Monday, April 20
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Bidiyo:Kalli yanda aka kama wani dan Najeriya da ya hadiyi kwaya zai fita da ita zuwa kasar Faransa

Bidiyo:Kalli yanda aka kama wani dan Najeriya da ya hadiyi kwaya zai fita da ita zuwa kasar Faransa

Duk Labarai
Hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi, NDLEA ta sanar da kama wani mutum da ya hadiyi kwayoyi dan ya kaisu zuwa kasar Faransa. https://twitter.com/SaharaReporters/status/1873335970801819690?t=BRxQgE7O2wZLT5nqVPdEew&s=19 Mutumin an kamashi ne a filin jirgin saman Abuja yayin da yake shirin hawa jirgi zuwa birnin Paris, babban birnin kasar Faransa. Yace an bashi kwayarne ya kaiwa wani inda aka masa alkawarin bashi Euro Dubu 3.
Hotuna: An kama ma’aikaciyar Gidan yari na lalata da me laifi

Hotuna: An kama ma’aikaciyar Gidan yari na lalata da me laifi

Duk Labarai
Hukukomin Gidan yari a kasar Ingila sun kama wata ma'aikaciya da bidiyonta ya bayyana tana lalata da me laifi. Jaridar TheSun ta ruwaito cewa, an kama ma'aikaciyar me shekaru 19 ne bayan da bidiyon lalatar da ta yi da me laifi a gidan yarin ya watsu sosai. An rika aikawa mutanen dake aiki a gida yarin bidiyon dama sauran wanda ke waje har ta kai ga ya kai ga hukumomin gidan yarin. A kasar ta Ingila dai ana yawan samun irin wannan matsala inda mata ma'aikatan gidan yari kan yi lalata da mazan da ake tsare dasu. A baya an kori mata kusan 29 saboda irin wannan halayya.
Gwamnatin tarayya ta kashe Naira Biliyan 1.4 wajan canjawa masu tsatstsauran ra’ayi tunani

Gwamnatin tarayya ta kashe Naira Biliyan 1.4 wajan canjawa masu tsatstsauran ra’ayi tunani

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta sanar da kashe Naira Biliyan 1.4 wajan canjawa masu tsatstsauran ra'ayi irin su B0K0 Hàràm tunani. Hakan ya farune a cikin shekara daya da rabi data gabata inda aka kafa sansanonin canjawa masu tsatstsauran ra'ayi da suka tuba tunani. A ranar May 12, 2022 ne tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sanyawa kudirin dokar kafa cibiyar yaki da ayyukan ta'addanci a Najeriya wanda kuma a karkashinta ne ake kula da tubabbun 'yan Boko Haram din. Gwamnatin tarayya dai ta gina cibiyoyin kula da irin wadannan mutane da suka tuba daga ayyukan ta'addanci.
Ji shirye-shiryen da Su Atiku, Obi, El-Rufai da Kwankwaso suke dan kayar da gwamnatin Tinubu a zaben 2027

Ji shirye-shiryen da Su Atiku, Obi, El-Rufai da Kwankwaso suke dan kayar da gwamnatin Tinubu a zaben 2027

labaran tinubu ayau
Rahotanni sun bayyana cewa, jam'iyyun Hamayya a Najeriya sun samu karfin gwiwar kayar da Gwamnati me ci ta Bola Ahmad Tinubu a zaben 2027 idan Allah ya kaimu. Sun samu wannan kwarin gwiwar ne bayan da suka ga jam'iyyun adawa a kasashen Amurka da Ghana sun yi nasara akan jam'yya me mulki. Rahotanni sun bayyana cewa a ranar 26 ga watan Nuwamba, Atiku Abubakar, da tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, da Peter Obi sun yi tattaunawa inda suka yanke shawarar hada kai dan kafa sabuwar jam'iyya ko kuma shiga wata dan su kayar da Gwamnatin Bola Ahmad Tinubu a zaben shekarar 2027. Hakanan a ranar 30 ga watan Nuwamba ma Atiku da Peter Obi sun sake tattaunawa a Adamawa. Kakakin Atikun, Paul Ibe ya tabbatar da cewa, me gidansa, Atiku Abubakar ya janyo hankalin jam'iyyun hamay...
An baiwa Tinubu Shawarar a tsaurara tsaro a iyakokin Arewa

An baiwa Tinubu Shawarar a tsaurara tsaro a iyakokin Arewa

Duk Labarai
Tsaffi janarorin soji da tsaffin jakadu da masana harkar tsaro sun baiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu shawarar a tsaurara tsaro a iyakokin Arewa dake da iyaka da Jamhuriyar Nijar. Hakan na zuwane yayin da dangantaka ke kara yin tsami tsakanin Najeriya da kasar ta Nijar inda kasar Nijar din ta zargi cewa Kasar Faransa ta baiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu makudan kudade dan a girke sojojin Faransa a iyakokin Najeriya da Nijar. Saidai a martanin me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu, yace babu sojojin Faransa a Najeriya. Ribadu ya kara da cewa kuma Najeriya ba zata canja huldar jakadancin dake tsakaninta da kasar Faransa da Amurka da Rasha ba saboda rashin jituwar dake tsakanin Faransar da Kasar Nijar. Ana ta ci gaba da kai ruwa rana tsakani...

Maganin yawan mantuwa

Magunguna
Yawan mantuwa matsalace da kan saka mutum cikin damuwa musamman a ma'amalarsa da mutane da wajan aiki da sauransu. A wannan rubutu zamu yi bayani game da yawan mantuwa da yanda ake maganinsa. Abubuwan dake kawo yawan mantuwa: Yawan Shekaru: A yayin da tsufa ya fara kama mutum, zai iya yin fama da yawan mantuwa saboda kwakwalwarsa bata aiki kamar lokacin da yake da kuruciya ko sauran karfi a jikinsa. Damuwa: Wanda ke cikin yawan damuwa kan samu matsalar mantuwa musamman idan damuwar ta yi yawa. Rashin Isashshen Bacci: Wanda baya samun bacci ko rashin isashshen bacci kan iya yin fama da matsalar yawan mantuwa. Rashin Cin Abinci me gina Jiki: Rashin cin Abinci me gina jiki na iya taba lafiyar kwakwalwar mutum wanda ke iya kaiwa ga yawan mantuwa. Hakanan yawan shan sikari da...

Maganin yawan fitsari

Magunguna
Yawan fitsari matsala ce dake sa mutum ya rika yin fitsari fiye da kima, idan ya zamana mutum na yin fitsari fiye da sau 8 a rana, za'a iya cewa yana yawan fitsari. Wannan matsala zata iya faruwa ga kowa amma tafi yawa a tsakanin mutanen da suka zarta shekaru 70 a Duniya, da mata masu ciki, ko bayan fara shan wani magani, ko kuma wani me wata cuta ta musamman. Yawan Fitsari na iya zama alamar daukar ciki ga mace, sannan yana iya zama alamar ciwon sugar wanda ake cewa diabetes ko ciwon mafitsara, da sauransu. Masana kiwon lafiya sunce ba matsala bace idan mutum ya tashi da dare yayi fitsari, sun ce idan mutum ya kai shekaru 40 zuwa 50, to zai iya fuskantar tashi cikin dare yayi fitsari sau daya. Idan kuma mutum yana tsamanin shekaru 60 zuwa 70, zai iya rika tashi cikin dare yana yi...