Sunday, July 26
Shadow

Jam’iyyun Adawa nawa jam’iyyar APC dariya saboda rikicin cikin gida daya balle a cikin APC din

Rahotanni sun bayyana cewa, Rikicin cikin gida ya balle a cikin jam’iyyar APC.

Rikicin daya balle shine APC ta aikawa INEC jadawalin sunayen ‘yan takararta wadanda a cikinsu akwai wandanda suka ci zaben fidda Gwani amma aka cire sunayensu aka maye da na wasu da basu ci zaben ba.

Sunayen sanatoci masu ci guda 6 ne wanda basu ci zaben fidda gwani ba daga jihohi 9 ana kutsa sunayensu inda aka cire na wadanda suka ci zaben fidda gwanin.

Hakan ya sabawa dokar INEC wadda tace INEC din ba zata amince da sunan duk wani dan takara wanda bai lashe zaben fidda gwaniba.

Hakan yasa jam’iyyun Adawa suka sako APC gaba suna ta mata dariya. Saidai APC tace su ji da rikice-rikicen dake faruwa a cikin jam’iyyarsu.

Karanta Wannan  Dan jarida ya zargi hukumar Kwastam da taimakawa masu fasa kwaurin shikafa zuwa cikin Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *