Lamari ya kara kazancewa tsakanin Sanata Natasha Akpoti da Godswill Akpabio, Mijinta yace Akpabio abokinsa ne kuma yasan yana neman matarsa
Lamari tsakanin Sanata Godswill Akpabio wanda shine kakakin majalisar dattijai da sanata Natasha Akpoti dake zarginsa da neman yin lalata da ita ya kara kazancewa.
Mijin Natasha, High Chief Emmanuel Uduaghan ya bayyana cewa, yasan da maganar neman matarsa da sanata Godswill Akpabio ke yi.
Yace asalima Sanata Godswill Akpabio abokinsa ne dan haka a matsayinsa na basarake kuma suna da alaka me karfi tsakaninsa da Sanata Godswill Akpabio bai nemeshi da fada ba, ya sameshi suka warware matsalar tsakaninsu inda ya mai alkawarin ya daina neman matarsa.
Saidai, High Chief Emmanuel Uduaghan yace matarsa ta ci gaba da kawo mai korafin cewa, Sanata Godswill Akpabio ya ci gaba da neman yin lalata da ita.
Dan hakane High Chief Emmanuel Uduaghan yake neman cewa a girmama matarsa wajan binci...








