Sunday, February 15
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Yadda ake yin pizza

Abinci
YADDA AKE YIN PIZZAAbubuwan Da Ake Bukata: Nikakken Nama Flour Albasa Yeast Tafarnuwa Mai Maggi Tumatur Farin masoro Yadda Ake Yi: Zaki Kwaba Flour ki da yeast da maggi da farin masoro da mai ko butter ki ajiye sai ya kumburo kaman kwabin cin~cin sai ki dauko nikakken namanki da kika soyashi sama~sama da maggi da garin tafarnuwa sai ki aje ki dauko flour nan ki gutsira ki murzata da dan tudu idan kuma falai~falai kikeso to sai kin gama murzawa sai ki debi wannan hadin ki zuba akai ki dauko tumatur dinki da kika jajjaga tare da attaruhu da albasa ki zuba akai ko kuma ki zuba kafin naman, sai ki murza wata flour kamar waccan sai ki rufeta dashi ki dora a farantin gashi bayan kin shafeshi da mai, ki barshi kamar 20 minutes sai ki fidda ita za kiga ya gasu ya...

Yadda ake kulacca

Duk Labarai
Kulacca 1) Vaseline ko cream2) garin misil3) garin sandal4) garin farce5) ambar6) matan arewa7) madaran turare kaman Kala uku da farko zaki samu tukunya ki daura a murhu sai kisa Vaseline ko cream dinda zakiyi amfanin dashi sai kibari sai ya narke kidan xuba ruwa kadan sai ya hade sai ki sa garin misil da garin sandal kina juyawa sai sun hade sai ki dauko ambar ki zuba ki juya ki sa matan arewa ki juya sai kisa garin farce kina juyawa sai yayi kauri sai ki zuba madaran turaren duka sai ki sauke ya huce sai kisa a robobi.

Yadda ake scotch egg

Abinci
Yadda ake SCOTCH EGG Kayan hadi:- KwaiFlowerBaking powderMaggiCurryGishiriAlbasaAttaruguTattasai Yadda ake yi:- Zaki dafa kwai adadin yadda kike bukata sai ki yanka albasa attarugu da maggi da gishiri ki soyasu sama sama, sannan ki kwaba fulawarki da butter da kwai mu murza da fulawa ko da abun murza taliya sannan kidauko kwan da kika dafa Zaki yanka shi biyu da wuka sai ki dinga yanka kwababen fulawar nan sai kidinga zuba soyayyen kayan miyanki a ciki sannan kinade da fulawa bayan kin nade sai ki kada kwai kidinga daukowa kina tsomawa acikin ruwan kwai kina soyawa.

Yadda ake dafa kazar amarya

Abinci
Hadin Kazar? Amare* Yanzu zamuyi bayanin sirrin dafa kazar Amare wanda idan har mace tayi kafin Aurenta da kamar sati 1 zataga amfaninsa,Irin wannan ne idan baki San sirrin ba zakije ki saya da tsada. ??Koda yake wasu kiwa ke hanasu yadawa da Kansu. To ga sirrin Yadda ake :Anaso kisamu bushashen ganyen magarya da kanunfari da idon zakara duk ki hadasu waje daya ki dakasu ki tankade su zama gari to idan kika samu:Budurwar kazar? kika gyarata saiki zuba wannan garin acikin tukunyar sannan zaki iya zuba kayan miya yanda kikeso. Bayan ta dafu saiki cinye gaba daya. Yana saka Farjin mace ya kumbura ya ciko da Ni'ima, kuma yana karawa mace dàn dàno… Matar Aure ma zata iya wannan Hadin ba lallai sai Amarya ba.

Yadda ake dafa ganda

Abinci
SLMYau nazo muku da yadda ake dafa ganda within some minutes duk taurinta,daga yau Baku basa qusa ko paracetamol ayayin dahuwar ganda. Dafarko zaki dauki gandarki kisa atukunya kisa ruwa yasha kanta,seki saka kanwa ungurnu babba aciki kirufe,kidora awuta kibarshi yayi tafasa kamar 3. Zakiga ruwan yayi baqi sosae,seki sauke ki barshi ya huce idan ya huce seki samu soson qarfe ki wanke abarki Tass se bakin yafita da qasar jiki. Seki sake dorata awuta kisa wata kanwar kadan kibarta taqara tafarfasa,zakiga ruwan yayi danqo seki zubar ki dauraye. Ki sa kayam qamshi da daddawa da seasoning and spices kisa ruwa kisake dorawa taqarasa dahuwa,wlh daga yau kin dena jiqa ganda tsahon kwana1-2, tasted and trusted.

Yadda ake zobo mai dadi

Abinci
YADDA AKE ZOBO DRINK Abubuwan buqata Sobo/zoboCucumberBawon abarbaDanyar cittaKanumfariFlavorSugarBevi mix cola da Bevi mix mangoKamshi (Wanda ake samu a cikin kayan yaji amma optional ne)Sai barkono kadan (optional) Da farko za a tsince dim dattin da ke cikin zobo sai a zuba a tukunya babba a markada cucumber a wanke bawon abarba dik azuba akai,a zuba barkono kadan da kamshin kayan yaji (optionals ne) a zuba kanumfari da jajjagaggiyar citta akai sai a zuba ruwa a Dora kan wuta ya tafasa sosai a tace a kara ruwa akai a sake tacewa har sai zobon ya salamce sai a ajiye domin ya rage zafi sai a zuba sugar,flavor na ruwa,da kuma Bevi mix (wadanda ba sa so wannan zasu iya Saka iya sugar kawai) sai juya su su hade jikinsu sosai a kara tacewa sai a juye a jug or a kulla a Leda ko a robob...

Yadda ake miyar zogale danye

Abinci
MIYAR ZOGALE AttaruhuTumaturAlbasaMaggiZogale danyeTafarnuwaManjaGyada Step 1Ki wanke kayan miya kiyi grating dinsu dasu tafarnuwa albasa a tare, ki daka gyadarki kar ta daku sosai Step 2Ki soya manja ki zuba kayan miyanki gyada ki qara ruwa dan daidai ki rufe, in ta fara dahuwa kizuba maggi kibarta ta dahu saiki zuba zogalen ki kibarshi ya fara nuna saiki zuba albasa ki barta ta qarasa saiki sauke

Yadda ake shinkafa da miya

Duk Labarai
YADDA AKE SHINKAFA DA MIYA Kayan hadi :- ShinkafaAttaruhuAlbasaKoren tattasaiKwaiPlantainMangyada Yadda ake hadawa :- Dafarko uwargida zaki dora ruwa awuta idanyatafasa saiki zuba shinkafa,idantayi rabin dahuwa,saiki sauke kiwanketa kitace kimayar tukunya kisa ruwa kadan yadda zai turarata,ammafa karyayi yawa don ba ason shinkafar tacabe saiki rage wuta. Saiki dauko attaruhu kiwanke ki jajjaga, saiki albasa itama ayankata yankan tsaye kiwanketa ki barta akwando tasane,sannan ki dauko koren tattasai kiyankashi ki ajje agefe, saiki dauko plantain ki bare kiyankata,saiki koma kan shinkafarki idanta turara saiki sauke kibarta a tukunyar tadan sha isaka kafin ki zuba a plaks,saiki dauko kasko ko tukunya kizuba mai kisoya plantain dinnan ki ajje agefe, sannan ki dauko tukunyar daz...

Yadda ake kunun gyada

Abinci
YADDA AKE YIN KUNUN GYADA Kayan da ake bukata; Farar shinkafa 3 tins Danyar gyada 4 tins Sugar dai-dai misali. Abu na farko da ake bukata uwar gida ta yi, shi ne ta gyara farar shinkafarta danya sai ta wanke ta ta tsane tsaf, Bayan haka,dama kin soya gyadarki sama-sama kin murje bayan km kin bushe sai ki kai a markado miki bayan an markado ki tace. Sai ki zuba tataccen ruwan gyadar a tukunya in ya tafasa, sai ki dakko wanna shinkafar da ki ka wanke kk km tsane sai ki zuba ta a ciki suyi ta dahuwa har sai ta dahu sosai in kina gudun kada ya tsinke zaki iya zuba ruwan lemon tsami kadan. Idan kuma kin ga bai yi miki kauri ba sai ki dan dibi gasarar koko ki dama da ruwan sanyi sai ki zuba ki juya sosai zai yi kauri insha Allah.

Yadda ake miyar dage dage

Abinci
MIYAR DAGE DAGE Tattasai Tumatir Albasa Attaruhu Man gyada Maggi Curry Gishiri Nama Kaza ko naman saniya /rago ko tunkiya Thyme Yadda za'a Hada a farko za ki tafasa namanki da gishiri, albasa, maggi, thyme. Ki wanke kayan miyarki a markada, attaruhun ki sa ka kadan don ya kara dandanon miyar. Bayan kin tafasa naman sai Ki soya shi ki kwashe naman sai ki zuba kayan miyar ki soya ki kwashe naman ne don kar ya nuna sosai. Ki zuba dukkanin ingredient dinki yadda ki ke so, sai ki mayar da soyyayen naman a ciki ki hade da ruwan tafasahen naman ki yanka albasa wadatacce ki zuba, sai ki bar shi ya turara minti uku zuwa biyar. Kamshi zai yi ta tashi sai ki sauke a cikin da farar shinkafa.