal yana ta neman ‘yan Majalisa su amince masa domin idan basu amince ba dole ya janye dakatarwar
Rahotanni sun bayana cewa, dakatarwar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya wa gwamnan jihar Rivers Simi Fubara na Tangal-Tangal.
Dalili kuwa sai an samu biyu bisa uku na 'yan majalisar dattijai dana majalisar wakilai duka sun amince masa kamin wannan dakatarwa ta tabbata.
A yanzu haka rahotanni, kamar yanda jaridar TheCable ta ruwaito na cewa, wakilan shugaban kasar sai kai kawo suke a tsakanin 'yan majalisar dan ganin sun samo kansu sun amince da dakatar da Gwamnan jihar Rivers din.
Saidai matsalar itace mafi yawanci 'yan majalisar basa Najeriya, da yawansu sun je aikin Umrah inda wasu ke wasu kasashen.
Hakanan wata matsala itace banda 'yan majalisar dake jam'iyyun Adawa, har wadanda ke jam'iyyar APC an samu suna nuna rashin amincewa da wannan dakatarwar da akawa Gwamnan ji...








